Arewa Teach

Arewa Teach ArewaTeach
(7)

25/11/2023

Dawo da WhatsApp Da akai Banned ko Restricted

25/11/2023

WhatsApp

Domin Sauraron Gidajen Radiyon BBCHAUSA,  VOA Hausa, DW Hausa, RIF HAUSA,  da duk wasu gidajen Radiyon da suke Arewacin ...
04/05/2023

Domin Sauraron Gidajen Radiyon BBCHAUSA, VOA Hausa, DW Hausa, RIF HAUSA, da duk wasu gidajen Radiyon da suke Arewacin Nigeria, [ Kano, Bauchi, Kaduna, Adamawa, Sokoto, Kaduna Abuja, katsina, Yobe, Jos, Da sauransu..] Maza sauqe app dinmu na Hausa Radio akan wayoyinku

Masha Allah💓🤲💓
22/03/2023

Masha Allah💓🤲💓

16/03/2023

Mu Kiyaye Abubuwan da zamu daura a Internet... Musamman abun da yake Sirri Garemu! Misali ( Date of Birth, Sa Hoton ATM ko wani Numbrs da suke da alaqa da Bankinmu, ko Adress, da kuma duk wani Abu da zai'iya zama Personal Information Namu..) Domin Kaucewa Hacker...
Allah ya Karemu ( Amen )

Saurari Radio Hausa kai tsaye. Hausa Radio Live.  Sabuwar manhajja domin sauraron tashoshin rediyo Hausa. Radio Hausa Li...
26/02/2023

Saurari Radio Hausa kai tsaye. Hausa Radio Live.

Sabuwar manhajja domin sauraron tashoshin rediyo Hausa. Radio Hausa Live Streaming app manhajja ce domin k**a tashoshin gidajen rediyo na Hausa.

Aciki zaku samu tashoshin Radio k**ar su:-
- BBC Hausa ( shirin safe, shirin hantsi, shirin rana, shirin yamma shirin ra'ayi riga kowa da irin tasa).
- Gidan rediyon Deutsche welle (DW Radio). Shima DW Hausa zaku iya sauraron shirin safe, shirin rana da kuma shirin yamma.
- Gidan rediyon Dala FM dake birnin Kanon Dabo.
- Gidan rediyon Wazobia 99.5 FM
- Freedom Radio 99.5 Kano dake arewacin Najeriya
- Radio NigeriaINFO 95.1 FM Abuja
- Hausa Radio Net
- ZongoLink Radio
- Live stations ( BBC, VOA, RFi, DW direct)
- VOA (shirin safe, hantsi, rana da dare)
- Rediyo Faransa (RFi) shirin safe da yamma

FAKE ALERTKa karanta har ƙarshe zai maka amfaniNa daɗe ina neman tayaya akeyin transfer ta ƙarya zuwa Bank Account ɗin m...
18/02/2023

FAKE ALERT

Ka karanta har ƙarshe zai maka amfani

Na daɗe ina neman tayaya akeyin transfer ta ƙarya zuwa Bank Account ɗin mutum wato "fake alert" k**ar yadda dai madamfara keyi ayayin da s**a sayi kayan mutum s**a masa transfer bayan wasu awanni da anduba account balance sai aga babu kuɗi...

Wato transfer ta ƙarya (fake alert) ashe abune mai sauƙin gaske sai dai kawai sirrintawa da akeyi saboda kar kowa ya iya yawan ɓarayi su ƙaru, ko kuma ɓarayin basuso agano tayaya suke wannan aika aika?

Ya zama dole ni nafada maku musamman a irin wannan lokaci da kowani cinikayya ya kusan zama harkar transfer, amma kai da zanfaɗawa na faɗa maka ne domin ka kare kanka daga faɗawa hannun waƴannan madamfara, adan haka kaji tsoron Allah kaima karda kace zaka gwada (wannan yasa ba'a faɗi saboda kar yawan azzalumai su ƙaru).

