Arewa Media

Arewa Media Arewa Media is a credible online news medium that focuses mainly on truthful, objective, fair and balance journalism.

We are always committed to bringing reliable information to our large and diverse subscribers from all parts of Nigeria and even beyond.

YANZU-YANZU: Ƴań Bìñďîîģà Sun Sace Mąhaifiýar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara A Gârin Kahutu Dáke Ƙaramar Hukumar Dánja, Jiha...
28/06/2024

YANZU-YANZU: Ƴań Bìñďîîģà Sun Sace Mąhaifiýar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara A Gârin Kahutu Dáke Ƙaramar Hukumar Dánja, Jihar Kátsina A Darén Jiya Al-hamis

Shaidu a ƙauyen sun ce da misalin ƙarfe ɗaya na dare ne dandazon ’yan bindiga s**a kutsa gidan dattijuwar s**a yi awon gaba da ita.

“A kafa s**a zo, ba su yi harbi ba a lokacin da s**a kai harin s**a yi garkuwa da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba a lokacin da s**a memi ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kadai s**a dauka.

“Babu wani yunkuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke dauke da su,” in ji wani mazaunin kauyen na Kahutu.

Ya ce, “Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa s**a tako zuwa cikin kauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kubutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan kauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan cigaba sosai a garinmu,” in ji shi.

Kokarin wakilinmu na ji daga Rarara bai yi nasara ba domin bai amsa kiran wayar ba, har zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.

Allah Ya Bayyana Ta Cikin Aminci.

28/06/2024

Shin kuna goyon bayan a bawa Sheikh Ibrahim Zakzaky riƙon ƙasar nan kamar yadda wannan budurwar ta buƙata?

Muhimman abubuwan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da su bayan ganawarsa da gwamnoni a yau AlhamisBawa iyalai 100,...
27/06/2024

Muhimman abubuwan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da su bayan ganawarsa da gwamnoni a yau Alhamis

Bawa iyalai 100,000 a kowace jiha tallafin N50,000 na tsahon wata uku.

Ware Naira biliyan 155 domin siyen kayan abinci da za a tallafawa masu ƙaramin ƙarfi kan farashi mai rahusa.

Baiwa kowace jiha Naira biliyan 10 domin sayen motocin sufuri masu aiki da iska gas domin sauko da farashin kuɗin zirga-zirga.

Gaggauta fara aikin hanyar da ta tashi daga Sakkwato zuwa Badagary a Lagos. Hanyar zata ratsa ƙauyuka kimanin 216, madatsun ruwa (dams) guda 58, ƙananan hukumomi 156 da manyan garuruwa 39 da kuma gonaki da s**a kai kimanin hectare miliyan ɗaya. Titin zai ratsa jihohin Sokoto da Kebbi da Niger da Kwara da Oyo da Ogun da kuma Lagos.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da biyan kuɗin aikin hanyar jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri wadda za ta ratsa jihohin Rivers da Abia da Enugu da Benue da Nasarawa da Plateau da Bauchi da Gombe da Yobe da kuma Borno.

Haka nan an amince da biyan kuɗin da ake buƙatar domin yin aikin hanyar jirgin ƙasa da ta taso daga Ibadan zuwa Abuja a wani ɓangare na aikin dogo da ya tashi daga Lagos zuwa Kano. Aikin zai haɗa jihohin Lagos da Ogun da Oyo da Osun da Kwara da Niger da Abuja da Kaduna da kuma Kano.

Shugaban ƙasa ya kuma bada umarnin cigaba da aikin hanyar Lagos zuwa Calabar wadda kuma zata yi rassa a jihohin Benue da Kogi da Abuja da Nasarawa da Enugu da Ebonyi.

MUHAWARA: Cikin Waɗannan Malamań Wáne Malami Ne Salòn Karatun Sa Yafi Burgeka?
27/06/2024

MUHAWARA: Cikin Waɗannan Malamań Wáne Malami Ne Salòn Karatun Sa Yafi Burgeka?

Ƴar Asalin Jihar Katsina Farfesar Shari'a Ta Zama Shugabar Jami'ar Abuja Ta Riƙo Hukumar Gudanarwar Jami'ar Abuja Ta Ami...
27/06/2024

Ƴar Asalin Jihar Katsina Farfesar Shari'a Ta Zama Shugabar Jami'ar Abuja Ta Riƙo

Hukumar Gudanarwar Jami'ar Abuja Ta Amince Da Naɗa Barista Aisha Maikuɗi, Yar Asalin Jihar Katsina, Wadda Ita Ce Farfesa Mafi Ƙarancin Shekaru A Matsayin Shugabar Jami'ar Abuja Ta Riƙon Kwarya, Biyo Bayan Karewar Wa'adin Mulkin Farfesa AbdulRashid Na'Allah Dake Cika A Ranar 30 Ga Watan Yuni.

