Jaruma Hausa

Jaruma Hausa Domin tunawa da bada muhimmanci ga al'adun muna gargajiya musamman a kasar hausa/fulani da kare martabar gidajen muna gado
(1)

Dr. Abubakar Imam Kenan Shahararren Marubucin Kasar Hausa, Kuma Fitacce A AfirikaAlhaji Dr. Abubakar Imam shahararren ma...
19/06/2024

Dr. Abubakar Imam Kenan Shahararren Marubucin Kasar Hausa, Kuma Fitacce A Afirika

Alhaji Dr. Abubakar Imam shahararren marubucin kasar hausa kenan marubucin littafin 'RUWAN BAGAJA' da 'MAGANA JARI CE'. Wanda ya taimaka wajen samar da jaridar Hausa ta farko a duniya mai suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo' a shekarar 1939.

Shi ne Editan farko na wannan jaridar. Ya bada kyakkyawar gudummawa wajen yada al'adun hausawa tare da yada shi kansa yaren ta hanyar yin rubuce rubuce masu yawa.

Fata Allah ya yi masa rahama.

Daga Nura Sagir

JIYA BA YAU BA...Nan Wasu Alhazai ne mata, Yayin da Suke Sauka a Filin Jirgin Saman Kano daga Ƙasa Mai Tsarki, Kuna Iya ...
01/06/2024

JIYA BA YAU BA...

Nan Wasu Alhazai ne mata, Yayin da Suke Sauka a Filin Jirgin Saman Kano daga Ƙasa Mai Tsarki, Kuna Iya Lura, da wata mata rike tukunya da Buta a Hannunta An ɗauki Hoton Cikin Shekarar 1961.

Allah ya jikan Magabatan mu.

JIYA BA YAU BA: Hoton Sarki Sanusi Mai Murabus (Kakan Sarki Sanusi II) Tare Da Kaninsa Alhaji Ado Bayaro (Mahaifin Sarki...
28/05/2024

JIYA BA YAU BA: Hoton Sarki Sanusi Mai Murabus (Kakan Sarki Sanusi II) Tare Da Kaninsa Alhaji Ado Bayaro (Mahaifin Sarki Aminu Ado) A Shekarun Baya

Allah Ya hada kan zuri'arsu da suke raye. Domin 'yan uwan juna ne.

Sarkin Kano Abdullahi Bayero, An haifeshi 1881, ya rásu 1953, ya zama Sarkin Kano 1926, ya haifi Sarkunan Kano guda 2, S...
27/05/2024

Sarkin Kano Abdullahi Bayero, An haifeshi 1881, ya rásu 1953, ya zama Sarkin Kano 1926, ya haifi Sarkunan Kano guda 2, Sarki Sir Muhammadu Sunusi I, da Kuma Sarki Ado Bayero, A cikin jikokinsa an samu Sarakuna 2, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Sai kuma Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero

Sai kuma jikan Dan sa Muhammadu Sunusi II wadda Dan Chiroman Kano Aminu Sunusi Bayero ne Dan Sarki Sir, Muhammadu Sunusi I

Allah ya jikan mazan Jiya.

Good Night Bauchi (peal of tourism)    don't forget this location
27/05/2024

Good Night Bauchi (peal of tourism)
don't forget this location

Sarki dan sarki jikan sarki. Allah ya kara lafiya da jan kwanan mai martaba.Duba da kyau ko zaka iya ganeshi.
20/05/2024

Sarki dan sarki jikan sarki.
Allah ya kara lafiya da jan kwanan mai martaba.

Duba da kyau ko zaka iya ganeshi.

Amarya, uwar gida. Ki daure kiyiwa angonki wannan hadin k**ar yadda kika ganshi a hoto.Ki siyo Kubewarki danya, ki wanke...
15/05/2024

Amarya, uwar gida. Ki daure kiyiwa angonki wannan hadin k**ar yadda kika ganshi a hoto.

Ki siyo Kubewarki danya, ki wanke ta sosai da ruwa, sai ki yayyaka ta, ki zuba a cikin ruwa. Ki barta ta kwana a cikin ruwan.

Sai mai gida ya dunga shan ruwan, so samu ne ya sha na tashon sati guda, kafin wani abu ya shiga tsakanin Ku, a samu Zuma Mai kyau a zuba a cikin Hadin.

insha'Allah indai matsala ta rashin kuzari ce, rashin gamsar da iyali, rashin dogon zango, da kuma low s***m count, ta zo karshe.

