21/12/2024
Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta saki tsohon gwamnan jihar Kogi, Yayaya Bello daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, bayan cika sharuɗan beli da babbar kotun Abuja ta gindaya masa a makon da ya gabata.
Sanarwar sakin tsohon gwamnan na ƙunshe cikin wata sanarwar da kakakin hukumar kula da gidajen yarin ƙasar reshen Abuja, Adamu Duzu ya fitar ranar Juma'a, kamar yadda jaridun ƙasar s**a ambato.
“An saki Yahaya Bello, bayan cika sharudan beli, kuma babban koturolan gidajen yari mai lura da Abuja, Ajibogun Olatubosun, ya je gidan yarin domin tabbatar an bi duka sharudan da s**a dace wajen sakin tsohon gwamnan,'' in ji sanarwar.
A makon da ya gabata ne mai shari'a MaryAnne Anenih ta babbar kotun Abuja ta bayar da belin Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.
Sannan cikin sharuɗan har da gabatar da mutum uku da za su tsaya masa, waɗanda s**a mallaki kadarori a manyan unguwann masu daraja a Abuja, kamar Maitama ko Asokoro da Guzape.
Haka kuma kotun ta buƙa tsohon gwamnan ya miƙa mata takardun tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen waje.
Hukumar EFCC mai yaƙin da cin hanci da rashawa ce dai ta gurfanar da Yahaya Bello tare da wasu mutum biyu, kan kan laifuka 16 ciki har da zargin karkatar da kuɗi naira biliyan 110 daga asusun gwamnatin jihar Kogi in da yake gwamnan jihar.
To sai dai tsohon gwamnan ya musanta duka zarge-zargen da EFCCn ke yi masa a gaban kotun.