Allah Ya Taya Riko!

Daga Jamilu Dabawa

Kaf Jáhohin Nájeriya Babu Jihar Da S**a Yi Dacen Gwamna Kamar...?Ƙarasa mana da naka ra'ayin….
27/06/2024

Kaf Jáhohin Nájeriya Babu Jihar Da S**a Yi Dacen Gwamna Kamar...?

Ƙarasa mana da naka ra'ayin….

ALLÁHU AKBÁR: Fitaccen Mawakin Annábi (S.A.W) Umar Adul'aziz Fadar Bege Kano Yau Yake Cika Shekara 11 Da RasuwaShin da w...
27/06/2024

ALLÁHU AKBÁR: Fitaccen Mawakin Annábi (S.A.W) Umar Adul'aziz Fadar Bege Kano Yau Yake Cika Shekara 11 Da Rasuwa

Shin da wacce waƙarsa ku ka fi tunawa da shi?

Rikicin sarauta: Ƴan siyasa ne s**a nemi Ado Bayero ya yi fada bayan an tsige shi – Gwamnatin KanoGwamna Abba Yusuf na j...
26/06/2024

Rikicin sarauta: Ƴan siyasa ne s**a nemi Ado Bayero ya yi fada bayan an tsige shi – Gwamnatin Kano

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano a ranar Laraba ya bayyana cewa wasu ’yan siyasa marasa kishin kasa ne s**a karfafa wa hambararren Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero kwarin guiwa da ya yi yaki bayan an tsige shi.

Da yake bayyana hakan ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Sanusi Bature, gwamnan ya ce wadannan ‘yan siyasa marasa kishin jiha ne ke da hannu a shari’ar kotun da ke kalubalantar tsige shi da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Da yake gabatar da shirin safe na gidan talabijin na Arise TV, mai magana da yawun gwamnan ya bayyana yakin da Bayero ya yi na tayar da zaune tsaye a matsayin wanda bai kamata ba.

Da yake jaddada cewa siyasa ta shiga cikin rikicin masarautar Kano, Bature ya bayyana cewa Sarki Muhammad Sanusi bai taba kalubalantar tsohuwar gwamnatin jihar ba a lokacin da aka tsige shi a 2019.

Idan za'a tuna cewa Gwamna Yusuf ya tsige Aminu Bayero ne a lokacin da yake nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano a watan Mayu.

Hakan ya biyo bayan matakin da majalisar dokokin jihar ta dauka na soke dokar masarautar Kano ta 2019.

Kalma Ɗaya Tak....
26/06/2024

Kalma Ɗaya Tak....

Hotunan Yadda Aka Fara Rabon Kayan Abincin Da Shugaba Tinubu Ya Aika Zuwa Jihohi Domin Rabawa TàĺàķàwaAikin rabon kayan ...
26/06/2024

Hotunan Yadda Aka Fara Rabon Kayan Abincin Da Shugaba Tinubu Ya Aika Zuwa Jihohi Domin Rabawa Tàĺàķàwa

Aikin rabon kayan abincin a Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika zuwa ga jihohi ya fara kankama. A waɗannan hotunan ana iya ganin rabon kayan abinci a jihohin Kano da Kaduna.

Kayan abinci da ake rabawa sun haɗa da masara, dawa da kuma gero.

Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji. Kashim Shettima ya ce Jam’iyyun APC, NNPP da PDP duk daya suke kuma abin da ya hada su ...
26/06/2024

Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji. Kashim Shettima ya ce Jam’iyyun APC, NNPP da PDP duk daya suke kuma abin da ya hada su ya fi karfin ya raba su.

Ya kuma ce Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf tsatsonsu ne.

Menene ra'ayinku?

YANZU-YANZU: Majalisar Dokokin Jihar Sokoto Ta Amince Da Sabuwar Dokar Rage Ikon Sarkin Músúlmí, Sa’ad Abubakar IIIDokar...
26/06/2024

YANZU-YANZU: Majalisar Dokokin Jihar Sokoto Ta Amince Da Sabuwar Dokar Rage Ikon Sarkin Músúlmí, Sa’ad Abubakar III

Dokar da aka gabatar wacce za ta buƙaci Sarkin Músúlmí sai ya samu amincewar gwamnati kafin ya naɗa sarakuna da hakimai a jihar Sokoto.