A dunga shan Hadin sau biyu a rana. Daga sanda Ka fara amfani da wannan hadin masu saida maganin karfin maza sun daina cin kudin ka.

Allah yasa a dace. Amin

Muhimmancin ajiye mage a gida1. Mage na hana mugun halitta zama a kowani gida2. A duk lokacin da aka ji mage na kuka, wa...
15/05/2024

Muhimmancin ajiye mage a gida

1. Mage na hana mugun halitta zama a kowani gida

2. A duk lokacin da aka ji mage na kuka, wata alama ce ta gargadi ga mutanen gida

3. A duk lokacin da mutum ke bacci da mage kusa da shi, babu wani mugun halitta da zai kusanceshi a wannan lokaci domin suna tsoron mage. Kafin su kusanci mutum, sai sun ce za su kirga gashin da ke bindinsa kuma kafin su gama ya karkada bindin wanda hakan zai rikita su har su ce sai sun sake kirgawa kuma.

Madogara: Life in Saudi Arabia

"Ja'afaru bajimi dan Isiyaku , Sarkin Zazzau ya hade maza - Marigayi Salihu Jankidi Allahu Akbar, kasa hoton 'yaya ukku ...
12/05/2024

"Ja'afaru bajimi dan Isiyaku , Sarkin Zazzau ya hade maza - Marigayi Salihu Jankidi
Allahu Akbar, kasa hoton 'yaya ukku Kenan da Marigayi Sarkin Zazzau Ja' afaru Dan Isiyaku ya rasu ya bari a duniya. Na farko shine Muhammadu Aminu Ja'afaru (ya rasu shekara daya bayan rasuwar mahaifinsu) , ta biyu kuwa babbar yayarsu ce, Gimbiya Maryam(Talle) Ja'afaru sai kuma autan su maigirma Madakin Zazzau Malam Mannir Ja'afaru. Allah ya jikan Sarki Ja'afaru ya akbarkaci abunda ya bari. Ameen.

Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un 💔 😭 Yau Marigayi Chiroman Kano Aminu Sanusi Mahaifin Mai Martaba Sarkin na 14 Khalif...
08/05/2024

Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un 💔 😭

Yau Marigayi Chiroman Kano Aminu Sanusi Mahaifin Mai Martaba Sarkin na 14 Khalifa Muhammad Sanusi II Yake
Cika Shekara 24 Da Rasuwa.

Allah ya jaddada Masa Rahma Tare da Musulmi Baki Daya.

Rijiyar da aka jefa Annabi Yusuf a Garin Ramat Korazim cikin Galilee a Kasar Isra'ila.
28/04/2024

Rijiyar da aka jefa Annabi Yusuf a Garin Ramat Korazim cikin Galilee a Kasar Isra'ila.

JIYA BA YAU BA...Marigayi Sir. Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto da Marigayi Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi cikin raha  anyi ...
28/04/2024

JIYA BA YAU BA...

Marigayi Sir. Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto da Marigayi Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi cikin raha anyi hoton cikin Shekarar 1955.

Allah Yagafarta Musu.

Daga Shafin Mai Martaba Sarkin Gombe.

Jiya Ba Yau Ba ✨ Fulani Hasiya Mai Babban daki, mahaifiyar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Hajiya Dudu Bayero,...
26/04/2024

Jiya Ba Yau Ba ✨

Fulani Hasiya Mai Babban daki, mahaifiyar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Hajiya Dudu Bayero, kanwar Sarkin Kano Ado da kuma Sarkin Kano na yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero.

Allah ya jikan magabatanmu ya karawa sarki lafiya.

Some Where In Kano…💚
21/04/2024

Some Where In Kano…💚

JIYA BA YAU BA...Wani malami yana rubutun allo a zaurensa anyi hoton cikin shekarar 1952 a garin Zazzau. Allah ya jikan ...
22/03/2024

JIYA BA YAU BA...

Wani malami yana rubutun allo a zaurensa anyi hoton cikin shekarar 1952 a garin Zazzau.

Allah ya jikan Magabatan mu.

Wannan shine Dakin Nana A'ishah R.T.AWanda a sammai 7 da kassai 7 babu wani wajen da ya kai shi daraja.Kabarin Manzon Al...
22/03/2024

Wannan shine Dakin Nana A'ishah R.T.A

Wanda a sammai 7 da kassai 7 babu wani wajen da ya kai shi daraja.