Wato shi "fake alert" transfer ta ƙarya zuwa asusun ajjiyar kuɗin mutum ta banki ana yinsa ne akan wani Application mai suna "PRO BANK" shima k**ar suffar Mobile Banking yake dashi musamman masu amfani da Mobile Bank App sunsan yadda procedure ɗin amfani da App ɗin yake.

Shi wannan PRO BANK App ɗin akansa ake tura transfer ta kuɗi ko ince alert zuwa kowani Bank Account amma bayan anturawa mutum bayan wasu awanni kuɗin zasu ɓace, sannan alert ɗin na da wasu ɗabi'u k**ar haka:

1. Shi wannan fake alert ɗin sau ɗaya (1 time) kawai ake iyayi a rana, idan kayiwa mutum ɗaya shikinan sai kuma after 24hrs kafin ya kumayi.

Dalili kuwa shine; dama anyi sane domin pretend/joke/ irin kayiwa mutum transfer ta ƙarya cikin wasa a tunaninsa gaskiya ne amma sai dai kawai wasa ne, k**ar irin su April fool dai haka... To saboda kar amaida abin ya wuce wannan manufar shiyasa aka tsara App ɗin da sau ɗaya kawai mutum zai iya transfer ɗin a rana.

2. Idan akai maku transfer; idan kuka duba ALERT message ɗinku na transaction ɗin to a wajan "DES" za kuga ansa "PRO" ko "PRO bank", shi wannan "Des" address ne na inda aka turo kuɗi, k**ar yadda idan kaje wajan mai POS zakaga yasa sunan POS ɗin, idan ATM ne ya rubuta sunan ATM ɗin, haka idan Mobile Banking ne ya rubuta, to haka shima za kuga an rubuta "pro bank" a wajan, to da zaran kaga "PRO BANK" a wajan ka tabbata fake translation ne.

3. Shi wannan credit translation ɗin na "fake alert" kawai ta SMS yake zuwa amma baya zuwa ta Gmail account da sauran dukkan hanyoyin da kuke receiving transaction NOTIFICATION messages na Bank naku, sannan da zaran alert ɗin ya shigo zakuga balance naku na baya da kuma kuɗin da aka turo da kuma total balance naku (to anan wajan ne za kuga k**ar alert din gaske domin komai da kuke gani ayayinda aka turo maku da kuɗi bai canza ba).

HANYOYIN KARIYA

Duk lokacin da aka turo maku da kuɗi a banki (Credit alert transaction);

1. Kuyi checking account balance naku direct, kusa code da ake duba balance na kuɗi zai baku normal balance na kuɗinki, karkuyi believing da SMS na wannan transaction ɗin.

2. Kuyi ƙoƙari ku sami Mobile Banking Application na bankin da kuke amfani dashi ku ɗaura akan Smart phone naku kuɗinga amfani dashi musamman masu business, shi wannan App ɗin kai tsaye zakaje profile naka ka duba Total balance na kuɗinka, sannan ka duba transaction statement na kuɗin dukda aka turo maka ( fake alert baya zuwa kai tsaye zuwa asusun ajiyar kuɗinka na banki, sannan shi wannan App ɗin zai nuna maka ne current status naka babu ragi babu ƙari), to duk sanda wani ya turo maka da kuɗi ka duba Mobile Banking App ɗinka a take a wajan zai nuna maka gaskiyar lamari kuɗinka ya shiga ko bai shiga ba.

3. Akwai LEO Banking system shi wannan amma na Whats'App ne sannan UBA na sani suna dashi bansan ko wani banki suma na dashi ba, shi k**ar yadda kake chatting da contacts naka akan Whats'App shima haka zaku dunga chatting dashi amma computer ne, zaka duba balance, zaka tura kuɗi, sannan zaka duba statement, to shima baya ƙarya (fake alert baya hawa kansa) da zaran anturo maka da kuɗi to ka duba balance naka ta wajan zai baka real balance naka.

Phone number ne da UBA s**ayi generating wanda zakai saving akan contact naka ya fito maka ta Whats'App k**ar dai sauran numbers naka to amma computer ne number din.

