Daga Taskar Crypto

Daga Taskar Crypto Muna kawo labarai, Muna Rubuta Novels lokaci lokaci, sannan muna kowa labarin kasuwanci da dai sauran su.
(1)

23/06/2024

June 23: Yau ce ranar zawarawa ta duniya!

Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ne ta ƙirƙiro wannan rana shekaru 13 da s**a wuce wanda a cewar ta, manufar shi ne tunatar da duniya irin ƙalubalen da zawarawa ke fuskanta.

Taken wannan ranar a yau shi ne “Ƙirƙira da Fasaha Domin Daidaiton Jinsi.”

Tsoffin alƙaluman UN na nuni da cewa akwai kimanin zawarawa miliyan 285 a duniya baki ɗaya. Ko ya alƙaluman suke a Najeriya?

22/06/2024

Kanuri ta Shiga adashe aka bashi Daukan fari.
Da aka zo amsar zubi sai Alanguburo tace ta fita don ita batason Rigima.😅

22/06/2024

Da shigarsa gurin sayar d abinci, sai ya hangi wani baƙin mutum a zaune a can gefe guda, shi kaɗai.

Sai ya fusata y ce, yaushe baƙaƙe s**a samu sake har suke haɗa kafaɗa damu a nan ƙasar France.

Ya ce, ku rabawa duk wanda suke gurin abinci kyauta, ni zan biya amma kar ku bawa wancan baƙin...!!!

Bayan ya biya kuɗi, wannan baƙin mutumin sai ya taso ya ce, na gode Yallaɓai!

Wannan abun sai ya sake ɓata masa rai, ya ce, ku raba musu lemo, ya ɗauki kuɗi ya biya. Baƙin nan ya sake tasowa ya ce, na gode Yallaɓai.

Wannan mutumin ya fusata, ya cewa ɗaya daga cikin ma'aikatan, wannan baƙin me yake yi a nan..!?

Sai ya ce, Yallaɓai wannan ai shi ne mai gurin gaba ɗaya.....!!!!

Idan aka ce ka goge guda biyu har abada wanne da wanne zaka goge cikin abinda aka lissafa a ƙasa?-Whatsapp-Telegram-TikT...
21/06/2024

Idan aka ce ka goge guda biyu har abada wanne da wanne zaka goge cikin abinda aka lissafa a ƙasa?

-Whatsapp
-Telegram
-TikTok
-Facebook
-Instagram
-X (Twitter)

Ni zan goge wa kaina Instagram da TikTok, Idan aka ce kuma na gogewa ɗanbaiwa, zan goge masa Telegram saina bashi zaɓi ya ƙara goge ɗaya. 🤣🏃

Idan aka ce ɗanbaiwa ka gogewa Influencer guda ɗaya ka bashi zaɓi ya ƙara goge ɗaya wanne zaka goge masa?

21/06/2024

Da ɗan majalisar ku na Jaha da Telegram dinka wanne ne yafi ma amfani 😎 nidai gwanda Tapswap da namu yasin 😩

21/06/2024

Tana zaune k**ar yadda ta saba, yazo ya ce, ranki daɗe ga shayin an kawo.

Ta ce: Na gode!

Ya ce: Ranki daɗe wannan shi ne Kofi na uku da na kawo miki amma baki sha ko ɗaya ba!

Ta ce: Saboda bana shan shayi!

Ya ce: Me yasa k**e siya toh?

Ta ce: Menene ruwanka a ciki?

Ya ce: Ina aiki ne a nan wajen, kuma na san ajinmu ɗaya dake a Jami'a. Na san baki taba lura dani ba, amma kullum in ana darasi bani da aiki sai kallonki kuma duk in da kika sanya ƙafarki ina biye dake..!

Ta ce: Duk saboda me kake aikata hakan..!?

Ya ce: Saboda sha'aninki yana bani mamaki......!
Wani lokacin kina dariya ba tare da dalili ba. A wani lokacin kuma sai na ga kin turbune fuska....!

Wannan aikin ina zuwansa ne, kuma ina ƙaunarsa saboda kullum sai kin zo wurin nan, ni kuma ina jin daɗin tozali da ke.

Baki san duk sa'ar da naga wani ko kallon banza ya yi miki a Aji sai mun yi rigima da shi ba...!

