Mahanga

Mahanga Ingantattun Labarai da Ra'ayoyi da dumi-dumi daga ko ina a fadin Duniya visit our website at www.mahanga.ng
(3)

INDA RANKA: Hisbah ta yi wa ma'auratan da s**a yi kome bayan saki Uku, har da malamin da ya mayar da auren an yi masa bu...
28/03/2024

INDA RANKA: Hisbah ta yi wa ma'auratan da s**a yi kome bayan saki Uku, har da malamin da ya mayar da auren an yi masa bulala....

Hukumar Hisba a Katsina ta yi ma wasu ma'aurata bulala da s**a yi kome bayan sun rabu saki Uku, hukumar ta haɗa har da Malamin da ya maida masu Auren ta yi masu bulala,

Mahanga ta ruwaito Lamarin ya faru ne a yau Laraba a garin Ajiwa dake ƙaramar hukumar Batagarawa, inda aka yi wa Yakubu Husamatu Ajiwa da Nafisa Adamu Ajiwa wanda ya saketa saki uku da kuma wani malami Abdurrahaman Abdurra'uf wanda ya jagorancin mayar da Auren akan Naira dubu hudu (4000)

DA DUMI-DUMI: Gidan man NNPC a Yola ya k**a da wuta...Gidan man NNPC dake kan titin Bank Road, Galadima Aminu Way a Jime...
27/03/2024

DA DUMI-DUMI: Gidan man NNPC a Yola ya k**a da wuta...

Gidan man NNPC dake kan titin Bank Road, Galadima Aminu Way a Jimeta, dake Yola cikin jihar Adamawa ya k**a da wuta... kawo yanzu ba a san musabbabin tashin wutar ba...

OPAY: Naku ya dawo?
27/03/2024

OPAY: Naku ya dawo?

27/03/2024

A shekara nawa ya k**ata a matsawa yara su fara azumi? 🥹🫣

KUNA DA LABARIN: Gwamna Abba ya nemi majalisa ta amince masa ya kafa ƙarin sabbin ma'aikatu huɗu a KanoMahanga ta ruwait...
27/03/2024

KUNA DA LABARIN: Gwamna Abba ya nemi majalisa ta amince masa ya kafa ƙarin sabbin ma'aikatu huɗu a Kano

Mahanga ta ruwaito Sabbin ma'aikatun sune ma'aikatar Kula da Jin ƙan jama'a da kawar da talauci wato Humanitarian Affairs and Poverty Eradication;

Sai ma'aikatar samar da wuta da kula da ma'adanai wato Solid Minerals Resources, Power and Renewable Energy,

Da kuma ma'aikatar tsaron cikin gida wato Internal Security

Sannan sai kuma ma'aikatar ayyuka na musamman wato Special Service

Kuna maraba da wannan yunkuri na Gwamna Abba Kabir Yusuf?

K¡san Sojojin da aka yi a Delta yana da matukar tada hankali – inji Shugaban SojiYa ce lokaci guda yara 21 sun zama mara...
27/03/2024

K¡san Sojojin da aka yi a Delta yana da matukar tada hankali – inji Shugaban Soji

Ya ce lokaci guda yara 21 sun zama marayu, mata 10 sun zama zawarawa, kuma cikinsu akwai masu cikin wata 2, 4, 5, 8.... shugaban sojojin wanda ke jawabi yanzu a wajen jana'izar sojojin su 17 da aka ka$$he ya ce ba za su yarda ba sai sun zaƙulo waɗanda s**a yi wannan aika-aika.

DA DUMINSU: Babu aiki ranar Juma'a 29 ga watan Maris da kuma ranar Litinin 1 ga watan Afrilu 2024 a Najeriya Ministan ci...
27/03/2024

DA DUMINSU: Babu aiki ranar Juma'a 29 ga watan Maris da kuma ranar Litinin 1 ga watan Afrilu 2024 a Najeriya

Ministan cikin gida ya ce Gwamnatin tarayya ta bayar da ranakun a matsayin hutun Good Friday da kuma Easter

DA DUMI-DUMI: An kawo gawar sojoji 17 da aka ka$$he a Delta domin yin jana'izarsu da binzne su a maƙabartar sojoji dake ...
27/03/2024

DA DUMI-DUMI: An kawo gawar sojoji 17 da aka ka$$he a Delta domin yin jana'izarsu da binzne su a maƙabartar sojoji dake Abuja yanzu haka....

YAU DA GOBE: Wannan fa kayan wani attajirin mai kuɗi ne a shekarun baya a 1990's... mu bi duniya ahankali jama'a...
27/03/2024

YAU DA GOBE: Wannan fa kayan wani attajirin mai kuɗi ne a shekarun baya a 1990's... mu bi duniya ahankali jama'a...

