19/06/2024
Dr. Abubakar Imam Kenan Shahararren Marubucin Kasar Hausa, Kuma Fitacce A Afirika
Alhaji Dr. Abubakar Imam shahararren marubucin kasar hausa kenan marubucin littafin 'RUWAN BAGAJA' da 'MAGANA JARI CE'. Wanda ya taimaka wajen samar da jaridar Hausa ta farko a duniya mai suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo' a shekarar 1939.
Shi ne Editan farko na wannan jaridar. Ya bada kyakkyawar gudummawa wajen yada al'adun hausawa tare da yada shi kansa yaren ta hanyar yin rubuce rubuce masu yawa.
Fata Allah ya yi masa rahama.
Daga Nura Sagir