Kabarin Manzon Allah S.A W shine a farko sannan na Sayyidina Abubakar R.T.A a tabangaren dama, sannan na Sayyidina Umar R.T.A

Allah ya bamu Albarkacin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama 🙏

BINDIGAR SARKIN HADEJIA BUHARI (1848)Sarki Buhari shine sarkin Hadejia na Hudu (4) a jerin sarakunan fulani wanda Shehu ...
03/02/2024

BINDIGAR SARKIN HADEJIA BUHARI (1848)

Sarki Buhari shine sarkin Hadejia na Hudu (4) a jerin sarakunan fulani wanda Shehu Usman Bin Fodio ya bawa tutar muslunci.

Sarki Buhari shine sarkin da ya shahara yayi fice a Masarautun kasar Hausa wajan fanin dabarun yaki da jarumta, wanda hatta kai da sauran Masarautan suna shakkar Hadejia wajan yaki.

Wannan Bindiga tana daya daga cikin kayan mulki na gidan sarautar Hadejia, wanda sarakuna Hadejia suke gada. Ana fitowa da ita sau uku a shekara, sallar azumi, Layya, da Maulid wanda mai martaba sarki ne yake amfani da wajan karbar gaisuwa idan ya hau doki, k**ar yadda kuka ga.

JIYA BA YAU BA...Tirkashi! 1950. Saboda muhimmancinta har rufeta da fata akeyi. Koka tashi kaganta agun magabatanka.Alla...
22/01/2024

JIYA BA YAU BA...

Tirkashi! 1950. Saboda muhimmancinta har rufeta da fata akeyi. Koka tashi kaganta agun magabatanka.

Allah ya jikan Magabatan mu.

Allah ya jikan Maje Azare.Sarkin Kano Sir Muhammadu Sunusi dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Abbas dan Sa...
16/01/2024

Allah ya jikan Maje Azare.

Sarkin Kano Sir Muhammadu Sunusi dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi dan Sarkin Kano Mallam Ibrahim Dabo dan Modibbo Mahmud.

Jiya Ba Yau Ba ✨Marigayi Sarkin Kano Alh. (Dr.) Ado Bayero CFR,  Yayin da Yakai Ziyaran Gani Da ido Zuwa Hukumar NASA Sa...
09/01/2024

Jiya Ba Yau Ba ✨

Marigayi Sarkin Kano Alh. (Dr.) Ado Bayero CFR, Yayin da Yakai Ziyaran Gani Da ido Zuwa Hukumar NASA Satellite Dake Garin Kano Anyi Hoton Cikin Shekarar 1965. Shekaru Hamsin da Takwas kenan da s**a Gabata.

Allah Ya Jikan Magabatan Mu.

Galadiman kano Alh Tijjani Hashim dan Turakin kano Hashimu dan Sarkin kano Abbas dan Sarkin kano Abdullahi maje karofi d...
09/01/2024

Galadiman kano Alh Tijjani Hashim dan Turakin kano Hashimu dan Sarkin kano Abbas dan Sarkin kano Abdullahi maje karofi dan Sarkin mal Ibrahim Dabo. Allah ya jaddada musu Rahama

Wannan hoton a ranar 01-01-1954 ne aka dauke shi . Ranar nadin sarautar Alhaji Sir Muhammadu Sanusi dan Sarkin Kano Abdu...
05/01/2024

Wannan hoton a ranar 01-01-1954 ne aka dauke shi . Ranar nadin sarautar Alhaji Sir Muhammadu Sanusi dan Sarkin Kano Abdullahi Bayero, a matsayin Sarkin Kano.
Ga Madakin Kano nan yana mikawa Maimartaba Sarki kayan sarautar Kano. Shi kuma Razdan na tsaye na kallonsau.

Allah ka jikan Burhanuddini na Abbas da dukkan magabatanmu.

