Hantsi24

Hantsi24 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hantsi24, Media/News Company, Kano.
(6)

12/12/2024

Zaku iya hawan wannan Motar domin zuwa neman Kudi?

Dalibai Sun Rasa Ransu Yayin Murnar Kamala Karatu A Maiduguri.Wasu ɗaliban dake murnar kammala karatu a jami'ar jihar Bo...
12/12/2024

Dalibai Sun Rasa Ransu Yayin Murnar Kamala Karatu A Maiduguri.

Wasu ɗaliban dake murnar kammala karatu a jami'ar jihar Borno sun mutu, yayinda wasu s**a samu raunuka a lokacin da motar dake ɗauke da su tayi taho mu gama da wata babbar motar ɗaukan kaya mallakin kamfanin Dangote

Allah ya jiƙan su.

~ Haji Shehu

12/12/2024

Yaushe rabon ku da wutar lantarki 💡 ?

12/12/2024

An Yafewa Garba! Sabuwar Wakar da akai kan sulhu Delu da Garba!

Jiya ba yau ba ko kun ganesu?
12/12/2024

Jiya ba yau ba ko kun ganesu?

Allah ya baka ikon sauke nauyi da ka dauka!
11/12/2024

Allah ya baka ikon sauke nauyi da ka dauka!

Frank-Walter Steinmeier  Shugaban ƙasar Jamus Ya Fara Ziyarar Aiki A NajeriyaA yau ne shugaban ƙasar Jamus Frank-Walter ...
11/12/2024

Frank-Walter Steinmeier Shugaban ƙasar Jamus Ya Fara Ziyarar Aiki A Najeriya

A yau ne shugaban ƙasar Jamus Frank-Walter Steinmeir
ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe inda ministan birnin tarayyar Abuja Nyesom Wike ya tarbeshi.

A ziyarar da shugaban na Jamus Steinmeier ya kawo Najeriya zai tattauna da shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma shugaban Kungiyar Tatttalin Arzikin Ƙasashen Afika ta Yamma ECOWAS Alieu Omar Touray.

Shugaban na Jamus zai kuma je birnin Lagos domin tattaunawa da wakilan ƴan kasuwa da wakilai a fannin al’adun ƙasar da kuma kungiyoyin fararen hula da tattaunawa da Dr Nike Okundaye da Prof Wole Soyinka.

Ana ganin shugaban na Jamus Frank-Walter Steinmeier zai samu damar zagayawa a birnin Lagos domin ganin irin ci gaban da aka samu da ma ƙalubalan da muhalli ke fuskanta da sauransu.

Jihohin Najeriya da dama na fama da matsalar karancin kudi wato ‘kash’Wanda hakan ke durkusar da harkokin kasuwanci musa...
11/12/2024

Jihohin Najeriya da dama na fama da matsalar karancin kudi wato ‘kash’

Wanda hakan ke durkusar da harkokin kasuwanci musamman a wasu kauyukan, inda mutane Kauyen ke kin yadda da a tura masu Kudi ta banki domin sayen kayansu sai da a basu Kudi a zahiri.

Ya lamarin yake a inda kuke?

10/12/2024

Labarin da Muke samu yanzu haka 'yan ana fadan Daba a Kofar Mata! Yau kusan Kwana uku kenan ana wannan fadan shin mai jami'an Tsaro suke dan shawo kan wannan Matsalar?

Idan Mijinki ya dakeki ki rama?
10/12/2024

Idan Mijinki ya dakeki ki rama?

Daliban Jami'ar Tarayya Dake Dutsenma akan Tankar Mai Zasuje Matsugunin Jami'ar Na Din Din-din Domin Daukar Darasu Wato ...
08/12/2024

Daliban Jami'ar Tarayya Dake Dutsenma akan Tankar Mai Zasuje Matsugunin Jami'ar Na Din Din-din Domin Daukar Darasu Wato Lecture.

Daliban a saman Tankar mai a hanyar ta zuwa mazaunin makarantar na din din-din sabo da rashin motar makarantar wacce a baya take diban daliban zuwa can Domin daga cikin gari zuwa Jami'ar yakai nisan Kilomita 24.

Idan baka taba zuwa Jam'iar ba bazaka taba ganewa ba.

08/12/2024

Zalunci Ne Ka Dauki Kudin Karamar Hukumar Ajingi Kaje Cikin Birni Kai Gada Da Shi Inji Sanata Abdulrahaman Kawu Sumaila.

DCL Hausa sun Ruwaito Sanata Kawu Sumaila na wannan jawabi a taron bawa manoma jari da ya gudanar a karshen wannan makon.

07/12/2024

Ina Goyon Bayan Gyara Dokokin Haraji Amma Akwai Gyare-gyaren Da Ya Kamata Ai Masu.

A tattaunawar da mukai da Prof Mustapha Bagudo Muhammad ya bayyana cewar tsoron da 'yan Arewa suke na gyaran Dokokin Haraji abin tsoron bai kai yadda ake rurutawa ba.

Akwai abubuwa masu kyau acikin wadannan Dokokin sai a duba inda ake ganin gyara Kuma a gyara.

Faruq Lawan Ya Bayyana Cikin Shigar Kwankwasiyya Tsohon Dan Majalisar Tarayya na mazabar Bagwai da Shanono Faruq Lawan, ...
07/12/2024

Faruq Lawan Ya Bayyana Cikin Shigar Kwankwasiyya

Tsohon Dan Majalisar Tarayya na mazabar Bagwai da Shanono Faruq Lawan, ya bayyana cikin shigar Kwankwasiyya, tun fitowarsa daga gidan gyara halin ake rade-radin cewar NNPP Kwankwasiyya yake ko PDP.

Domin tun 1999 Hon Faruq yake wakiltar mutanen Bagwai da Shanono a Majalisar Wakilai ta tarayya a Tutar PDP ba tare da yayi rawa ba ko canza Jam'iyya ba.

Bayyanarsa cikin wannan shiga ta Kwankwasiyya ta kawo karshen rade-radin da ake na Jam'iyyar da yake ci.

Ko wanne fata kukewa Faruq Lawan?

06/12/2024

Zanga-zangar ta barke a Masarautar Bichi kan cewar Masarautar Bichi basu yadda akai masu Hakimi ba, a Cewar mutanen garin Bichi Masarautar ce mai masarauta ce mai Daraja ta daya!

06/12/2024

Duk da kawanyar da jami'an Tsaro s**aiwa fadar Sarkin Kano bai hana sarki Muhammad Sunusi fitowa zaman fada ba!

Allah ya jikan Hajiya Saratu Gidado Daso ta rasu Yan watanni kadan da bikkin Murnar zagayowar ranar haihutar inda tai mu...
06/12/2024

Allah ya jikan Hajiya Saratu Gidado Daso ta rasu Yan watanni kadan da bikkin Murnar zagayowar ranar haihutar inda tai murnar cikarta shekara 33 da haihuwa.

Allah ya kyautata makwancinta.

Ko Ina Labarin Shari'ar Chuchu Ya Kwana? Idan baku manta yanzu haka Chuchu na gidan gyaran halin inda take dakon yanke h...
06/12/2024

Ko Ina Labarin Shari'ar Chuchu Ya Kwana?

Idan baku manta yanzu haka Chuchu na gidan gyaran halin inda take dakon yanke hukunci bisa Zargin da ake mata na Ķàśhè wani matashi dan asalin Bauchi dake zama a Kano mai suna Nafi'u Gorondo.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hantsi24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share