05/06/2024
Ga fassarar sabon TAKEN Najeriya a Harshen Hausa
Nigeria we hail thee
Najeriya muna jinjina maki
Our own dear native land
Kasarmu ta gado abin alfaharinmu
Though tribes and tongue may differ
Duk da cewa kabilunmu da yarurrukanmu sun bambanta
In brotherhood we stand
Zamu ci gaba da zama yan uwan juna
Nigerians all, are proud to serve
Duk yan Najeriya suna alfaharin bayar da gudunmawarsu
Our sovereign Motherland.
Ga wannan kasar tamu ta gado mai cikakken yanci
Our flag shall be a symbol
Tutarmu zata zama wata alama
That truth and justice reign
Ta cewa gaskiya da adalci zasu wanzu
In peace or battle honour'd,
Ko a yaki ko a zaman lafiya muna alfahari
And this we count as gain,
Kuma wannan abu ne da zamu dauke shi a matsayin riba
To hand on to our children
Zamu mikawa yayanmu
A banner without stain.
Tuta wacce bata da tabo
O God of all creation
Ya Allah Sarkin kowa da komai
Grant this our one request.
Ka amsa mana wannan addu'a tamu daya tilo
Help us to build a nation
Ka taimake mu mu gina kasa
Where no man is oppressed
Wacce a cikinta babu wani dan Adam da zaa zalunta
And so with peace and plenty
Sannan idanmuka samu zaman lafiya da wadata
Nigeria shall be blessed.
Albarka zata ci gaba da rubanya a Najeriya.
IBRAHIM Alihsan 21radio