09/08/2023
Menene Takaddar Licence MTFE Suke Da Ita, Ta FINTRAC Da MSB Dake Canada?
Menene Shaidar FINTRAC..?
Abinda FINTRAC dai yake nufi shine “Financial Transaction And Report Analysis Centre Of Canada”. Hukuma ce mai gudanar da abinda ake kira “Financial Intelligence Unit And Regulatory Agency”, a takaice dai hukuma wacce a iya kwatantata da hukumar EFCC dake Nigeria.
Hukumar tana yaki ne da AML “Anti Money Laundering”, CTF “Counter-Terrorist Financing”, sannan kuma ita ce take yaki da duk wani kalar laifi da ake yi na kudi k**a daga damfarar kudi na zahiri dana internet. Hukumar FINTRAC tana gudanar da ayyukanta ne ta hanyar karbar duk wasu bayanai a gurin kamfanunuwa, har da bayanan da bazasu iya fada a public ba.
Akwai Abubuwa Guda Shida Da FINTRAC Take Tabbatarwa Kafin Ta Baka Shaida.
1. COLLECTING INFORMATION; FINTRAC tana karbar bayanai na kasuwancinka, kafin ta baka shaida.
2. ANALYZING DATA; Bayanan da s**a karba zasu tsaya su tabbatar bayanan naka daidai ne ko karya ne, sai sun tabbatar ba karya a ciki.
3. DISSEMINATING INTELLIGENCE; Ita hukumar FINTRAC tana daukar dukkan bayanan data samu a gurinka, sai ta tura su zuwa hukumar CSIS “Canadian Security Intelligence Service”, k**ar dai ace a Nigeria hukumar NIA da DSS. Su gudanar da binkice na tsaro akan bayanan daka tura.
4. REGULATORY OVERSIGHT; Hukumar tana tsayawa bayan binkice ta tabbatar bayanan daka bayar sunyi daidai da abinda s**ayi binkice akanka.
5. GUIDANCE AND EDUCATION; Banda binkice kuma, akwai wayar da kai da hukumar take bawa duk wanda ya chanchanci shaidar ta. Wayar dakai akan yadda zaiyi ya bi dokar kasar.
6. MONITORING AND ENFORCEMENT; Duk bayan baka shaidar, hukumar zata ci gaba sa bibiyarka ta tabbatar kana bin ka’idar da s**a dora maka. Idan kuma ka sauka toh an basu dama su rufe kasuwancinka.
Menene Shaidar MSB…?
Kafin ka samu shaidar MSB “Money Service Bussiness” akwai sharudda guda 12 da dolenka sai ka cika su.
1. FINTRAC LICENCE; Dole ma sai kana da shaidar FINTRAC kafin a sau