Ta ce: Me ka ce....!

Ya ce: Abin da kunnuwanki s**a ji.
Bana samun nutsuwa har sai na kalli fuskarki, sai n biki a baya a baya in kina tafiya. Ki yi haƙuri, Ki yafe mini....!

Ta ce: Akan me ka ke bani haƙuri ne...!?

Ya ce: Saboda ina bin diddiginki ba tare kin sani ba! Kuma kullum da daddare in ki ka zo nan kika zauna sai na koma gefe ina ta kallonki.... Ki yi haƙuri....!

Ta ce: Babu komai maganar ta wuce. Mu dawo kan batun farko da muke tattaunawa...

Ya ce: Ai babu wani batu d muka fara magana akai!

Ta ce: Ba ka tambayi me yasa nake sakawa a kawo mini shayi amma bana sha ba...!?

Ya ce: Ƙwarai da gaske...!

Ta ce: Da gaske bana shan shayi, kaɗai dai in cewa a kawo ne saboda aikinka ne, dole kai zaka kawo, ni kuma ina jin daɗin kallonka... Saboda na ganka kaɗai nake siyan abin da bana buƙata....!

21/06/2024

Bayan ya dawo gida tare da abokinsa.

Matarsa ta hau shi da faɗa tana cewa, ba na gaya maka kar ka sake zuwa gidan nan da baƙi ba in baka sanar da ni ba! Me yasa baka yi mini waya ka tambaye ni zan yi girki ba ko ba zan yi ba?

Kuma dama na gaya maka, yau a gidanmu zan Ci abincin rana amma saboda taurin Kai shi ne kazo da abokinka, toh na ga abin da zaku Ci.

Kaima ban dafa maka abincin ba b***e har wani Ƙato ya Ci. Ni yanzu Ƙanwata nake jira ta gama shiryawa, zamu tafi gidanmu, sauri muke.

Bawan Allah! Ya Sallami abokinsa. Shi kuma ya dawo gida.

Matarsa ta ce, wana kinibibin ne ya sa ka gayyato mini abokinka cikin gidan nan?

Ya ce, ki yi haƙuri, kullum in muka haɗu sai ya ce, gaskiya na yi dacen mata mai tarbiya.

Sai ya ce, yana so ya auri wannan Ƙanwar ta ki, shi ne na kawo shi don ya ga samfurin tarbiyyar gidan ku a aikace....!!!

20/06/2024

Shugaban Kamfanin da yake aiki ya kirawo shi, ya ce, " Haƙiƙa muna jin daɗin aiki da kai sosai, ban san yadda zamu iya tafiyar da kamfanin ba in babu kai, amma dole mu gwada ko zamu iya, don haka daga sati mai zuwa zamu fara gwada aiki babu kai...!!!

20/06/2024

Larabawa, ɗayansu ya kasance baya sayar d Dokin da matarsa take hawa....... in kuwa Dokin ba shi da lafiya yanka shi yake yi don kar wani ya siya ya hau, saboda tsananin kishin matarsa.

Mamakin wanda zai bawa wani Namiji wanki da kuma gugar kayan matarsa....

Me yasa ba zaka yi mata wankin da gugar d kanka ba..?

Baka kishin wani ya taba kayan da matarka take sanyawa a jikinta...!?

Ko kuma kishi ya mutu a zuciyar maza ne.....!

19/06/2024

Masoyan $Blum suyi "Like" su huce!

Masoyan $TapSwaps suyi comment!
😃😄😃

19/06/2024

Dui wanda baya jin Turanci yak**ata yai marmaza ya je a fassara masa wannan rubutun (rubutu ne dayak**ata a rubuta shi da ruwan Zinari da alƙalamin Azurfa).

THE S*X YOU MUST NOT HAVE.

1. Never agree to have s*x with your boss. If the harassment becomes too much, resign and trust God for a better job.

2. If God put people under your care to mentor or Pastor, it is better you die than to have s*x with them. Never take advantage of God's people no matter what.

3. Don't have s*x with a married woman. If you are getting too much attached via chatting, official or academic rapport, break up the closeness or whatever name you have for it.

4. Never have s*x with your lecturers. S*x for grades or marks is for nonentity. You are not. Never must you be.

5. If you are a marketer, never agree to sleep with a prospective client just to meet your official target. Never!

6. Don't have s*x with your in-laws. If he or she stays with you and you are finding it difficult to resist the pull, let him or her leave. I mean latest tomorrow.