Me zaku ce?

Ya Zama Wajibi Mu Dawo Da Tambarin "Kwankwasiya Amana" Da Gwamnatin Ganduje Ta Goge A Gine-gine Da Makarantun Gwamnatin ...
26/06/2024

Ya Zama Wajibi Mu Dawo Da Tambarin "Kwankwasiya Amana" Da Gwamnatin Ganduje Ta Goge A Gine-gine Da Makarantun Gwamnatin Jihar Kano, Céwar Gwamna Abba

Menene ra'ayinku?

26/06/2024

ALLURA CIKIN RUWA: Murja Kunya Na Cigiyar Wanda Zasu Fara Yin Soyayya

Allàh ya bawa mai rabo sa'a.

YANZU-YANZU: Gwamna Abba Ya Ceto Iyalan Marigayi Sarki Ado Bayero Daga Wùĺàķànťa A Gidan HàýaDaga Hon. Saleh Shehu Hadej...
25/06/2024

YANZU-YANZU: Gwamna Abba Ya Ceto Iyalan Marigayi Sarki Ado Bayero Daga Wùĺàķànťa A Gidan Hàýa

Daga Hon. Saleh Shehu Hadejia

Gwamnan Jihar kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya ceto rayuwar y'ar marigayi Ado Bayero tarė da mahaifiyarta da d'an uwanta domin biya musu kudin hayar gida a jihar Lagos.

Zainab Jummai Ado Bayero tarė da mahaifiyarta da dan uwanta sun baiyyana yanayin kunci da suke ciki tun bayan rasuwar mahaifinsu marigayi Ado Bayero, sun kuma godewa Gwamna ta hannun mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa, domin zuwa da ya yi ya biya musu kudin hayar gida a daidai lokacin da ake shirin korarsu daga gidan hayar.

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin kayan miya ya fara saukowa a Najeriya Binciken gani da ido a bakin dogo kwandon tumatirin da ake ...
25/06/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin kayan miya ya fara saukowa a Najeriya

Binciken gani da ido a bakin dogo kwandon tumatirin da ake sayarwa Naira dubu 130,000 yanzu ya sauko zuwa Naira dubu N60,000

Ya labarin kayayyaki a wajajen ku?

24/06/2024

BIDIYO: Jihar Bauchi Ce Kan Gaba A Samun Cigaba A Fanin Ilimi Fiyeda Ko Wace Jiha A Aréwacin Najeriya A Ƙarƙashin Gwamnatin Sanata Bala Mohammed Ƙauran Bauchi

Wane fata zaku yi musu?

Ka Gaggauta Ficewa Daga Fadar Nasarawa Tun Kafin Mu Zo Gyare-Gyare, Sakon Gwamna Ababa Ga Sarki Aminu Ado BayeroMe za ku...
24/06/2024

Ka Gaggauta Ficewa Daga Fadar Nasarawa Tun Kafin Mu Zo Gyare-Gyare, Sakon Gwamna Ababa Ga Sarki Aminu Ado Bayero

Me za ku ce ?

INNÁ LILLAHÍ WA'INNÁ ILAIHI RAJI'UŃ'Yan Bìñdìģa Sun Ķašhè Farfesa Yusuf Sa'idu Na Jami'ar Usman Danfodiyo Dake Sokoto 'Y...
24/06/2024

INNÁ LILLAHÍ WA'INNÁ ILAIHI RAJI'UŃ

'Yan Bìñdìģa Sun Ķašhè Farfesa Yusuf Sa'idu Na Jami'ar Usman Danfodiyo Dake Sokoto

'Yan Bìñďìģa Sun Kàśhè Mataimakin Shugaban Jami'ar Usman Danfodiyo Mai Kula Da Bincike Da Kirkira, Farfesa Yusuf Sa'idu Har Lahira A Garin Kucheri Dake Kan Iyaka Zamfara Da Katsina, Yau Litinin

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Daga Jamilu Dabawa

WATASABÚWA: Gwamnan Sòkoto Na Yunƙurin Tsíge Sarkiñ Musúlmi, Céwar Ƙungiyar Kare Haƙƙin Músulmí, MURICƘungiyar ta kuma g...
24/06/2024

WATASABÚWA: Gwamnan Sòkoto Na Yunƙurin Tsíge Sarkiñ Musúlmi, Céwar Ƙungiyar Kare Haƙƙin Músulmí, MURIC

Ƙungiyar ta kuma gargadi Gwamnan ná Sokoto da ya kiyáye yunƙurín nasa.