28/12/2023

SUNNONIN MANZON ALLAH ﷺ GUDA BIYAR (5) LOKACIN TASHI DAGA BARCI

SUNNA TA FARKO

1- Farawa da Ambaton Allah lokacin tashi daga barci*

Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya tashi daga barci yana farawa da ambaton Allah yana cewa cewa;-

*(ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﺣﻴﺎﻧﺎ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺃﻣﺎﺗﻨﺎ،ﻭﺇﻟﻴﻪ ﺍﻟﻨﺸﻮﺭ*

"ALHAMDU LILLAHIL LAZI AHYANA BA'ADA MAA A MATANA A ILAIKAL NUSHUR"

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

*(Dukkan wanda ya farka cikin dare sai yace:-*

"ﻻ ﺍﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ،ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﺊ ٍﻗﺪﻳﺮ . ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ،ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ،ﻭﻻ ﺍﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ،ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻭﻻ ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ"

Sannan yace;
"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ"
*(Ko yayi addu'a,za'a amsa masa addu'arsa,kuma idan yayi alwala yayi Sallah an karbin Sallarsa)*
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 1154 )

SUNNA TQ BIYU

2- Farawa da yin Aswakin bayan ambaton Allah*.

Manzon Allah ﷺ ya kasance,baya barci face Aswakinsa yana tare da shi,idan ya tashi daga barci sai ya fara da yin Aswaki.

@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻟﻮﺍﺩﻋﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ - ﺭﻗﻢ :‏( 775 ).

SUNNAH TA UKU

3- Goge alamar barci daga idonsa da hannunsa*.

A cikin wani Hadisi mai tsawo daga Ibn Abbas
ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻬُﻤَﺎ
yace;-

"... Sai Manzon Allah ﷺ ya tashi daga barci, sai ya zauna yana goge alamar barci daga fuskarsa"*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ - ﺭﻗﻢ : ‏( 4572 ).

SUNNAH TA HUDU

4- Wanke hannu sau ukku*

Daga Abi Hurairata
ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ,
Lallai Manzon Allah ﷺ yace;-

(Idan ɗayanku ya tashi daga barcinsa, Kada ya sanya hannunsa acikin mazubi ,har sai ya wanke hannunsa sau ukku, domin shi bai san inda hannunsa ya kwana ba)*
️@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ : ‏( 278 ‏)

SUNNAH TA BIYAR

5 - Shaƙa ruwa da facewa sau ukku*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

*(Idan ɗayan ku ya tashi daga barci, to ya shaƙa ruwa ya fyace sau ukku, domin Shaidan yana barci acikin hanncinsa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ : ‏( 238 )

Allah ne mafi sani

Allah Ka bamu ikon koyi da Manzon Allah ﷺ a dukkan rayuwa baki daya. Amin
✍️ Jaruma Hausa.

Allah Ya gafarta masa shi da yayan sa da s**a gaface shi. Yau 24/12/2023 ne shekaru 70 cif da wafatin Sarkin Kano na 10,...
25/12/2023

Allah Ya gafarta masa shi da yayan sa da s**a gaface shi. Yau 24/12/2023 ne shekaru 70 cif da wafatin Sarkin Kano na 10, Sarki Alhaji Abdullahi Bayero.

'Ya'yan Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero su 59 (Maza 26, Mata 33) da ya bari bayan rasuwar sa (24th December, 1953)

Ya'yan Sarki Alhaji maza
1. Sarkin Kano Sir Muhammad Sanusi I
2. Ɗan Iya Aminu
3. Ɗan Darman Isa
4. Ɗanburan Farouk
5. Turaki Maje
6. Galadima Sani
7. Ɗan Buran Bello
8. Barde-Ƙerarriya Kabiru
9. Wakiln Kudu Tijjani
10. Barde Ibrahim Cigari
11. Sarkin Kano Ado
12. Galadima Hamidu
13. Barde Mahmoud
14. Ɗanburan Abubakar
15. Ɗan Iya Yusuf
16. Ɗan Isa Bashari
17. Sarkin Shanu Hamzat
18. Barde Idris
19. Ɗanburan Salihi
20. Baba Ɗalha
21. Ɗan Ruwata Halliru
22. Baba Ja'afaru
23. Baba Auwalu
24. Ɗan Amar Sani
25. Baba Salisu
26. Baba Tijjani

18 & 25 suna raye.