7. Don't have s*x with your neighbour or colleague. A neighbour is a neighbour. A colleague is a colleague. Don't get your life more complicated.

8. Don't have s*x with your platonic friend. If the relationship is no longer platonic, break up the thing.

9. I believe God created s*x to be between male and female. Stay away from having s*x with your same gender. God is against homos*xuality and so should you.

10. Don't have s*x with your sibling or relatives. In**st is vile.

11. Don't have s*x with your girlfriend. Don't have s*x with your boyfriend. God did not create s*x for love relationships. He created it for MARRIAGE.
S*x is for procreation
The only s*x you should have is with your Legally married partner

Copy
🙏👏

HALACCIN MU'AMALA DA BITCOIN A MUSULUNCE BISA FAHIMTAR MASHAHURAN MALAMAI (1)Tarihin kudi ya faro ne kafin zuwan musulun...
19/06/2024

HALACCIN MU'AMALA DA BITCOIN A MUSULUNCE BISA FAHIMTAR MASHAHURAN MALAMAI (1)

Tarihin kudi ya faro ne kafin zuwan musulunci (akwai musulunci tun farkon samuwar duniya; ina nufin lokacin jahiliyya). Daulolin Rumawa da Byzantium (turkiyya a yanzu) na amfani da kudade na karfe da aka samar daga zinari "gold", azurfa "silver" da kuma sinadarin kwafa "copper coinage". Ire-iren wadannan kudade su ne su ka yawaita a lokutan jahiliyya. A tsawon shekaru arba'in na kalifanci da kuma shekaru talatin din farko na daular Banu Ummayad "ummayad period", wadannan kudade na karafa su ne dai su ka ci gaba da wanzuwa ana amfani da su. Har zuwa shekarun Hijra na 70s (CE 690s) ne inda musulmai s**a fara samar da na su kudaden na karafa.

Kudade na da aiyuka guda uku sa ya wajaba su cika:

1. Hanyar musaya "medium of exchange"
2. Ma'aunin kimar hajojin da mu ke saye "unit of account"
3. Haja mai kima "store of value"

A gurguje za mu bayanin abin da ke sa kudi su zama kudi, da kuma yadda aka rika samar da hanyoyin mu'amala da kudi din, daga wannan marhala zuwa wata.

1. Barter

Tun farkon lokaci, mutane na amfani da tsarin ban-gishiri-na-baka-manda "barter system". Mutane na cinikayya da musayar hajoji domin wadansu hajojin. Wannan tsari ya haifar samuwar cikas da tangarda sosai saboda tsari ne da babu inganci ta musamman ta fuskar gwaji da kimanta kaya.

2. Commodity Money System

A tsarin Barter, ya faye faruwa cewa mutane ba za su iya cimma matsaya ba ta fuskar yadda aka auna da kimanta hajojin su, a wasu lokutan kuma ba su bukatar irin hajojin da abokin musaya zai ba da. Domin warware irin wannan matsala, sai aka samar da tsarin commodity money system.

A irin wannan salo, mutane na mu'amala da wasu hajoji zababbu wadanda mutane su ka faye bukatuwa gare su kuma ake iya samun su cikin sauki. Suna amfani da ire-iren wadannan hajoji a matsayin hanyar biyan kudi. A lokuta daban-daban, a kuma garuruwa daban-daban, mutane sun yi amfani da hajoji nau'uka daban-daban, alk**a, gishiri, ganyen taba, iri na shuka da sauran su. Duk da haka, wannan tsari na da nashi tawaya shima saboda ba za ka iya daukar buhun gishiri da na alk**a ba a kusan koda yaushe.

3. Metallic Money System

Domin warware matsalolin da tsarin Commodity Money System ke dauke da shi, mutane sun koma amfani da kudade na karafa inda s**a rika amfani da wasu karafa na musamman k**ar zinari da azurfa a matsayin kudi. Wannan tsari ya dauki lokaci mai tsawo mutane na mu'amala da shi, amma ya samu sauye-sauye ta hanyoyi k**ar haka:

(1) An yi amfani da zinari da azurfa a matsayin kudi yayin da aka rika auna kimar su ta hanyar nauyin su.

