08/12/2022
BAZAN GUDU IN BAR AL'UMMATABA IN JI SARDAUNAN SOKOTO.
Ranar juma'ar da za'a kashe su firimiyan jahar Arewa Sardaunan Sokoto, firimiyan jahar yamma Akintola yazo kaduna wurin Sardauna. Lokacin da Akintolan yazo Sardauna na Masallacin Juma'a sai yaba daya daga cikin ministocinshi Michele Audu Buba umurnin cewar yaje ya tari Akintola.
Bayan Sardauna ya idar da Sallah yazo sun yi wata ganawa ta sirri da Akintola, da Birgediya Samuel Ademulegun. Duk da yake marubuta sun rabu biyu akan abun da s**a tattauna.
Wasu sun ce sun tattaunane akan rikicin jahar yamma. In da wai Akintolan ya roki Sardauna da ya shiga maganan. Kamar yadda wayannan s**ace an tattauna akan yadda kaddamar da wani samame na soja a jahar yamma wato operation Wiety zai kasance.
Amma mafi rinjayen magana shi ne sun tattauna akan rade-raden juyin mulkin da akeyi. Kamar yadda rahotanni s**a tabbatar Akintolan ya ba Sardauna shawarar cewa tun da yanada kyaukyawar alaka da shugaban kasar Nijar mai zai hana ba zasu tafi Nijar ba su samu mafaka? Akintolan ya ce bayan sun yi juyin mulkin sai mu nemi taimakon kasar Burtaniya ta taimakemu da sojoji a kori yan juyin mulkin.
Nan take Sardauna yai fatali da wannan shawarar. Ya ce babu in da za shi bai ga dalilin da zai sa tsoron mutuwa tasa ya gudu ya bar al'ummarsaba. Kana ganin kona rayu nan gaba idan magana ta taso inada bakin maganane za'a gorantamun ace na taba guduwa nabar al'ummata.
Akintola yai juyin duniyannan amma Sardauna yaki yadda. A karshema ya ce ma Akintola ka koma gida ka jira kaga abun da Allah zai yi, ni Musulmi ne nasan ba zan taba gudun ma ajalinaba.
Wasu sun ce lokacin da Akintola zai hau jirgi ya juyo ya cema Sardauna wallahi kashemu zasu yi. Yau kuma zasu kashe mu.
Kamar yadda Marigayi Hassan Hadejia ya ce akan hanyarsu ta dawowa daga rakiyan da s**aima Akintola, sun gamu da Nzeogwu dai, dai, Kotoko barrack. Daya hangi ayarin Sardauna ya kame yai gaisuwa. Sai Sardauna ya cema Hassan Hadejia yauwa sai da naga Sarkin yaki na tuna.