Menene ra'ayinku?

Rundunar 'Yan Sanda Jihar Kano Ta Kai Samame Fadar Sarki Sunusi IIA yayin samamen rundunar 'yan sandan ta kori dukkanin ...
24/06/2024

Rundunar 'Yan Sanda Jihar Kano Ta Kai Samame Fadar Sarki Sunusi II

A yayin samamen rundunar 'yan sandan ta kori dukkanin mafarautar da suke gadan lafiyar Sarki Sunusi tare da mamaye inda Sarkin yake, kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana.

Ko me ya yi zafi haka?

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Fitaccen mawaƙin kudu, Davido zai angwance da masoyiyarsa Chioma Rowland bayan ta haifa masa yaraWane fata zaku yi musu?
23/06/2024

Fitaccen mawaƙin kudu, Davido zai angwance da masoyiyarsa Chioma Rowland bayan ta haifa masa yara

Wane fata zaku yi musu?

Ɓarayi sun b***e tagar másalláci sún sace Bátirin Mòta da'ake amfani dashi a Masallaci domin sauti na kimanin Naira dubu...
23/06/2024

Ɓarayi sun b***e tagar másalláci sún sace Bátirin Mòta da'ake amfani dashi a Masallaci domin sauti na kimanin Naira dubu 300 a Unguwar Aisami dake Kano.

Barayin sun ɓalle tagar masallaci s**a haura s**a sace babban batirin sola da'ake amfani da shi a Masallaci domin bada sauti da haske na kimanin Naira dubu ɗari 300 a unguwar Aisami da ke Kano.

A wannan zamani hatta masallatai ma basu tsira ba daga miyagun ayyukan ɓata gari/'yan dabada ke addabar al'ummar birnin Kano da sace sace.

Me zaku cé?

DUNIYA JUYI-JUYI: Wai Ina Fatima Mai Zogale Ta Shige Ne?
23/06/2024

DUNIYA JUYI-JUYI: Wai Ina Fatima Mai Zogale Ta Shige Ne?

SUBHANALLAH: 'Yan Bìñďìģa Sun Ķàśhe Mutane Tara Tare Da Sace Sama Da Hamsin A Katsina 'Ýan bindiga Sun Ķàśhè Mutañe Tara...
23/06/2024

SUBHANALLAH: 'Yan Bìñďìģa Sun Ķàśhe Mutane Tara Tare Da Sace Sama Da Hamsin A Katsina

'Ýan bindiga Sun Ķàśhè Mutañe Tara Da Sace Sama Da Mutum 50 Da Kone Motoci Tara Da Kone Shaguna Fiye Da Goma Sha Biyar Da Kuma Gidaje Da Dama A Wani Hari Da Su Ka Kwashe Awanni A Garin Maidabino Dake Karamar Hukumar Danmusa A Jihar Katsina, Daren Jiya Asabar

Allah Ya Jikansu Ya Kuma Kubutar Da Wadanda Aka Sace!

KUTURU DA KUDINSA...Mene Ne Aibu Don Barirah Ta Saka Takalmin Kimanin Naira Dubu Dari Biyu A Wankan Sallah?Takalmin da B...
23/06/2024

KUTURU DA KUDINSA...

Mene Ne Aibu Don Barirah Ta Saka Takalmin Kimanin Naira Dubu Dari Biyu A Wankan Sallah?

Takalmin da Barirah Musbahu ta saka bai kamata ya zama abin cece ku ce ba a kafofin sada zumunta ba.

Duk wanda ya san Barirah Musbahu ya san ta shahara ne wajen shiga gasar "GIVEAWAY" a kafofin sada zumunta, yanzu kuma ta zama cikakkiyar yar crypto (kasuwancin yanar gizo ta zamani).

Hakika idan ka san irin makudan Kuɗaɗen da ake samu a hakar crypto bai kamata ka fara tuhumar ta ina ta samu kuɗin sayan wannan takalmin mai tsada a matsayin ta na matashiyar budurwa.

Kuma duk wanda ya riki harkar crypto hannun bibbiyu to zaisa abinda yafi haka ma tsada saboda irin kuɗaɗen da ake samu a crypto kuma na halal ga wanda ya kiyaye haram.