(2) An samar da sulallan kudade na karafa daga zinari da azurfa. Kimar wadannan kudade na daidai da kimar da zinari da azurfa ke da ita. Wannan shine abin da ake kira Gold Specie Standard

(3) Wasu sarakunan a zamunnan baya sun yi amfani da tsarin kimanta kudi bisa hadakar darajar zinari da azurfa "bimetallic system". A lokaci guda an rika anfani da zinari da azurfa duka a matsayin kudi. Kimar su kuma ana auna ta ne ta hanyar auna tsakanin su.

(4) A wancan lokaci, yana da masifar wahala ka iya adana zinari ko azurfa ba tare da an sace su ba. Wannan ya sa mutane sun rika ba da ajiyar su ga manyan diloli da ke cinikayyar su "jewelry dealers" domin kaucewa ta'adar barayi. Wadannan masu ajiya na ba mutane rasidi "receipt", yayin da mutanen ke iya samun isa ga zinari ko azurfa ta hanyar wadannan takardun rasidi. Yayin da wannan tsari ya shahara, mutane sun rika amfani da takardun rasidan kadai a saye da sayarwa da su ke yi ta yau da kullum, a madadin yin amfani da zinari ko azurfa wadanda wadannan takardu ke wakilta.

(5) Karbar takardun rasidi a kasuwanni shine abin da ya samar da tsarin (commodity backed money) wato, kudin da su ka samu goyon-baya daga wasu hajoji masu kima. Bankuna sun cigaba da samar da takardun kudade wadanda ke samun goyon-baya na zinari dari bisa dari. Wannan na nufin kana iya musayar wadannan takardu a ba ka zinari. Wannan shine abin da ake kira Gold Bullion Standard.

4. Fiat Money

A shekara ta 1971, shugaban amurka na wancan lokaci, Nixon, ya fitar da wasu matakai na wucin-gadi da su ka shafi tattalin arziki "temporary economic measures" inda ya soke tsarin canza dalar amurka kai-tsaye zuwa zinari "US dollar-gold convertibility".

Daga bisani, manyan bankuna su ka fara samar da takardun kudade. Babban banki ya tursasa amfani da su a matsayin kudaden da doka ta halatta. Wanda ya wajabtawa dukkanin al'umma su karbe su a matsayin kudi domin cinikayya da kuma sauke nauyi na bashi ga wadanda ake bi.

Shamsudin Yashe ✍
Insha Allahu, zan ci gaba.

19/06/2024

Jama'a dole muyi Mozo...

Abinda na fahimta, Avive suna son gyara kuskuren da s**ayi na ɓatawa mutane rai a Avive, shine s**a sake samar da Mozo.

A halin yanzu sun dawo da Mining ɗin su na Avive, amma dole sai kayi register fa Mozo kafin mining ɗinka ya dawo normal. Babu laifi mu fara muga tsarin nasu ya zai kasance:

https://t.me/MozoAI_bot?start=c5L0mSwi

19/06/2024

🔥🔥ATH price 🔥🔥
₦100
WhatsApp
09085121984

19/06/2024

Dattijo: Ka je ka nemo mana abin da zamu Ci ɗana.

Ɗan ya amsa, ya k**a hanya. Jim kaɗan ya dawo gida....

Dattijo: Me yasa ka dawo da wuri haka....!?

Yaro: Na fita gefen gari, sai na zauna kusa da wata Bishiya, sai ga wani Jemage nan yazo a wahale, a gajiye, kuma a yunwace ya hau kan bishiyar.....

Sai na ce, a raina ta ya ya wannan Jemagen zai iya rayuwa...!? Kafin na gama bawa kaina amsa sai ga Zaki da ƴaƴansa sun dawo daga farauta........ S**a baje abinci s**a Ci s**a ƙoshi, s**a bar sauran a wurin.... Bayan tafiyarsu Jemagen ya sakko shima ya Ci ya ƙoshi......

Anan na tabbatar arzikin bawa a hannu Allah yake, kuma duk in da bawa yake sai ya samu arzikinsa, hakan ya sanya na yi dawowata gida...

Dattijo: Kaiconka! Me yasa baka zama k**ar Zaki ba mutane su rinƙa Ci daga ragowarka ba........ maimakon ka zama Jemage wanda yake Ci daga ragowar mutane ba.....