4. Hanya ta ƙarshe, kafin mutum ya maka transaction idan yana kusa dakai ka tambaye sa ta ina zai turo maka da kuɗin? Ya nuna maka App ɗin da zaran kaga PRO BANK application ne to karka yarda fake alert za'a maka, sannan da zaran alert ya shiga kaga message ka duba wajan "Des" k**ar yadda na faɗa a baya da kaga pro ko pro bank a wajan to fake alert ne.

Ko wani Banki nada Mobile Banking Application nasu, adan haka ku kula sosai...

Allah ya daɗa karemu daga sharrin azzalumai.

Cc- Abu Bakr

CBN - Tabbas CBN ya umarci bankuna suci gaba da karɓan tsaffin kuɗi 500k.Yadda abun yake shine :- wajibi ne duk wanda za...
18/02/2023

CBN - Tabbas CBN ya umarci bankuna suci gaba da karɓan tsaffin kuɗi 500k.

Yadda abun yake shine :- wajibi ne duk wanda zai kai ƙudinsa banki sai yayi Register a shafin CBN dake internet, kuma ya zama na kudin da zai shigar basu haura 500k ba.

Abubuwan da ake buƙata sune :-

Bank Account
Email address
BVN
NIN number

Zaka iya ziyartan shafin CBN da kanka ka cike, amma zai fi kyau kaje CAFE a cike maka, zasu tura maka sako ta Email dinka kayi PRINTING ka tafi dashi bankin ka.

Amma sai dai wani hanzari ba gudu ba, shine idan ka saka kuɗi sau ɗaya to har abada baza ka iya sake saka wa ba, misali kasa a Gt bank, to baka isa ka sake sawa a Zenith ba ko Uba Bank ko wani banki.

Sannan baza ka iya zuwa da Account din wani ba sai dai kuje tare da shi, sabo da dole sai yayi THUMBPRINT na ƴan yatsun hannun sa.

Don Allah kuyi sharing Sabo da jama'a su amfana, wallahi Nina shigar da nawa yau, amma babu dama na shigarma wasu dole Limit dina ya kare.

Copy: Faisal Abbas NG

YAKIN NEMAN KARFIN FADA AJI A DUNIYAR 'ARTIFICIAL INTELLIGENCE' YA FARA.Source and Author:  Kamfanin Google sun shigo du...
10/02/2023

YAKIN NEMAN KARFIN FADA AJI A DUNIYAR 'ARTIFICIAL INTELLIGENCE' YA FARA.

Source and Author:

Kamfanin Google sun shigo duniyar 'Artificial Intelligence', yayin da a karon farko s**a sanar da 'AI' din su na farko mai suna 'DREAMIX'. A maimakon ChatGPT da yake baka amsar kusan duk abin abinda ka tambaye sa, Dell-E kuma yake baka hoton duk abinda zaka hakaito a kwakwalwarka ka.

Toh bari kuji shi kuma wannan sabon 'AI' din na Google me yake yi:

Idan ka saka masa hoton kowane abu, to zai mayar da wannan hoton daga hoto zuwa video. Bafa video na hoto ba, A'a video zai yi maka na gaske. Ina nufin ka dauki hoton Sunusi Danjuma Ali ka saka masa, to idan ka fadi me kake so ya maka da hoton zai dawo maka dashi a video.

Misali: A maimakon video da oga sunusi yake yi yanzu, sai ya siyi babbar waya da babbar camera, sannan ya zauna yayi editing na kwana biyu. Toh zai iya amfani da hoton shi kawai da ya dauka a daki mai kyau, yayi generating din duk kalar video din da yake so ba tare da yayi aikin sisi ba.

Sannan kuma wani abun gaba da mamaki da 'Dreamix' na kamfanin Google yake yi shine: Zaka iya rubuta masa gabaki daya script na labarin film, da kanshi zai maka generating film din da characters, tare da duk wani abun da kake tunanin akeyi a film. Kan Bala'i..🤦

Banda 'Dreamix' akwai kuma 'Bard AI' shima duk Google suna kan yin aikin fitar dashi.