'Ya'yan Sarki Alhaji mata
1. Gwaggo Binta - Magajiya
2. Gwaggo Zinariya
3. Gwaggo Ta Sarki - Gaya
4. Gwaggo Maimuna - Madaki Shehu
5. Gwaggo Iya Iya - Musawa
6. Gwaggo Takau
7. Gwaggo M

GIDAN SARAUTAR BAREBARI DA SARAKUNAN SUBarebari sun fito, ne daga cikin jinsin larabawa, a kasar da ake kira da bagdada ...
22/12/2023

GIDAN SARAUTAR BAREBARI DA SARAKUNAN SU
Barebari sun fito, ne daga cikin jinsin larabawa, a kasar da ake kira da bagdada karkashin shugabancin wani mashahurin malami da ake kira Malam Ibrahim (Sadauki). Shi Malam Ibrahim Sadauki da ne wurin Sarkin Bagdada. Ya yi Hijira daga Kasar Bagdada ya zauna wasu kasashe inda daga karshe ya tafi kasar sudan ya zauna. Ya da de kwarai a sunan inda ya yi suna, kuma ya kasance cikin manyan malamai wadanda ake zuwa daukar karatu wurinsu a wannan kasa ta Sudan. Kuma a dalilin haka ne ya sa s**a shaku da 'yan kasuwa masu safara da almajirai masu zuwa kasar sudan kuma ta dalilin haka ne ma ya sa ya ziyarci kasar Borno ya kuma zauna a can kasar Borno har Shehun Borno ya ba shi auren 'yarsa wadda ita ce ta haifi masa dan da aka sa masa suna Musa shi ne kuma ake kira da Yamusa cikin harshen Barebari.
Malam Ibrahim Sadauki ya rasu a lokacin da Malam Yamusa ya ke da Shekara 18 a duniya. Bayan rasuwar mahaifinsa sai ya bar kasar Borno ya koma kasar Misau tare da mahaifiyarsa da kuma wasu daga cikin almajiransa. Ya kasance daya daga cikin manyan malamai a kasar Misau, yana wannan kasa ta Misau ne ya sami labarin bullowar Shehu Usman ibn Fodiyo. Daga nan ya tashi ya k**a hanya inda ya shigo cikin kasar zazzau ya sauka a zariya. Kuma dama ga shi zariya kasa ce ta malamai don haka ya tsaya a garin na tsawon wani lokaci ya yi karatu a gidan Limamin Kona. A nan s**a hadu da Malam Musa Bamalle, kuma ya hadu da wani mashahurin malami, da ake kira Malam Kilba, inda ya yi karatu a wurinsa har ma malamin ya dauki 'yarsa ya ba Malam Yamusa. Daga nan kuma ya wuce zuwa kasar Gobir, inda ya iske Malam Musa a wurin Mujaddadi Shehu usman, kafin a kaddamar da jihadin Shehu Usman Zuwa kasashen Hausa. Malam Yamusa shi ne ya fara sarautar Madaki a cikin Fulani bayan cire Madaki Makaye da Sarkin Zazzau Malam Musa ya yi bisa Umurnin Shehu dan Fodiyo.
Ya kuma yi Sarkin zazzau Bayan Rasuwar Sarkin zazzau Musa Bamalle. Kuma cikin 'Ya'yansa guda biyu duka sun yi

SARAUTAR SHAMAKI, A FADAR KANO A TAKAICE. Daga Alh Nasiru Wada Khalil. Nasiru Wada Khalil A bisa tsari Shamaki shi ne Ba...
20/12/2023

SARAUTAR SHAMAKI, A FADAR KANO A TAKAICE.

Daga Alh Nasiru Wada Khalil.
Nasiru Wada Khalil

A bisa tsari Shamaki shi ne Babba kuma shugaban duk wani bawan Sarki, Amfara Shamaki kiyasi (1899)Zamanin Sarkin Kano Dabo (Stilwell:30).

Gidan Sarautar Shamaki yana daga bangaren Arewa a cikin gidan Sarki.

Shi ne yake tsayawa a hannun damar Sarki idan ana tafiya a kan doki.

Sannan kuma a fada yana wajen zama a hannun dama kusa da Limamai kuma ko da ya tashi ko baya nan, wani baya zama a wurin k**ar yadda Nasiru Wada Khalil ya kawo a cikin littafinsa na Bayi a Gidan Dabo.

Ayyukan Shamaki suna da yawa matuka wadanda s**a kun shi lura da dukkanin Bayin Sarki da suke fada, tun daga kan Sarakunan kofa masinjoji, Leburori, gadina, masu shara, da sauransu.

Haka kuma shi ne mai kula da dawakan Sarki, da dukkan kayan dokunan.