Akwai abinda na manta a Post ɗin ɗazu...Matsalar scalability na Ethereum ya sanya Binance s**a yi faka-faka s**a samarda...
18/06/2024

Akwai abinda na manta a Post ɗin ɗazu...

Matsalar scalability na Ethereum ya sanya Binance s**a yi faka-faka s**a samarda BEP 2.0 a shekarun baya, daga baya s**a yi upgrading zuwa Bep20 wanda muka sani da BSC a yau.

Ga waɗanda s**a san Bep 2.0 a shekarun baya na Binance kafin upgrade mutane sun sha fama da matsalar Memo/Tag. Wanda tana daga cikin irin matsalar da mutane suke fama da ita a TON Blockchain, mun tattauna da ma'aikacin su kan wannan matsalar yake ce mini suna aiki akan upgrade k**ar yadda Binance s**ayi daga Bep2 zuwa Bep20.

Duk ranar daya tabbata TON sunyi wannan upgrade ɗin, a sannan za'a fara ɗaura abubuwa ssoai akan Blockchain ɗin, k**ar yadda ya faru da BSC a shekarar 2020/2021

Ga misalin Wallet address na Bep 2.0 ɗin Binance
bnb16xkwj5fqhf5cw5hjdpcfpy62fyyxl7s9ljydys

Ga misalin Bep 20 wanda mukafi sani da BSC
0xCF7F1a247AD2F5b4ed01c4f300D9feB18F998598

A yanzu haka; Telegram yana da mutane da yawan su ya kai 1.56 Billion da suke amfani da Telegram, wannan shine zaiyi dai...
18/06/2024

A yanzu haka; Telegram yana da mutane da yawan su ya kai 1.56 Billion da suke amfani da Telegram, wannan shine zaiyi daidai da kaso ɗaya cikin biyar na mutanen duniya. Suna da active mutane da yawan su ya kai 800M a kowani wata.

Daga cikin dalilan samar da TON Blockchain shine waɗannan mutanen a juyar dasu daga tsarin da muka sani na gargajiyar web2.0 zuwa web3.0. Duka adadin mutanen duniya da suke Crypto ayanzu an ƙiyasta basu fi 300M ba, idan Telegram yayi nasarar zuwa ko da 1B s**a shigo duniyar Blockchain yaya kake ganin Blockchain ɗinsu zaiyi nisa?

TON ba sunzo bane suyi gasa da sauran Blockchains, sunzone su gina wata sabuwar duniya da zata rinjayi duniyar Blockchain baki ɗaya. Misali idan ka ɗauki Ethereum Blockchain, kusan duk masu amfani dashi akai-akai masana Crypto ne sosai, haka zalika dukkan layer 2s da muke dasu. Masana Crypto a yanzu sune s**afi ƙaranci a sabgar.

Jiga-jigan TON Blockchain a karan kansu sun san ba abu ne mai sauki ba su iya jawo masoya Ethereum da Masoya Solana ba zuwa TON cikin sauki, saboda galibin su masu kuɗi ne, kuma daga cikin hanyoyin da ake iya jawo mutane zuwa kan Blockchain akwai yawan bayar da Airdrop ga community ɗinka.

Masoya Ethereum da irin su Solana da yawan su sun raina Airdrop ɗin $500 zuwa $1000. Zasu amshe, sannan kuma in ba sa'a ba su raina, suyi gaba su bar maka Blockchain ɗinka, wannan ya saka TON Blockchain ya mayar da hankali wajen samar da Telegram-Mini-Apps wanda ake ta onboarding ɗin ƴanbaiwa zusa kai, ƴanbaiwa idan ka basu Airdrop na $100 ma they'll appreciate it kuma suji sunfi son Blockchain dinka akan kowanne.

Kuɗin da Notcoin kaɗai ya bayar ya saka mu da yawa muna son TON Blockchain yanzu, wannan dalilin ya saka da WCoin s**ayi zaɓen wani Blockchain muke so a ɗaura shi a yau TON ya samu 82% na ƙuri'a, Solana 12%, Ethereum kuma 6%. Duka wannan soyayyar ta samu ne saboda kuɗin da Average ƴan baiwa s**a samu na $200 daga Airdrop akan TON.