LABARI: Tinubu ya taya sabon shugaban ƙasar Senegal mai shekara 44 da haihuwa murnar lashe zabe
27/03/2024

LABARI: Tinubu ya taya sabon shugaban ƙasar Senegal mai shekara 44 da haihuwa murnar lashe zabe

Halin da Kanawa s**a tsinci kansu.... 🤔-Daga Shehu Caji
27/03/2024

Halin da Kanawa s**a tsinci kansu.... 🤔

-Daga Shehu Caji

KUN JI FA: Ƙasashen Turai na shawarar daina turo Gwanjo Afrika Dillalan Gwanjo a Kenya suna shirin yin zanga-zanga domin...
27/03/2024

KUN JI FA: Ƙasashen Turai na shawarar daina turo Gwanjo Afrika

Dillalan Gwanjo a Kenya suna shirin yin zanga-zanga domin nuna adawa da matakin da ƙasashen Faransa, da Denmark, da Sweden ke shirin dauka na hana fitar da kayan sawa (Gwanjo) daga Tarayyar Turai (EU) zuwa Afrika

WOW: Shafukan sada zumunta 10 da aka fi ziyarta a 2023 Sashin ƙididdiga na Lifesight ya fitar da rahoton dandalin sadarw...
27/03/2024

WOW: Shafukan sada zumunta 10 da aka fi ziyarta a 2023

Sashin ƙididdiga na Lifesight ya fitar da rahoton dandalin sadarwa 10 da aka fi ziyarta a 2023 k**ar haka.... za mu fara daga na ƙarshe.....

10. Quora (19 billion visits)
An ziyarci dandalin Quora, sau Biliyan 19 kuma Maza ne s**a fi ziyartar shafin da kaso 67.5%, sannan kashi 73.37% na maziyarta shafin da wayoyin hannu suke ziyartarsa.

9. Twitch (20 billion visits)
Mutum Biliyan 20 ne s**a ziyarci Twitch wanda galibi na masu sha'awar Games ne.

Shima dai Twitch maza ne s**a fi ziyartarsa da kaso 75% sai dai kashi 43.43% ne kacal suke ziyartarsa da wayoyin hannu.

8. LinkedIn (20.5 billion visits)
Shi kuwa LinkedIn, mutum Bilyan 20.5 ne s**a ziyarce shi. Duk da dai shima din maza ne s**a fi ziyartarsa da kaso 68%, amma dai kashi 67.73% na masu ziyartarsa da kwamfuta ne suke shiga.

7. WhatsApp (31.3 billion visits)
Dandalin WhatsApp shine na 7 inda mutum Bilyan 31.3 s**a ziyarce shi kuma kashi 81% maza ne amma kuma kashi 64.37% da kwamfuta suke ziyartarsa.

6. TikTok (41.8 billion visits)
Shafin TikTok ne na 6, bayan ya samu maziyarta 41.8 billion a 2023.

Kashi 69% maza ne kaso 31% kuma mata ne, sannan kaso 78.35% da wayoyin hannu suke shigarsa.

5. Reddit (81 billion visits)
Reddit ya samu maziyarta 81.0 billion, maza 69%, kuma kaso 72.27% da wayoyin hannu s**a shiga.

4. Instagram (87.3 visits)
Instagram ya samu maziyarta 87.3 billion, maza 67% mata 33% sannan kashi 58.05% da wayoyin hannu s**a shiga.

3. X (Twitter) 112.9 billion visits
X wanda aka fi sani da Twitter, shine na Uku inda ya samu maziyarta 112.9 billion kuma kaso 57%, maza ne sannan kaso 77.51% s**a shiga da wayoyin hannu.

2. Facebook (216.4 billion visits)
Facebook shine na Biyu inda aka ziyarce shi sau Biliyan 216.4,

Kaso 66% maza ne sannan duka ana amfani da wayoyin hannu da kwamfuta wajen shigarsa.

1. YouTube (1.35 trillion visits)
Shafin sadarwa da aka fi ziyarta a 2023 shine YouTube, wanda ya samu maziyarta Tiriliyan 1.35

Kaso 67%, maza ne s**a ziyarce shi kuma kaso 69.96% da wayoyin hannu suke ziyartarsa....