Barirah Musbahu ba'a iya crypto ta tsaya ba 'yar kasuwa ce mai siya da siyarwa ta samu ribanta, dan haka ayi crypto kuma a haɗa da nasa'a domin tafi daɗi da kuma samun kuɗi lokaci guda.

Daga Hafiz Ali

Muna Roƙon Malamai Su Taimaka Wa Tawagar Ƙwallon Ƙafa Ta Najeriya Da Addu'a, Cewar Shugaba Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Super...
22/06/2024

Muna Roƙon Malamai Su Taimaka Wa Tawagar Ƙwallon Ƙafa Ta Najeriya Da Addu'a, Cewar Shugaba Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Super Eagle

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafan Najeriya Super Eagle, Ibrahim Musa Gusu, ya roƙi malamai su taimaka wa tawagar ƙwallon ƙafan Najeriya da addu'a domin ta samu nasarar shiga cikin rukunan ƙasashen da zasu buga gasar cin kofin duniya na 2026.

Me za ku ce?

WATASABUWA: Idris Abdulkarim da ya taɓa rera waƙar Nájeriya jâga-jâga ya buga wata sabuwar waƙa ya ce lamarin ƙasar a ya...
22/06/2024

WATASABUWA: Idris Abdulkarim da ya taɓa rera waƙar Nájeriya jâga-jâga ya buga wata sabuwar waƙa ya ce lamarin ƙasar a yanzu ya wuce a ce jâga-jâga

Menene ra'ayinku?

Aminu Ado Bayero bai taba zama Sarkin Kano ba, face Sarkin ƙwaryar garin Kano – Gwamnatin Kano Babban Sakataren Yaɗa Lab...
22/06/2024

Aminu Ado Bayero bai taba zama Sarkin Kano ba, face Sarkin ƙwaryar garin Kano – Gwamnatin Kano

Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano Sanusi Bature ya bayyana cewa Aminu Ado Bayero bai taba zama Sarkin Kano ba.

Bature ya ce tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin kananan hukumomi takwas na birnin Kano.

Da yake magana a gidan Talabijin na Arise, Bature ya ce Ganduje ya naɗa Bayero Sarkin Kano ne saboda batanci ga masarautar.

A cewar Bature Ganduje ya shigo da siyasa ne a Masarautar Kano saboda wani ra'ayin kansa.

Ya ce, “Aikin da Gwamnan na yanzu ya yi shi ne kare martabar masarautar a matsayinta na babbar Masarauta a Najeriya kafin daga bisani Najeriya da kundin tsarin mulkin kasar ta sauya tsarin da ya shafe shekaru sama da dubu inda mutane ke rayuwa tare a karkashin Sarki daya.

Gwamnatin Ganduje da ta shude ta yanke shawarar bata wannan tarihin inda ta shigo da siyasa a ciki.

Siyasantarwar da akayi wa Masarautar shi ne abin da Gwamna Yusuf ya yi alkawarin dawo da martabar da aka rasa a Gwamnatin baya.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka tsige Sarki ba. Ganduje ya tsige Sanusi inda ya bar Kano domin a samu zaman lafiya, a yanzu kuma Sanusi ya koma Kano bayan soke dokar da ta tsige shi.

Ina so in bayyana cewa Aminu Ado Bayero bai taba zama Sarkin Kano ba, an naɗa shi ne Sarkin Kananan Hukumomi takwas na birnin Kano.

Don haka da aka yi wa dokar kwaskwarima, Masarautar da Aminu ya yi aiki ba ta wanzu ba a yanzu domin dokar Masarautar ta 2019 ta lalata babbar masarautar.

Shi ne Sarkin Kano 14, amma ba wai ana nufin ikonsa na kananan hukumomi 44 na Kano ba ne, kawai na kananan hukumomi takwas ne da ke cikin gari.

Gwamna Yusuf ya tsige Ado Bayero ne a lokacin da ya maido Muhammad Sanusi a matsayin Sarkin Kano.

Duk da matakin da Gwamna ya ɗauka, Aminu Ado Bayero ya ki barin fadar sa ta Nassarawa.

Tun daga lokacin ne Bayero ya ki amincewa da matakin da Gwamnatin Jihar ta dauka inda ya ƙalubalence ta a gaban kotu.

Address

Zoo Road
Kano
700224

Telephone

+2348101029115

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Nearby media companies