Idan TON suna so aci gaba da damawa dasu, kuma burin su na maida mutanen da suke amfani da Telegram mutun 1.6B zuwa duniyar Web3.0 ya cika, k**ar ya zamar musu wajibine suci gaba da taimakon Telegram-Mini-Apps (Minings/Farming) da suke Telegram har su kai ga nasara.

Fundamentally idan wannan burin nasu ya cika, mafi ƙaranci TON zai kamo Solana Blockchain ta fuskar Market Cap koma ya wuce ta, TON mafi ƙaranci zaiyi 4X daga inda yake yanzu kafin ya kai Market Cap ɗin Solana. NFA

18/06/2024

🔥🔥ATH price 🔥🔥
₦80
WhatsApp
09085121984

18/06/2024

Dattijuwa tana hira tare da mijinta, sai ta ce, da zan ga Fir'auna da na tambaye shi abin da ya ruɗe shi har ya shimfiɗa mulkin zalinci....!!

Miji ya ce: Oh! Ke kina Aljanna shi yana cikin wutar Jahannama, ina za ki gan shi b***e ki tambaye shi!?

Ta ce, haka ne! Amma na tabbata kai kam zaku haɗu, don haka sai ka tambayar mini shi...!!

18/06/2024

RIKICIN MASARAUTA
Jihar Kano ta gamu da jarraba wacce ke bukatar hadin kan masu hankalin cikin mu domin tunkarar wannan jarraba.Tun muna ganin wannan rikici k**ar wani Abu me sauki da zai iya wucewa cikin kankanin lokaci amma Sannu Sannu abin ya zama k**ar cin kwan makauniya.Lokaci yayi da ya k**ata ace Al’ummar jihar Kano sun ajiye bambamcin siyasa da akida dan tunkarar wannan babbar masifa da ta tunkaro mu.
Mu sani cewar bamu da in da yafi Kano Idan muka Kau da idon mu daga barin gaskiya karshe mu ne za mu zo mu afka cikin kogin nadama. Mu ajiye son zuciya muyi hakuri mu guji duk abin da zai jefa Garin mu cikin garari.
Mu kaucewa jefa Kano cikin kirkirarren rikici wanda wasu ke Neman gwara kan mu,mu Nemi gaskiya mu bita ko da kuwa daga gun wa ta fito.
Idan mun yi haka sai Allah ya taimake mu.
Allah ya yayi mana maganin duk wani Abu da ya fi karfin mu.

HAMSTER KOMBAT SUN ƘARA NANATAWA CEWA: PPH SHI YAFI AMFANI AKAN COIN BALANCE, ME YAKAMATA MUYI..?1. Tambayata wa Hamster...
18/06/2024

HAMSTER KOMBAT SUN ƘARA NANATAWA CEWA: PPH SHI YAFI AMFANI AKAN COIN BALANCE, ME YAKAMATA MUYI..?

1. Tambayata wa Hamster Shine: Idan har PPH yafi Coin Balance amfani, toh ya maganar Level kuwa? Shin yanzu ba ruwan mu da balance, kawai muyita tara PPH kome?

2. Idan kuma Level na da amfani, kenan Coin Balance yana da amfani. Tunda PPH baya saka Level naka ya ƙaru Coin Balance ne ke sawa. Dole kana buƙatar tara Coins.

3. Sannan har yanzu tambayata bata samu gamsasshen amsa ba: Tambayata itace, idan da PPH za'a yi amfani gurin Airdrop menene Amfanin Level kenan bashi da amfani ko yaya?

4. Shi kansa PPH ɗin da akace za'a yi amfani dashi gurin Airdrop, wane mechanism za'a bi gurin Airdrop din. Za'a na bayar dashi ne based on yawan PPH naka ko yaya abin yake.

5. Banda haka Hamster naji sunce PPH yafi Coin Balance amfani, amma banji sunce Coin Balance bashi da amfani ba. Kenan hakan na nufin idan an tashi Airdrop za'a dubi gabaki daya ne tun daga Coin Balance, PPH, Cards, Level ko yaya?

