Jama'are Emirate Council

Jama'are Emirate Council Updates and important message from jama'are Emirate council.

Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un.😭😭😭Cikin jimami da kaduwa muke sanar da wannan babban rashi ga masarauta, Allah yay...
15/05/2024

Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un.😭😭😭

Cikin jimami da kaduwa muke sanar da wannan babban rashi ga masarauta, Allah yayiwa Baba Kilishin Jama'are Alhaji Abubakar Adamu Buba rasuwa daya daga cikin dattijai makusanta sarki das**a rage a masarautar jama'are shine mahaifi ga Alh. Sabo Buba (Sarkin Tsaftar Jama'are) da kuma Mallam Sa'idu Buba (Cashier Jama'are LGAs)

muna addu'a Allah yajikansa da rahama ya gafarta masa yasa aljanna makoma gareshi yabawa mai martaba sarki hakurin wannan rashi tare da iyalan mamacin Amin

Za'a sanar da lokacin janaza da zarar gawarsa ta iso daga asibitin FMC Azare Allahummah gafirhum warhamhum Baba Kilishin Jama'are.

Mai-girma wakilin wajen jama’are, allah yakara lafiya
02/05/2024

Mai-girma wakilin wajen jama’are, allah yakara lafiya

28–04–2024A yau ne mai-martaba sarkin jama’are, Alh. Nuhu Ahmad wabi mni,  ya karbi bakuncin Hon. Bala rabilu kashuri ( ...
28/04/2024

28–04–2024

A yau ne mai-martaba sarkin jama’are, Alh. Nuhu Ahmad wabi mni, ya karbi bakuncin Hon. Bala rabilu kashuri ( Dan majalisa tarayya mai wakiltar, jama’are da itas gadau) a fadar sa dake nan cikin garin Jama’are.

Allah yakarawa sarki lafiya. Ameen🙏🏼

Daga fadar mai- martaba sarkin Kano , kenan Alh. Aminu Ado bayaro, a yayin mai-marbata sarkin jama’are, Alh. Nuhu Ahmad ...
26/04/2024

Daga fadar mai- martaba sarkin Kano , kenan Alh. Aminu Ado bayaro, a yayin mai-marbata sarkin jama’are, Alh. Nuhu Ahmad wabi mni, ya halarci taron Daurin auren Dan gidan mai-martaba sarkin kano, Allahu yabasu zaman lafiya. Ameen🙏🏼

26/04/2024

Daga masarautar kano, Allah ya karawa sarki lafiya🙏🏼

Allah ya kara lafiya, mai girma cikasoron jama’are,🙏🏼
26/04/2024

Allah ya kara lafiya, mai girma cikasoron jama’are,🙏🏼

Tawagar mai girma Bunun-jama’are, Allah ya dafa maka🙏🏼
26/04/2024

Tawagar mai girma Bunun-jama’are, Allah ya dafa maka🙏🏼

Dan-makwayon jama’are, ubangiji Allah yakara daukaka🙏🏼🙏🏼
26/04/2024

Dan-makwayon jama’are, ubangiji Allah yakara daukaka🙏🏼🙏🏼

Mai girma- Dan iyan jama’are, Allah yakara girma
22/04/2024

Mai girma- Dan iyan jama’are, Allah yakara girma

Maidalan jama’are, Allah yakara lafiya
22/04/2024

Maidalan jama’are, Allah yakara lafiya

Kaigaman jama’are, Allah yakara Girma🙏🏼
18/04/2024

Kaigaman jama’are, Allah yakara Girma🙏🏼

Tawagar mai-girma Uban Doman jama’are, Allah yakara daukaka🙏🏼
18/04/2024

Tawagar mai-girma Uban Doman jama’are, Allah yakara daukaka🙏🏼

Gado da masun Jama’are, kenan Allah yakara Daukaka🙏🏼
16/04/2024

Gado da masun Jama’are, kenan Allah yakara Daukaka🙏🏼

Galadiman Jama’are, Allah yakara Daukaka🙏🏼
16/04/2024

Galadiman Jama’are, Allah yakara Daukaka🙏🏼

Mai girma waziri, Allah yakara lafiya🙏🏼
16/04/2024

Mai girma waziri, Allah yakara lafiya🙏🏼

Mai-girma Iyan jama’are (Hakimin kasar Hanafari)  Allah yakara lafiya
15/04/2024

Mai-girma Iyan jama’are (Hakimin kasar Hanafari)
Allah yakara lafiya

Mai-girma wambam jama’are (Hakimin kasar jama’are) Allah yakara lafiya😘🎉🎉
15/04/2024