YADDA AI YAKE AIKI SHINE

Misali: Idan ina son na kirkiri AI wanda zai dinga tuqa mota, to ina da buqatar lallai sai na samu information da yawa game da yadda dan adam yake tuqa mota.

1. Ya mutane suke cin birki.
2. Ya ake yin kwana.
3. Me mutane s**a fi haduwa dashi akan hanya idan suna tuqi.
4. Ta yaya mutane suke fahimtar abinda ya k**ata su ciwa birki.
5. Ya mutane suke parking.
6. Me yake jawo hadari, kuma ya za'a kauce masa.
7. Ina ne hanya, ina ne ba hanya ba.
8. Taswira 'Map' na inda kake dss.

To bayan na samu biliyoyin wadannan informations din sai na dora su akan kwakwalwar software ta motar, daga nan idan ka kunna motar zata fara fahimtar da tazo guri gaza kwana zata yi, idan taga kaza birki zatayi dss.

To anan kuma kada fa mu manta Google yafi ko ina information a duniya, sune suke da fasahar Android, Gmail nasu ne, YouTube shima haka, Chrome ma haka. Kai kusan duk abinda muka fi amfani dasu a intanet mallakin Google ne.

Kamfanin Google yana da information da yawa game da mutane, Code din da aka rubuta program na Google ya kai layi Biliyan 2, mai bin sa MacOS ne da layi Miliyan 82, sai Facebook mai layi miliyan 62.

Hakanan Kamfanin Google da Apple da Facebook tare da Amazon su ne s**a fi kowa yawan kudi cash a ajiye. Kai gwamnatin America ma tana rantar kudi a hannun Google. Sai dai kuma Masana suna cewa kamfanin OpenAI ya fitar da kaso 10% ne cikin darin abinda ChatGPT zai iya yi. Dama suna sane da Google zasu iya gasa dasu.

Chabdijan Akwai Rigima, Menene Ra'ayin Ku..😎😎😎😎

GB User 🤪🚶‍♂️🚶‍♂️🚶‍♂️
21/01/2023

GB User 🤪🚶‍♂️🚶‍♂️🚶‍♂️

19/01/2023
Saurari Radio Hausa kai tsaye. Hausa Radio Live.  Sabuwar manhajja domin sauraron tashoshin rediyo Hausa. Radio Hausa Li...
16/01/2023

Saurari Radio Hausa kai tsaye. Hausa Radio Live.

Sabuwar manhajja domin sauraron tashoshin rediyo Hausa. Radio Hausa Live Streaming app manhajja ce domin k**a tashoshin gidajen rediyo na Hausa.

Aciki zaku samu tashoshin Radio k**ar su:-
- BBC Hausa ( shirin safe, shirin hantsi, shirin rana, shirin yamma shirin ra'ayi riga kowa da irin tasa).
- Gidan rediyon Deutsche welle (DW Radio). Shima DW Hausa zaku iya sauraron shirin safe, shirin rana da kuma shirin yamma.
- Gidan rediyon Dala FM dake birnin Kanon Dabo.
- Gidan rediyon Wazobia 99.5 FM
- Freedom Radio 99.5 Kano dake arewacin Najeriya
- Radio NigeriaINFO 95.1 FM Abuja
- Hausa Radio Net
- ZongoLink Radio
- Live stations ( BBC, VOA, RFi, DW direct)
- VOA (shirin safe, hantsi, rana da dare)
- Rediyo Faransa (RFi) shirin safe da yamma

30/12/2022

ABUBUWA MASU CIN RAI A WHATSAPP 😨

Matakan da za ka bi don tsare wayarka daga shiga shafukan da suke wallafa contents na 'batsa' da 'badala' a yanar gizo:1...
27/12/2022

Matakan da za ka bi don tsare wayarka daga shiga shafukan da suke wallafa contents na 'batsa' da 'badala' a yanar gizo:

1. Ka shiga cikin 'SETTING' na wayarka.
2. Ka shiga NETWORK & INTERNET, ko kuma ka yi searching 'PRIVATE DNS'
3. Ka shiga cikin 'PRIVATE DNS' za su nuna 'option' guda 3 a 'modal box':
• Off
• Automatic
• Private DNS provider hostname
Sai ka shiga na ƙarshen 'Private DNS Provider'
4. Za a ba ka wani 'field' a ƙasa, an rubuta: "enter hostname of DNS Provider"

Sai ka rubuta:
adult-filter-dns.cleanbrowsing.org

5. Sai ka yi 'SAVE"

Idan ka bi waɗannan matakan, zai kare ka daga shiga shafukan badala a yanar gizo, ko ka yi 'searching' ko 'link' ne ka yi 'click' a kai, ba zai buɗe ma ba.


(Numbobi 10 tare da qarin Umarni 6)Sune jigo wajen gudanar da kowanne kalar Lissafi a Duniya!Gasu k**ar haka!1 ,2,3,4,5,...
15/12/2022

(Numbobi 10 tare da qarin Umarni 6)

Sune jigo wajen gudanar da kowanne kalar Lissafi a Duniya!

Gasu k**ar haka!
1 ,2,3,4,5,6,7,8 9,0
saikuma
+, ×, ÷, =, -, .

Ko kunsan wanne suna ake qiransu dashi a duniyar Lissafi?

14/12/2022

Zuwaga Masu Shawa'ar Koyon Video Editing a wayar Android, Domin Qarin Bayani Kuna iya Tuntubarmu mu akan Number waya k**ar haka ( +234 814 603 1537 )

Ku Karanta Sabbin Dokokin Hada-hadar Kuɗi Da Aka Samar A Nijeriya Da Za Su Fara Aiki A Farkon Shekarar 2023Ga dokokin k*...
07/12/2022

Ku Karanta Sabbin Dokokin Hada-hadar Kuɗi Da Aka Samar A Nijeriya Da Za Su Fara Aiki A Farkon Shekarar 2023

Ga dokokin k**ar haka:

1. Duk wanda zai cire kuɗi a asusun ATM, iya Naira dubu ashirin (₦20,000) kawai zai iya cirewa a rana.

2. Haka kuma Naira dubu ashirin ce kacal (₦20,000) mutum zai iya cirewa a rana a asusun POS.

3. Naira dubu ɗari ce kacal (₦100,000) mutum zai iya cirewa a ATM ko POS a cikin sati daya.

4. Mafi girman kuɗin Naira za za'a dinga sakawa a dukkanin ATM itace Naira ɗari biyu (₦200).

5. Mafi yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa a cikin banki wato Counter a wuni shine Naira dubu ɗari (₦100,000).

6. Idan kuma wata ma'aikata ce zata cire kuɗin a cikin banki wato Counter, mafi yawan kuɗin da za'a iya cira shine Naira dubu ɗari biyar (₦500,000).

7. Dukkanin kudaden da aka samu dalilin mai karfi na fitar da sama da abinda doka ta amince dashi, Tou za'a biya kuɗin processing fee na cirar waɗannan kudaden.

Idan mutum ne zai cire sama da adadin ba kamfani ko ma'aikata ba, zai biya kudin kamisho wato processing fee na kashi biyar cikin dari da adadin kudin da zai cire wato 5%.

Idan kuma kamfani ne ko ma'aikata, zasu biya kudin kamisho wato processing fee na kashi goma cikin ɗari wato 10% na abinda zai cire.

8. Dukkanin kuɗin da za'a cire ta hanyar wani ya baka Cheque wato 3rd Party Cheque na kudin da ya haura naira dubu hamsin (₦50,000) dole sai a kanta za a cire.

Wadannan wasu ne daga cikin sabbin dokokin hada-hadar kuɗi da bankin CBN ya fitar.

Sabbin dokokin za su fara aiki ne a watan ɗaya na sabuwar shekara (9/01/2023).
-Bashir Sani. 7/12/2022, 6:30am.

