19/12/2023
Sen Barau Maliya Zai Gana da Masu Kantin Shoprite Domin Dakatar da Yunƙurin su na Rufe Sashen su Daga Jihar Kano
Mataimakin Shugaban majalisar dattijai, Barau Maliya, Yana ƙoƙarin dakatar da yunkurin da Shoprite daya daga cikin manyan kantuna a Najeriya da yake ƙoƙarin rufe reshensa daya tilo a jihar Kano.
Shahararren kantin sayar da kayayyaki na Ado Bayero Mall a Kano, Shoprite a makon da ya gabata, ya sanar da matakin ficewa daga cibiyar kasuwanci a watan Janairu, yana mai dora hakan a kan "matsalolin tattalin arziki mai kalubale."
Sanarwar da mashawarcin Barau Maliya na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar tace Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan zai gana da mahukuntan kamfanin a cikin makon nan a Abuja kan lamarin.
Wani ɓangare na sanarwar ya kara da cewa, “Ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa yai Yi ƙoƙari wajen Ganin ya dakatar da ficewar Shoprite daga jihar Kano.
Tauraruwa Hausa