Shi ne kuma mai nemawa Hakimai izinin ganin Sarki,
Sannan kuma duk matsalar da ta shafi kyauyuka shi ne mai shigar da ita gaban Sarki.

Chiroman Shamaki Kabiri Inuwa Dan Indo (2005) :
Ayyukan Shamaki sun hada da lura da kayan sarauta irin su wukar yanka takalmin gashin jimina tagwayen masu da sauransu a lokacin da sarauta ta fadi kafin a nada sabon Sarki.

HAKIMAN SHAMAKI;

(1)Chiroman Shamaki
(2)Babban Zagi
(3)Sarkin Dogari
(4)Majasiddi
(5)Madakin Shamaki
(6)Mak**an Shamaki
(7)Turakin Shamaki
(8)Jarman Shamaki
(9)Barden Shamaki
(10)Garkuwan Shamaki
(11)Malafa
(12)Sarkin Makera
(13)Barwan Shamaki
(14)Kenkedi
(15)Sarkin Hawa
(16)Sarkin Yakin Shamaki
(17)Jakadan Garko
(18)Sarkin Ruwa
(19)Sarkin Kofa
(20)Sarkin Busa
(21)Mai Dawakai
(22)Galadiman Fanisau
(23)Sarkin Mota
(24)Sarkin Kakaki
(25)San Kira
(26)Sarkin Kitso
(27)Magajin Banga
(28)Magajin Gwanso
(29)Galadiman Shamaki
(30)Sarkin gado
(31)Sarkin Kaji
(32)Shamakin Mai Babban Daki

Daga shafin Labbo Kundumm

MADAKIN ZAZZAU DA KULIYAN ZAZZAU.Yau kenan Mai Girma Madakin Zazzau Malam Malam Munir Jaafaru OFR. mni tare da Mai Girma...
16/12/2023

MADAKIN ZAZZAU DA KULIYAN ZAZZAU.

Yau kenan Mai Girma Madakin Zazzau Malam Malam Munir Jaafaru OFR. mni tare da Mai Girma Kuliyan Zazzau Justice Ishaq Usman Bello tare da Admiral Moh'd Lawal Barau da Captain Aliyu Munir Jaafaru. Allah ya kara lafiya da nisan kwana da Jinkiri mai amfani

PROF ANGO ABDULLAHI  YA CIKA SHEKARA TAMANI DA SHIDA A DUNIYA (86)Yau Ne Mai Girma Magajin Rafin Zazzau Prof Ango Abdull...
13/12/2023

PROF ANGO ABDULLAHI YA CIKA SHEKARA TAMANI DA SHIDA A DUNIYA (86)

Yau Ne Mai Girma Magajin Rafin Zazzau Prof Ango Abdullahi Yake Cika Shakara Tamani Da Shida A Duniya. Muna Adu'an Allah Ya Kara Maka Lafiya Da Gamawa Lafiya Dattijon Arziki Bawan Allah Sauran Maza Jiya Mai Kishin Arewa Da Kasa Bakidaya.

DAGA MASARAUTAR KAZAURE Mai martaba sarkin Kazaure Alh (Dr) Najib Hussaini Adamu ya fitar da zakkan da yakai kimanin nai...
03/12/2023

DAGA MASARAUTAR KAZAURE

Mai martaba sarkin Kazaure Alh (Dr) Najib Hussaini Adamu ya fitar da zakkan da yakai kimanin naira miliyan 60,000,000.

An bada wannan zakkah ne wa mabukata da yawan su yakai mutum 10,000 wadanda addinin Musulunci ya yi umarnin a basu zakkah.

Ran Sarki Ya Dade

Madakin Zazzau Alhaji Munir Jafaru tare da dan'uwansa Muhammadu Aminu. Dukkansu 'ya'yan Sarkin Zazzau Mallam Jafaru dan ...
29/10/2023

Madakin Zazzau Alhaji Munir Jafaru tare da dan'uwansa Muhammadu Aminu.
Dukkansu 'ya'yan Sarkin Zazzau Mallam Jafaru dan Isyaku ne.
Allah ya jikan Muhammadu Aminu Jafaru ya karawa maigirma Madakin Zazzau lafiya.

Photo source: Masarautar Zazzau Jiya da Yau

Address

No. 3 Sambolei Road Emir Drive Kofar Yamma Jama'are
Jama'are

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaruma Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaruma Hausa:

Videos

Share

Nearby media companies


Other News & Media Websites in Jama'are

Show All