Mai-girma wambam jama’are (Hakimin kasar jama’are)
Allah yakara lafiya😘🎉🎉

Mai-girma Hakimin Galdimari,, ( san-turakin jama’are) Allah yakara lafiya da nisan kwana🙏🏼
14/04/2024

Mai-girma Hakimin Galdimari,, ( san-turakin jama’are) Allah yakara lafiya da nisan kwana🙏🏼

Sakon Barka Da Sallah !!Mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi,Mni yayin hawan bikin Sallah Babba na wannan sh...
10/04/2024

Sakon Barka Da Sallah !!

Mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi,Mni yayin hawan bikin Sallah Babba na wannan shekaran 1445AH/2024

Yayi jawabai da kuma yiwa illahirin jama'ar masarautar Jama'are, barka da sallah, da fatan allah ya maimaita mana. Ameen

Allah Ya karawa Mai martaba sarki lfy da Nisan Kwana!

Mai Girma Hakimin Gundumar Kasar Galdimari, kuma Santurakin Jama'are.Alhaji Adamu Ahmad Wabi, Ya jagoranci Kaddamar da R...
15/03/2024

Mai Girma Hakimin Gundumar Kasar Galdimari, kuma Santurakin Jama'are.

Alhaji Adamu Ahmad Wabi, Ya jagoranci Kaddamar da Rabon Zakka na Gundumar kasar Galdimari A wannan Rana mai albarka, kaddamar da rabon zakkar na wannan lokaci ya samu Halartar Manyan Malaman Addini musulunci da kuma wasu daga cikin Jami'an Hukumar Zakka ta jahar Bauchi.

Yayin Gabatar da Rabon Zakka an gabatar da Adadin yawan kayan da aka Tara da Kuma yawan Al'ummar da zasu amfana da Ita.

A jawabinsa mai girma Hakimin Kasar Galdimari Yaja hankalin Mawada ta da su Zama mutane masu fitar da Hakkin Allah domin samun Rabautuwa musamman a cikin wannan tawa Mai alfarma na Ramadana.

Muna addu'ar ya ubangiji Allah madaukakin Sarki ya karbi dukkan Ibadun mu, Yasa agama da duniya lafiya.

Daga Gundumar Hakimin Kasar Hanafari, Alhaji Ahmad Wabi kuma [ Iyan Jama'are].Uban kasa mai martaba sarkin Jama'are HRH ...
05/03/2024

Daga Gundumar Hakimin Kasar Hanafari, Alhaji Ahmad Wabi kuma [ Iyan Jama'are].

Uban kasa mai martaba sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni. Ya halarci Taron bada Zakka A gundumar kasar Hanafari, dake Karamar hukumar Jama'are.

Allah yaja zamanin sarkin.
Allah ya kara bama alumar musulmi ikon taimakon addinin musulunci .

Ziyara ta biyu Daga Fadar Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Gumel.Daga Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel HRH. Alhaji ( Dr ) Ahme...
21/12/2023

Ziyara ta biyu Daga Fadar Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Gumel.

Daga Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel HRH. Alhaji ( Dr ) Ahmed Muhammed Sani II, Con. Inda Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni Yake Cigaba Da Gabatar Da Ziyarar Sada Zumunci Domin Kara Jaddada Alakar Dake Tsakanin Masarautar Jama'are Da Sauran Masarautun Mu Masu Albarka.

Muna Addu'ar Allah Yaja Zamanin Masu Martaba Sarakuna Iyayen Kasa Masu Albarka.