"Duk Wannan Tambayar Hamster Sun Gama Amsata Da S**a Ce Play Wisely, Hamster Game Ne A Game Kuma Ba Komai Ake Faɗa maka Ba"😁😁😁

18/06/2024

Dukkan minings ɗin da mukeyi da Telegram sun rabu kashi-kashi, kaɗan daga wanda nayi nazari:

1. Akwai waɗanda dama suna da Fundamentals ɗinsu da kudin su a hannu, community s**a rasa, sai s**a shigo ta wannan sigar, sune irin su CEXP, Timefarm, CEDEX.

Misali kunga CEX .IO tun shekarar 2013 take, amma a Play.store duka 1 million download take dashi, sai gashi yanzu sun samu hanyar da zasu iya ƙarawa kansu 5Million users.

Kamar haka Timefarm tun shekarar 2016 kamfanin yake, suna da utility da komai, kawai users suma suke nema.

***** Irin waɗannan galibin su zasuyi nasara, saboda dama suna da dalilin tara community ɗin, ya k**ata su faranta musu. Shiyasa bazaka ji suna shiga jikin su TON Foundation ba, ko Ton Blockchain ba don suyi magana kansu.

2. Akwai waɗanda basu da wani Fundamental, kawai sun fara ne, sai kuma s**a samu community daga baya s**a fara nemarwa kansu utility sannan suke neman a ɗauki nauyin su, sune irin su Hamster, Tapswap, WCoin, Yescoin**, Dotcoin, Firecoin da mak**antan su.

Waɗansu daga cikin su zasuyi nasara, wasu kuma zasuyi ta raina mana wayo har su mutu, su irin waɗannan dama zallar samun kuɗi ne a gaban su k**ar yadda muma son kuɗi ya kawo mu.

3. Akwai waɗanda suna da Fundamental ɗinsu daidai gwargwado, sannan kuma suna da kuɗi a hannun su daidai yadda zasu iya ɗaukar nauyin Project ɗinsu, waɗannan yiwuwar zasuyi nasara tana da ƙarfi In shaa Allahu, saboda ƙarfin da suke dashi zai ya ƙara ƙarfi da samun support daga TON. Sune irin su Blum, Catizen, da kuma Pixelverse.

Akwai wasu ma da yawa, shiyasa mu duka munayi!!! Add yours!!!

Ku duba Comment Section👇👇

18/06/2024

ME KUKE GANIN ZANYI????

Zaune nake cikin daki ni kadae ina naxari game da rayuwa, aljihuna babu komae face N400. Kwatsam naji karar waya a gefena, in duba sae naga budurwatace. Amsawata keda wuya: - Hello Honey, kaxo ka sameni a "U & Me Restaurant" yanxunnan pls.

Take na hau aca6a ina tafe ina xulumi har daga karshe dae na yanke shawarar siya mana kwalba 2 na maltina idan na isa wnda bae wuce N200 ba. Bayan mintoti kadan, sae gamu mun iso. Na cire N100 na mikawa dan acaba.

Budurwata kuwa tana ganina tasa ayi mata odar 5Alive guda 2 =N700, sannan ta kara da cewa: a kuma kawo mata full plate na papper soup =N400. Ganin haka yasa hankalina ya tashi kwarae da gaske, gashi N300ne kacal ya rage a aljihuna.

Na xauna a gefe ina tunanin yanda xanyi in kaucewa irin wannan abin kunyar, can sae naji tana cewa a kawo mata plate na abinci da xtra meat =N500. Ta juyo gareni: Honey wlh sha'awar nake yi, pls kaje ka sayo min koh na N500 ne.

Nayi farin ciki da samun wannan dama, na mike tsaye na gangara xuwa bakin t**i. Me kuke ganin xanyi?

17/06/2024

Kullum abunda yasa muke cewa mutane su dage su Nemi ilimin crypto currency da blockchain technology, Bai k**ata ka saka kudinka a abunda Baka da Sani akansa ba. Ba crypto ba, kowacce sana'a Yana da kyau kafin Saka ka kudinka ka Fara neman Ilimi akanta. kwanaki naji Anyi Wani program a DCL HAUSA akan crypto currency da mining, Wanda aka gayyachi Rabiu Biyora da Bello Kano.

