21/10/2024
Wasu sojojin Isra'ila sun ce ba za su ci gaba da yaki ba
Akalla sojojin Isra'ila 130 s**a rubuta wasika wa gwamnatin kasar cewar ba za su ci gaba da yaki ba, muddin hukumomin kasar ba za su dauki matakin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tun daga ranar 7 ga watan Oktobar bara ba. A wata wasikar da s**a rubuta ta ranar 9 ga wannan watan, sojojin da wadanda aka kira domin yiwa kasar yaki sun ce sun fahimci gwamnatin kasar ba ta son kawo karshen yakin domin gudanar da zabe. Daya daga cikin sojojin ya ce tun da babu wani ci gaba wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, saboda haka babu dalilin ci gaba da wannan yakin da kasar ke yi. Sojan ya ce wannan wani matsayi ne ya dauka na bijirewa gwamnatin kasarsa saboda yadda ta kai matakin karshe na yaudara. Sojan ya ce da da gaske ake yi wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, da tintini anyi nasara, amma ana tsawaita yakin ne domin kin gudanar da zabe, matakin da zai bai wa (firaminista) damar ci gaba da zama a karagar mulki. Rahotanni sun ce wasikar ta harzuka gwamnati wadda ta dakatar da wasu daga cikin sojojin.
📷 Reuters