Ameen ya Allah.

Ziyarar Sada Zumunci A Fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia.Daga Garin Hadejia Na Jahar Jigawa, Inda Uban Kasa Mai Martaba S...
21/12/2023

Ziyarar Sada Zumunci A Fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia.

Daga Garin Hadejia Na Jahar Jigawa, Inda Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni Yaje Domin Gabatar Da Ziyarar Sada Zumunci Tsakanin Masarautar Jama'are Da Ta Hadejia A Wannan Rana Mai Albarka, Alakar da aka samo tun zamanin Iyaye da Kakanu. Muna fata allah ya kara hada kan masarautun mu , allah kuma ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan mu da kasa baki daya. Ameen

MASHA ALLAH... ALLAH YA TAYASHI RIKO.!!HRH. Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni yayin da zuri'ar gidan marigayi Dan Iyan jama'ar...
27/08/2023

MASHA ALLAH... ALLAH YA TAYASHI RIKO.!!

HRH. Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni yayin da zuri'ar gidan marigayi Dan Iyan jama'are Alhaji Ahmadu Malle s**a zo domin gabatar da godiyar sarautar Sabon Barden Gabas Malam Ahmad Atiku Malle Na masarautar jama'are, wanda ya samu sahalewar uban kasa mai martaba sarkin jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni a kwanakin baya.

Muna addu'ar ya Allah ya taya shi riko ameen ya rabbi.

SMASH _photography, jama'areSMASH _photography, jama'are

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM RANA MAFI ALKHAIRIRana mafi alkhairi awajen dukkan Mumini, ita ce ranar mutuwarsa.... Domin ...
20/08/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

RANA MAFI ALKHAIRI

Rana mafi alkhairi awajen dukkan Mumini, ita ce ranar mutuwarsa.... Domin Misalinsa shine kamar 'mutumin da yake cikin Kurkuku, shima babu abinda yafi Qauna kamar ranar da zai samu 'Yancinsa.

Ita duniya kurkukun Mumini ce, kuma Aljannar kafiri. Mumini yana shan fama da yaki da shaitan da kuma zuciya, sannan ga bala'o'I da jarrabawa kala-kala wadanda dasu ne Allah yake kankare zunubansa ya daukaka darajarsa.

Don haka ranar mutuwar mumini ta zamto ranar samun 'yanci gareshi da gafara da rahamar Ubangijinsa, kuma ranar tabbatuwar dukkan abinda yake buri na alkhairi awajen Ubangijinsa.

Rana ce wacce Mumini zai ga Karamci da Mutunci da Girmamawa irin ta Ubangiji madaukakin Sarki. Wanda ba ya manta alkhairi, kuma Shi keda abun yin sakayya.

Rana ce wacce Mala'ikun rahama zasu zo karbar ruhinsa cikin aminci da girmamawa da tausasawa, kuma acikin mafi kyawun Siffa mai kwantar da hankali mai Qamshi. Zasu kwantar masa da hankalinsa da kyawawan kalmomi masu dadi.

Za'a kaishi cikin Qabarinsa wanda Allah ya yalwata masa shi... ya Qawata masa shi, ya ni'imta masa shi fiye da duk wani gida ko Masauki irin na duniya.

Kafin karbar ran Mumini da kuma bayan shigarsa Qabari, Allah zai sa Mala'ikunsa su nuna ma wannan muminin gidansa na Aljannah, tare da Matayensa na Hurul-Ein duk sunci ado domin Maraba da zuwansa.

Rana ce wacce Mumini zai hadu da cikar dukkan burinsa, wato haduwarsa da Babban abin Qaunarsa, SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Ya Allah ka kyautata tunaninmu, ka tsare mana Imaninmu da Qaunar da muke wa Annabinka, kasa mu rayu dashi, mu mutu dashi, kuma mu tashi tare dashi aranar Mahashar.

Dafatan Zamu Kasance Cikin Koshin Lafiya Tareda Daukacin Iyalan Gidajen mu, Barka Da Hutun Karshen Mako.

