27/09/2024
IMANI DA ƘADDARA DA DARAJOJIN ƘADDARA
Tawagar masu tsira ta Ahalus Sunna wal Jama’a suna ban gaskiya da ƙaddara: alherinta da sharrinta. Kuma imani da ƙaddara hawa biyu ne, kuma ko wane hawa yana ƙunsar abubuwa biyu.
Hawa na farko shi ne imani da cewa Allah Maɗaukaki masani ne da halittu, kuma cewa su suna aikata aiki gwargwadon saninsa na tun azal wanda yake sifantuwa da shi tun azal, kuma har abada. Ya san dukan halayensu na ɗa’a da na saɓo, da arzikinsu da ajalinsu. Sa’an nan kuma Allah ya rubuta ƙaddarorin halittu a Lauhul Mahafuz.
Farkon abinda Allah ya halitta shi ne alƙalami. Sai ya ce da shi: Rubuta! Sai ya ce: Me zan rubuta? Sai ya ce: Rubuta abinda zai kasance har zuwa Ranar Ƙiyama.
Saboda haka, abinda duk ya samu mutum, da ma ba zai taɓa kauce masa ba. Kuma abinda duk ya kauce wa mutum, da ma ba zai taɓa samun sa ba. Alƙaluma sun bushe, kuma an ninke takardu, k**ar yadda Allah Maɗaukaki yake faɗi, “Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah yana sanin abinda yake cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yana cikin Littafi, lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.” (Suratul Hajji: 70). Kuma yana faɗin, “Wata masifa ba za ta auku ba a cikin ƙasa ko a cikin rayukanku face tana a cikin littafi a gabanin mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne. (Suratul Hadid: 22).
Wannan ƙaddarawa, wacce take biye da ilmin Allah Maɗaukaki, tana kasancewa a wurare a dunƙule da a fayyace. Allah ya rubuta abinda yake so a cikin Lauhul Mahafuz. Kuma lokacin da ya halicci jikin ɗan tayi (a cikin uwarsa), kafin ya busa masa rai, sai ya aiko Mala’ika ya umarce shi da kalmomi huɗu: Sai a ce masa: Rubuta arziƙinsa da ajalinsa da aikinsa da mara rabo ne shi ko mai rabo, da abubuwan da s**a yi k**a da haka.
Irin wannan ƙaddarawar, a da ƙungiyar Ƙadariyya masu tsananin ra’ayi sun kasance suna musun ta. Amma a yau, masu musun ta kaɗan ne. [“A da, da a yau” da ya ambata yana nufin a zamanin Shaihul Islami Ibnu Tamiyya. Mu a zamaninmu, ba karba ko musu ne matsala ba, SANI shi ne matsala. Sai ka san abu sa’an nan za ka karbe shi ko ka yi musun sa. Muna da sauran aiki!].
Hawa na biyu na ƙaddara shi ne nufin Allah mai zarcewa da ƙudurarsa mai gamewa. Wajibi a nan shi ne imani da cewa, abinda Allah ya so shi zai kasance, kuma abinda bai so ba ba zai kasance ba. Kuma cewa, duk abinda yake cikin sammai da ƙasa na motsi da shuru, ba sa kasancewa sai da nufin Allah Maɗaukaki. Duk abinda ba ya nufi, ba ya kasancewa a cikin mulkinsa. Kuma shi, tsarki ya tabbatar masa, mai iko ne a bisa dukan kome na samammun abubuwa da rasassu. Babu wani abin halitta a cikin sama ko a ƙasa, face Allah ne mahaliccinsa. Ba mahalicci sai shi, kuma babu Ubangiji sai shi.
Amma tare da haka, Allah ya umarci bayi da su yi masa ɗa’a, su yi ɗa’a ga Manzanninsa. Kuma ya hane su ga barin saɓo.
Kuma shi, mai girma da ɗaukaki, yana son masu taƙawa da masu kyautatawa da masu adalci. Kuma yana yarda da waɗanda s**a yi imani, s**a yi ayyuka na ƙwarai. Ba ya son kafirai, kuma ba ya yarda da mutane fasiƙai. Ba ya umarni da alfasha, ba ya yarje wa bayinsa kafirci, kuma ba ya son fasadi.
Bayi masu aikata ayyukansu ne a haƙiƙa, kuma Allah shi ne mahaliccin ayukan nasu.
Bawa shi ne mumini, shi ne kafiri, [Watau shi ne mumini idan ya yi imani, ba’a cewa Allah ne ya imanantar da shi duk da cewa Allah ne mahaliccin imaninsa, kuma da mufinsa ya yi imanin. Shi ne kafiri idan ya yi kafirci, ba’a cewa Allah ne ya kafirtar da shi duk da cewa Allah ne mahaliccin kafircinsa, kuma da nufinsa ya kafirta. Watau imaninsa da kafircinsa aikinsa ne, saboda zabinsa ne, ikonsa ne, kuma Allah zai yi masa sak**ako a kai, duk da cewa imanin da kafircin halittar Allah ne kuma nufinsa ne] shi ne mai biyyaya, shi ne mai fajirci, shi ne mai sallah, shi ne mai azumi.
Bayi suna da iko a kan ayyukansu, suna da nufi. Amma Allah shi ne mahaliccin su da ikonsu da nufinsu, k**ar yadda Maɗaukaki yake cewa, “Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiriya. Kuma ba za ku so ba, sai idan Allah Ubangijin halitta ya yarda.” (Suratut Takwir: 28- 29).
Wannan hawa na ƙaddara, kafatanin ƙungiyar Ƙadariyya, waɗanda Annabi (SAW) ya kira su Majusawan wannan al’umma, suna ƙaryatawa da shi. Wasu masu tabbatar da ƙaddara kuma suna wuce gona da iri, har ta kai su suɓale bawa daga iko da zaɓi da yake da su. Kuma su fitar da hikimomi da maslahohi daga ayyukan Allah da hukunce-hukuncensa.
📚 JERIN LITTAFAN SHI’A NA 11: "Aƙidar Ahalus Sunna" - na Prof. Umar Labɗo
✍ AnnasihaTv
╭─┅───═ঊঊঈ═───┅─╮
📌 Masu son siyen littafan Prof su tuntuɓe mu k**ar haka;
Call/WhatsApp: 08063836963
Twitter: https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
╰─┅───═ঊঊঈ═───┅─