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin Dala ya yi muguwar faɗuwa a safiyar yau inda ake sayar da ita kan N1,000 zuwa 900 a AbujaRahotann...
27/03/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin Dala ya yi muguwar faɗuwa a safiyar yau inda ake sayar da ita kan N1,000 zuwa 900 a Abuja

Rahotanni masu tushe sun tabbatar da a safiyar wannan rana, Dala ta yi rugu-rugu ta faɗo ƙasa warwas inda ake saida kowace ɗaya akan Naira 1,000 a yankin (Zone 4) kusa da Otel ɗin Sheraton dake birnin tarayya, Abuja. Sannan a wasu wuraren ma har akan Naira 900 ake sayar da ita.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a fitar da Naira Biliyan 1.6 domin a tallafawa manoman citta a NajeriyaA ƙoƙarin shaw...
27/03/2024

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a fitar da Naira Biliyan 1.6 domin a tallafawa manoman citta a Najeriya

A ƙoƙarin shawo kan matsalar annobar da ta faɗawa citta wadda ta jawo hasarar citta dayawa a Najeriya musamman a Kudancin Jihar Kaduna, mai girma ministan noma na Najeriya Sanata Abubakar Kyari CON, ya ƙaddamar da kwamitin da zai kula wajen shawo kan annobar ƙarƙashin jagorancin ƙaramin ministan noma, Sabi Aliyu.

Sen. Abubakar Kyari CON, ya bayyana cewa wannan yunƙuri ne na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an magance matsalar annobar da ta faɗawa jinjar wadda ta haifar wa manoma hasarar sama da Naira Biliyan 12 a ƙasa gaba ɗaya.

Baya da haka, Minista Kyari ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya ba da umarnin a ware Naira Biliyan 1.6 domin a tallafawa manoman cittar waɗanda wannan iftila'i ya afkawa duba da yadda noman citta yake taimakawa ƙasa da wadataccen abinci gami da tasirin da take da shi wajen ɗaga darajar kayayyakin da Najeriya take samarwa (GDP).

27/03/2024

Da me zai fi ɗaɗin yin sahur ga wanda ya farka yanzu? 🫣🤭😢

MUHAWARA: Inda su MTN, Airtel, Glo, 9Mobile za su maido maku da duka kuɗaɗen da kuka saka katin kira da Data, nawa kuke ...
26/03/2024

MUHAWARA: Inda su MTN, Airtel, Glo, 9Mobile za su maido maku da duka kuɗaɗen da kuka saka katin kira da Data, nawa kuke hasashen za ku samu?

Mai kuɗin Amurka yayi tayin zai sayi TikTok Billionaire ɗin ƙasar Amurka Kevin O'Leary, mamallakin Shark Tank ya yi tayi...
26/03/2024

Mai kuɗin Amurka yayi tayin zai sayi TikTok

Billionaire ɗin ƙasar Amurka Kevin O'Leary, mamallakin Shark Tank ya yi tayin a sayar masa da kamfanin sadarwa na TikTok kan kuɗi Ɗala Ɓilyam $20 zuwa $30

A ganin ku farashin TikTok zai kai nawa?

LABARI: Rundunar yan sandan Najeriya ta dage ranakun tantance sabbin kuratan yan sanda zuwa ranar 16 ga watan Afrilu 202...
26/03/2024

LABARI: Rundunar yan sandan Najeriya ta dage ranakun tantance sabbin kuratan yan sanda zuwa ranar 16 ga watan Afrilu 2024

Kakakin rundunar Ikechukwu Ani ya ce an dauki matakin dage ranakun medical screening din ne saboda azumin Ramadana da kuma hutun kirista

DA DUMI-DUMI: Matar da ta kamo hanya tana tuƙo kanta a mota daga London zuwa Najeriya Pelumi Nubi, tayi hatsari,Ana farg...
26/03/2024

DA DUMI-DUMI: Matar da ta kamo hanya tana tuƙo kanta a mota daga London zuwa Najeriya Pelumi Nubi, tayi hatsari,

Ana fargabar tayi hatsarin ne a yankin ƙasar Liberia

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Kano ya nada ɗan Kwankwaso a matsayin Kwamishina Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Mustapha Ra...
26/03/2024

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Kano ya nada ɗan Kwankwaso a matsayin Kwamishina

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Mustapha Rabiu Kwankwaso, yaron cikin Kwankwaso da Adamu Aliyu Kibiya, da Usman Shehu Aliyu da kuma Abduljabbar Garko a matsayin Kwamishinoni,

Ya tura sunayensu majalisar dokokin jihar domin tantancewa

DA DUMI-DUMI: Kotu ta yanke wa ɗan Chinan da ya ka$$he Ummi hukuncin k¡$sa ta hanyar rątáya
26/03/2024

DA DUMI-DUMI: Kotu ta yanke wa ɗan Chinan da ya ka$$he Ummi hukuncin k¡$sa ta hanyar rątáya

LABARI: Gwamnoni sun nemi a basu dama su kafa hukumar wutar lantarki a jihohinsu Jihohi 12 daga cikin 36 sun nemi Gwamna...
26/03/2024

LABARI: Gwamnoni sun nemi a basu dama su kafa hukumar wutar lantarki a jihohinsu

Jihohi 12 daga cikin 36 sun nemi Gwamnatin tarayya ta basu dama su kafa tasu hukumar kula da wutar lantarki a jihohin su domin samun damar haɗa tasu wutar lantarkin.