Cc: SMASH SMASH _photography, jama'areSMASH _photography, jama'are jama'are

Daga Fadar Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mniYa gabatar da zaman majallisar masarautar jama'are...
15/08/2023

Daga Fadar Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni

Ya gabatar da zaman majallisar masarautar jama'are a wannan Rana mai albarka kamar yadda aka saba gudanarwa domin karban baki daga ciki da wajen masarautar jama'are.

Kadan daga cikin bakin da s**a ziyarci fadar uban kasa mai martaba sarkin jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni sun hada Da ---

Shugaban Rundunar Jami'an Tsaro Na Sojojin Kasa mai kula da Shiyar Katagum Zone.

Shuwagabannin Gudanarwa Na Makarantar Abdulkadir Ahmad Memorial College Of Health Science And Technology Jama'are.

Shuwagabannin Hukumar Lafiya Matakin Farko da kuma Wasu daga cikin Kungiyar Unicef reshen jahar bauchi.

Duk ziyara nasu nada nasa bane domin gabatar da kansu da kuma neman tabarraki a wajen uban kasa mai martaba sarkin jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni. Ran Sarki Ya Dade.


Photograph from. SMASH SMASH _photography, jama'areSMASH _photography, jama'are jama'are

Sakon Barka Da Sallah !!Mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi,Mni yayin hawan bikin Sallah Babba na wannan sh...
28/06/2023

Sakon Barka Da Sallah !!

Mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi,Mni yayin hawan bikin Sallah Babba na wannan shekaran 1444AH/2023.

Yayi jawabai da kuma yiwa illahirin jama'ar masarautar Jama'are, barka da sallah, da fatan allah ya maimaita mana. Ameen

Allah Ya karawa Mai martaba sarki lfy da Nisan Kwana!

Alhamdulillah! Alhamdulillah!!Alhamdulillah!!!~20-06-2023~Ayau ne, Allah (s.w.a) ya azurta masarautar Jama'are da samun ...
20/06/2023

Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!

~20-06-2023~

Ayau ne, Allah (s.w.a) ya azurta masarautar Jama'are da samun sabo secretary Alh. BALA HAFIZU, bayan kawo da ritaya da tsohon secretary yayi, Alh. ABUBAKAR WALI a satin da ya gabata, muna rokon Allah yasa wannan canji yazama alheri ga wannan masarautar tamu mai dogon tarihi da albarka.

Allah yaja zamanin sarkin.

Ameen.
Mai- photo SMASH _photography, jama'areSMASH _photography, jama'are

May Almighty Allah Bless you and your family with a restful mind, useful soul, peaceful home, commendable effort, accept...
17/06/2023

May Almighty Allah Bless you and your family with a restful mind, useful soul, peaceful home, commendable effort, acceptable worship, and a successful end.

May He beautify your tongue with truth, heart with sincerity, and count you among the dwellers of Jannatul Firdaus, and provide final solution to insecurity in Nigeria.

Ameen.

29/05/2023A yau ne mai martaba sarkin jama'are, Alh. Nuhu Ahmad wabi, mni. Ya halarci bikin rantsar da  governor jihar B...
29/05/2023

29/05/2023

A yau ne mai martaba sarkin jama'are, Alh. Nuhu Ahmad wabi, mni. Ya halarci bikin rantsar da governor jihar Bauchi , His excellency. Sen. Bala Abdulkadir Muhammad (kauran Bauchi, jagaban katagum) Wanda aka gudanar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, mai martaba sarki yana taya shi murna da kuma addu'ar Allah yakara riko da hannunsa ,akan ayyukan alheri da yafara, allah kuma yakara bashi ikon karawasa da alheri.

Allah yabamu zaman lafiya a Bauchi da kasa baki daya.

Ameen...

SMASH _photography, jama'areSMASH _photography, jama'are

Address

Emirs Palace
Jama'are

Telephone

+2348114942708

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jama'are Emirate Council posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other News & Media Websites in Jama'are

Show All