30/09/2024
Ana yin aure ne da nufin samun nutsuwa, kwanciyar hankali, soyaiya da tausayin juna, sannan kuma da burin zaman mutu-ka-raba, duk auren da ya rasa wadansu daga cikin wadannan manufofi, ba za a ji dadinsa yadda ya dace ba.
Hanyar tabbatar da wadannan manufofin ita ce; yin bincike kafin a yi auren, yin istikhara da yawaita addu`ar neman kyautatar rayuwa, sai kuma kauce wa auren gaggawa.
Maimakon kullum a rinka neman wanda za a yi auren da shi da wuri, gara dai a rinka rokon Allah zabin mafi alkhairi, maimakon a je, kwanaki kadan a fito, gara dai a yi auren da idan an yi shi, babu jeka ka dawo.
Kafin ku amince da mutum a matsayin abokin zama, ku rinka tsananta bincike kafin aure, domin duk wata damarku, kafin a daura auren ne, da zarar an riga an daura, kin zamo rakumi da akala, domin mace ba ta da ikon sakin kanta, namiji ne me wannan damar, shi idan bai gamsu ba, zai iya tsinke igiyar auren naku, ke kuwa fa, damarki ba ta shige ta ki yi yaji ba, shi kuma idan zamanki ya yi tsayi a gidanku, watakila kosawa tabiyo baya.
Hattara dai zawarawa da `yanmata, a daina gaggawar amincewa da wanda ya zo, ba tare da an yi kwakkwaran bincike ba.