Kun gamsu cewa Gwamnan jihar ku zai iya samar maku da wutar lantarki?

DA DUMI-DUMI: Ƙasar Togo ta canza kunɗin tsarin mulki sannan ta watsar da tsarin shugaban ƙasa ta dauko tsarin framinist...
26/03/2024

DA DUMI-DUMI: Ƙasar Togo ta canza kunɗin tsarin mulki sannan ta watsar da tsarin shugaban ƙasa ta dauko tsarin framinista

Majalisar Dokokin ƙasar Togo sun sanar da amincewa da sabon tsarin mulki a ƙasar wanda zai tashi daga tsarin Shugaban ƙasa zuwa tsarin Framinista, sannan zai zama tsarin zango 1 shekara 6 a madadin shekara 5 sau Biyu da ƙasar ke amfani dashi a yanzu.

DA DUMI-DUMI: Ɗan takarar Gwamnan jihar Ondo na jam'iyyar APC ya mutuMista Paul Akintelure, wanda ƙwararren likita ne ku...
26/03/2024

DA DUMI-DUMI: Ɗan takarar Gwamnan jihar Ondo na jam'iyyar APC ya mutu

Mista Paul Akintelure, wanda ƙwararren likita ne kuma dan siyasa ya mutu a wani asibiti dake Lagos, a baya-bayan nan sai da ya kwarmata cewa ana yiwa rayuwarsa barazana.

LABARI: An yanke wa tsohon shugaban kwallon kafa na ƙasar China hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda karɓar cin hanciGwamna...
26/03/2024

LABARI: An yanke wa tsohon shugaban kwallon kafa na ƙasar China hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda karɓar cin hanci

Gwamnatin shugaba Xi Jinping ta daure shugaban kungiyar ƙwallon ƙafa na ƙasar, CFA, Xuyuan Chen ɗaurin rai-da-rai saboda zarginsa da karɓar cin hancin Ɗala milyan $11m, wannan na zuwa ne bayan an dauki mak**ancin wannan mataki kan manyan jami'an hukumar ta CFA su 10.

Mahanga ta ruwaito Shugana Xi Jinping ya ce ba zai lamunci cin hanci da rashawa ba a Gwamnatinsa

26/03/2024

Subhanallahi, kun san wa ya makara yau?
🫣🤭😬🥺🥹😵

WATA SABUWA: Babbar kotun India ta haramta makarantun Islamiyya a ƙasarBabbar kotun Allahabad High Court dake Uttar Prad...
26/03/2024

WATA SABUWA: Babbar kotun India ta haramta makarantun Islamiyya a ƙasar

Babbar kotun Allahabad High Court dake Uttar Pradesh ta haramta tsarin karatun Islamiyya a ƙasar bayan da ta rushe dokar da ta bayar da yancin kafa makarantun Islamiyya mai suna Madrasa Act of 2004,

Mahanga ta ruwaito Kotun ta ce bai yiwuwa wani addini ya kafa tsarin karatu na daban da zai riƙa koyar da karatu da aƙidunsa. Don haka ta umurci a kwashe duk ɗaliban Islamiyyu a mayar da su firamare wato makarantun Bokon ƙasar.

Kuyi following shafin =>> Mahanga domin samun labari na gaba....

KO KUN SAN: Wannan ita ce saniya mafi tsada a duniya da aka sayar a ƙasar Brazil, an sayar da ita akan kudi dala miliyan...
25/03/2024

KO KUN SAN: Wannan ita ce saniya mafi tsada a duniya da aka sayar a ƙasar Brazil, an sayar da ita akan kudi dala miliyan $4.8m kwatankwacin Naira Bilyan 7.720bn a kudin Najeriya

Najeriya ce ƙasa ta Biyu da aka fi samun ƴayan da aka haifa ba ta hanyar aure baDaga Mahanga A ƙididdigar da wata cibiya...
25/03/2024

Najeriya ce ƙasa ta Biyu da aka fi samun ƴayan da aka haifa ba ta hanyar aure ba

Daga Mahanga

A ƙididdigar da wata cibiyar nazari mai zaman kanta ta fitar ta nuna cewa ƙasar Jamaica ce ta fi kowace kasa yawan samun ƴaƴan da aka haifa ba tare da aure ba da kashi 34.6%,

Mahanga ta ruwaito sai Najeriya ta zo na biyu da kashi 30%, sai Canada 2.8%, sai Birtaniya 1.6%, sannan sai Faransa 1.4%.

Address

N0 5ABC Yakubu Gawon Way
Kaduna
800273

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mahanga posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mahanga:

Videos

Share


Other Kaduna media companies

Show All

You may also like