APP DIN BLOGGING KOYI DA KANKA (Dawanau Version)A baya kusan shekaru 3 da s**a wuce, idan ba'a manta ba mun taɓa yin app...
04/12/2022

APP DIN BLOGGING KOYI DA KANKA (Dawanau Version)

A baya kusan shekaru 3 da s**a wuce, idan ba'a manta ba mun taɓa yin application na koyon blogging da blogger portal wato BLOGGING KOYI DA KANKA (Ɗanbatta Version)...

To ganin an ɗauki dogon lokaci da yin wancan app ɗin sannan abubuwa da yawa sun canza, don haka na sake updating dinsa zuwa Dawanau Latest Version.

What's new
Sababbin tutorials

Kowane text tutorial is attached with a video

Akwai text zoom in and out saboda dattawa waɗanda idanunsu sun yi nisa k**ar su Sardaunan Dawanau Thé M Jáméél ko waɗanda hasken waya ya fara sheƙe masu idanu irinsu Omar Aderm Omar Aderm Jr.Omar Aderm Jr.

Da dai sauran new features
Zaku iya sanƙamo shi daga playstore anan https://play.google.com/store/apps/details?id=com.sirrinwaya.BloggingCareer

Zaka iya koyan kowanne yare a duniya ta hanyar amfani da wayarka🔥
03/12/2022

Zaka iya koyan kowanne yare a duniya ta hanyar amfani da wayarka🔥

Mungode da ziyartar channel din Arewa Teach. Kada ku manta ku danna Alamar Subscribe sannan ku danna Alamar kararrawar Tuna tarwa Domin samun Sabbin Tutorial...

SABON YAKI NA SHIRIN BALLEWA A DUNIYAR INTANET DA ELON MUSK || "Yaki na shiri ballewa tsakanin Elon Musk, Apple, Google ...
30/11/2022

SABON YAKI NA SHIRIN BALLEWA A DUNIYAR INTANET DA ELON MUSK

|| "Yaki na shiri ballewa tsakanin Elon Musk, Apple, Google da Facebook" ||

Cecekucen ya fara ne yayin da kamfanin Apple s**a ce tsare-tsaren manhajar twitter da Elon Musk ya siya kwanannan ya sabawa dokokin su, inda s**ayi barazanar zasu sauke manhajar Twitter daga kan wayar salula ta iPhone.

Hakanan kamfanin apple suna da tsarin ApplePay wanda ake amfani dashi gurin siyi da siyarwa akan wayar iPhone, sannan dashi ake amfani gurin yin subscription na kowane app akan Apple. Tsarin kuma da suke dashi kuma shine.

Duk App din da yake kan Appstore ake subscription to fah akwai 30% fees da kamfanin apple suke chaji duk lokacin da wani siyayy. Wannan na nufin chajin da Elon yake son farayi na $8, toh duk mai iPhone din da yayi sa kamfanin nada 30%.

Wanda shi Elon Musk yake kallon hakan a matsayin "kura da shan bugu....."😡😡😡

Idan muka dawo kan Google suma dai hakan ne, k**ar yadda Apple sukeyi suma haka suke chajin 30% a GooglePay, kuma shima dai Elon na ganin ai wannan zalunci ne, k**ata yayi ace ba haka bane. Gwara ace akwai wani tsari da zai fi wanda ake kai.

Wannan lamarin ya tunzura Elon Musk idan yace, kamfaninsa suma zasu kirkiri "Altanative Phone" wacce zata kara da iPhone da kuma Andriod, sannan ya kara nuna cewa sufa bazasu biya wannan kudin ba hakananan bazasu bi tsare-tsaren Apple ba.

Wannan shi ake kira gaba da gabanta, Elon yace duk mai blue tick a Twitter sai ya biya $8. Su kuma internet gaint din sunce toh kada fa ya manta 30% din kudin nasu ne, ko kuma su cire app din daga kan manhajar su.

Sannan daga bangare daya kuma akwai Elon Musk worst rival wato kamfanin "Meta" wanda ake ganinnk**ar sune ma suke ta kulle-kullen ganin sun sauko da Twitter baya, k**ar dai yadda CZ ya lalata FTX da sunan regulations.