Akwai Wanda naji Daga cikin masu saurare da aka bashi Dama, yace yayi asarar kusan Naira miliyan biyu a crypto currency, Ina jira naji ta yadda yayi gagurumar wannan asara, ko Yana cikin wadanda s**ayi asara a Luna ko Kuma FTX. Sai naji yace Wai a MTFE yayi wannan asarar, sai abun ya bani mamaki ta yadda Mutumin Da Bai iya banbanche crypto currency da ponze scheme ba, Amma Sabida tsabar San yin kudin dare Daya, ya iya dibar har 2 million ya zuba. Kuma yanzu yazo Yana kallon crypto currency a matsayin danfara bayan shine ya damfari Kansa.

Indai har kaiwa crypto currency hawan Qawara tofa ita zatayi maka irin Shigar da kayi Mata. Mafita shine a Fara neman Ilimi kafin ayi investing a ciki, wannan shine babbar ka'ida har cikin kasuwar mu ta jari Bola.

Allah yasa mu dace Ameen

17/06/2024

Kifi na ganinka mai jar koma...!!!

Suna zaune da matarsa sai ya ce, idan wani ya yi niyyar haifar mana da rigima sai ya ce miki fa ina neman aure..!!

Ta ce, menene matsalar, Allah ne ya halatta ma ka auri har mata huɗu in kana so.

Mijin ya yi murna sosai ya ce, ai dama na san ki da kaifin hankali...!

Ta ce, ka tuna lokacin da kake yawan waya tare da abokinka TALLE da daddare da kuma rana!

Ya ce, ƙwarai ma kuwa, akwai matsala ne...!!??

Ta ce, ka tuna sanda na k**a ka kana waya da shi a uwar ɗaki, kana ganina idanuwanka s**a cicciko, wayar ta faɗi daga hannunka, jikinka na karkarwa... A lokacin na baka takarda ka saka hannu, kuma ka karɓa ba tare d ka duba mai ta ƙunsa ba ka rantaɓa

Ya ce, sai aka yi ya ya....?

Sai ta ce, takarda ce da lauyanka ya rubuta mini wacce take tabbatar da cewa ka bani wannan gidan kyauta. Kuma ta tabbatar da cewa ina bin ka bashin naira miliyan biyar wacce zaka biya a ƙarshen wannan watan...!

Ta ce, yanzu zamu gani in abokin naka TALLE zai cigaba da mu'amala da kai bayan ka tsiyace ka kuma talauce...!

Ashawarce kada kacika maida hankali akan mining gaba daya kabari wasu abubuwa masu mahimmanci a harkan blockchain k**ar ...
17/06/2024

Ashawarce kada kacika maida hankali akan mining gaba daya kabari wasu abubuwa masu mahimmanci a harkan blockchain k**ar investing akan projects masu kyau da trading, wasu dalilan da yasa nace haka akwai lokutan da za'a zo agaji da dayawa daga cikin mining din saboda bawai duka bane legit,ko da kuwa akwai legits dayawa ba lalle bane ace duka zasu bada irin kudaden da muke tunani ba saboda wasu zaka iya bata dogon lokaci ga kuma data ba tare da kacimma abubuwan da kakeso kacimma ba.

Yana da kyau ko baka iya DEX ba katsaya ka fahimci CEX sosai saboda volume na trade Yana ta dawo CEX kayi kokari ka fahimci candlestick psychology, indicators, market trends da sauransu kafin lokacin bukatar hakan yataso ka iyaiya kayi nisa.

A iya sanina wan nan mining din da muke yi ba skills bane acikin abubuwa masu mahimmanci da yak**ata atsaya atattara hankali gaba daya akai ba saboda ko Wanda bai shiga aji bazai iya,wasu kadan daga cikin matsalolin mining din nan shine dayawa masu kawowa kullum zakaji ance Wanda aka kawo yau yafi najiya kyau kaga kuwa ana samun rarrabuwar hankali Kuma uwa uba idan Allah yasa baka da community da zasu iya hadama refferal ba kanaji kana gani bakaramin dagewa kake zakayi har kasamu wani abin kirki akai ba.

Sau tari wasu mining din da'ake kawowa idan kaga ba'a cika damuwa dakawo update akai ba su kansu masu kawowar bayi suke ba Sai dai a dogara da refferal din dazaka hada ayi hakuri a dinga tantancewa a kuma hada da Neman illmi

Address

Kano

Telephone

+2349085121984

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daga Taskar Crypto posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Digital creator in Kano

Show All

You may also like