Kada mu manta fa kamfanin iPhone na Apple da kamfanin Andriod na Google sai kamfanin Meta masu (Facebook, Whatsapp, Instagram) sune kamfanunuwa mafi girma a duniya, suna da Net Worth na:-

Apple = $2.5 Trillion (Quadrillion 1 kenan da Trillion 950 a kudin Nigeria)

Google = $1.3 Trillion (Quadrillion 1 kenan da Trillion 14 a kudin Nigeria)

Meta = $300 Billion ( Trillion 234 kenan a kudin Nigeria)

Nidai abinda nake gani shine, fadan daya fi karfinka kawai ka mayar dashi wasa, wannan shine kuskuren da maigidana SBF yayi a lokacin da CZ yayi masa barazana, sai yake ganin k**ar shima wani shege ne. Idan wadannan mutanen s**a so durkusar da mutum kawai sai dai Allah ya kiyaye.

Author: Muhammad Abdulrahman Sheka

Yauwa! Muna Hada Banners,Flyers, Stickers, iV card, Weeding Events, Fosta,da dai Saura  duk wani nau'in Design akan Fara...
09/11/2022

Yauwa! Muna Hada Banners,Flyers, Stickers, iV card, Weeding Events, Fosta,da dai Saura duk wani nau'in Design akan Farashi me sauqi!

Kuna iya tuntubarmu ta WhatsApp:-
https://wa.me/message/AUNJ5TXPNSKKB1

YADDA ZAKA HANA KOWANE APP YIN AMFANI DA DATA A WAYARKA
05/11/2022

YADDA ZAKA HANA KOWANE APP YIN AMFANI DA DATA A WAYARKA

Mungode da ziyartar channel din Arewa Teach. Kada ku manta ku danna Alamar Subscribe sannan ku danna Alamar kararrawar Tuna tarwa Domin samun Sabbin Tutorial...

29/10/2022

Mata Kenan....

Tana kwance akan shimfiɗar ajali ta ce, Habibina in na mutu zuwa yaushe zaka sake wani auren?

Yana kuka ya ce, zuwa lokacin da ƙasar kabarinki zata bushe. Ta yi murmushi ta ce, ka yi alƙawari? Ya ce, ƙwarai ma kuwa.

Bayan ta rasu sai da ya shafe fiye da shekaru 5 ya na zuwa maƙabarta amma abin mamaki kabarin bai bushe ba.

Allahu Akbar, ya yi mamaki sosai kuma ya ƙudurce a ransa matarsa Waliyyiya ce.

Wata rana ya yi sammako don ziyarar kabarinta, sai ya ci karo da ɗan uwanta, s**a gaisa. Ya ce kazo ziyarar ƴar uwarka ke nan?

Sai ya ce na dai zo don cika wasiyyar da ta mutu ta bar mini. Ta yi mini wasiyyar kullum da sassafe nazo na jiƙa ƙasar kabarinta, hakan zai sanya ta kwanta cikin nutsuwa, shekara da shekaru kenan ina wannan aikin.

Wani aikin sai mata...

CBN ya bayar da adadin kwanaki 47 ga yan Nigeria su mayar da TAKARDUN kudin su Yan 1k da yan da yan 100 da yan 200 zuwa ...
27/10/2022

CBN ya bayar da adadin kwanaki 47 ga yan Nigeria su mayar da TAKARDUN kudin su Yan 1k da yan da yan 100 da yan 200 zuwa bankuna domin ya sauya FASALIN su.

Wannan na zuwane a dai-dai lokacin da NAIRA ke cigaba da Shan Kashi a hannun dalar Amurka inda a kusan kowwace Rana dala take kafa sabon All Time High inda ko a satin da ya GABATA sai da akayi CANJIN dala akan 765 abinda wasu ke ganin sauya FASALIN kudi bashi ne mafi MUHIMMANCI ba illa kokarin inganta DARAJAR su | Gonar Bitcoin

Address

No_21 Muhammad Wabi Street Jama'are
Jama'are

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Teach posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category