04/08/2021
BUHARI YA FASA KWAI - Karanta ka Raba a shafinka
Dalilin da yasa Najeriya ta shiga cikin Matsalolin Tabarbarewar Tattalin Arziki da Talauci - Muhammadu BUHARI
------------------------
Shugaba Muhammadu Buhari a birnin New York na kasar Amurka, ya sake yin bayani dalla - dalla kan dalilan da ya sa Nigeria ta samu kan ta cikin matsalolin da muke fama da su a yanzu.
Shugaba Buhari yayi bayanin ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu 'yan Nigeria su 15 da s**a yi fice tare da kwarewa a wuraren da suke aiki a kasar ta Amurka, wadanda Babbar Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Kasashen Waje, Mrs. Abike Dabiri-Erewa ta jagoranta s**a gana da Shugaban Kasar.
Ganawar ta bawa Shugaba Buhari damar yi musu bayanin dalla-dalla kan dalilan da ya sa 'yan Nigeria da kasar ke cikin wahalhalu a yanzun, sai dai ya basu tabbacin cewa idan dukkan 'yan Nigeria zasu bada gudunmawarsu ciki harda mazauna kasashen waje, Kasar za sake daidaituwa har ma a koma fiye da yadda ake a baya cikin lokaci ba mai tsawo ba.
Ga bayanin na Shugaba Buhari wanda ya ratsa zukatan duk wadanda suke wurin ganawar...
"Na yi matukar farin cikin wannan ganawa da ku, duk inda ka je a fadin duniya, za ka samun 'yan Nigeria na kwarai kuma hazikai da s**a yi fice ta fannoni daban - daban. Kuma ba suna amfanar kasar da suke zaune ne kadai ba, mafi yawan lokuta suna taimakawa Nigeria musamman a bangaren tattalin arziki.
"Mun shiga matsalolin da muke ciki a yanzu saboda ba mu yi tanadi domin lokaci mak**ancin wannan ba. A misali, daga shekarar 1999 zuwa 2015, a lokacin da muke iya samar da danyen mai ganga milyan biyu da rabi a kullum kuma farashin danyen man ana sayar da shi fiye da dalar Amurka $100, ba mu yi tadani ba, kuma ba mu samar da ayyukan da zasu ciyar da kasar nan gaba ba. Cikin kankanin lokaci a yayin da muka zo a 2015, farashi danyen mai ya fadi zuwa kasa da dalar Amurka $30.
"Na tambaya, ina tanade - tanaden da muka yi domin irin wannan lokaci? Sai aka ce Babu komai, ba mu yi tanadin komai ba. Na sake tambayar ina hanyoyin jiragen kasa da tituna da zasu saukaka mana rayuwa a irin wannan lokaci? Wadanan ma babu. Na sake tambaya, me da me muka yi da biliyoyin dalolin da muka tara cikin wadannan shekaru? Sai s**a ce wai sun sayo abinci. Abinci na biliyoyin daloli? Ban yarda da su ba kuma ba zan taba yarda ba.
"A mafi yawan yankunan Nigeria, muna cin abin da muka noma ne. Mutanen Kudu suna cin gari ne, wadanda suke Arewa suna cin gero ne, wanda su s**a noma shi, kuma wannan abincin da suke nomawa ya kai akalla kaso 60% na abin da muke ci. Saboda haka, ina biliyoyin dalolin s**a tafi? Mun yi wa kan mu matukar barna, mun ki ciyar da kasar mu gaba a lokacin da muke da makudan kudade.
"Idan za mu yi maganar jami'an tsaron mu ne, sun samu daraja, ana girmama su, saboda kokarin samar da zaman lafiya da s**a yi a kasashen k**ar su Burma, Zaire, Sudan, Liberia, Sierra-Leone, kawai cikin kankanin kokaci wadannan jami'an tsaro sai s**a kasa kawo kananan hukumomi 14 daga cikin 774 da muke da su daga hannun 'yan Boko Haram. 'Yan ta'adda sun gagare su, har sai lokacin da muka zo, muka hargitsa su, muka nakasa su, muka rage musu karfi tare da kwato duk wuraren da suke hannun su.
"Kafin mu zo, Boko Haram suna yin abin da suke so, suna kashe mutanen da basu ji ba, basu gani ba a masallatai, majami'u, makarantu, kasuwanni da tasoshin motoci da sauran su. Kuma suna kiran Allahu Akbar, kuma idan har da gaske sun san Allah ba zasu taba yin irin wadannan ta'addanci ba. Musulunci ko kowane addini da na sani ba, bai yarda da ta'addanci ba. Amma sun kashe dubban mutane da sunan addini. Yanzu mun yi maganin wannan ta'addancin.
"Haka kuma wadanda s**a sace dukiyar Nigeria ba sa cikin farin ciki, sun dauki tsageru a yankin Niger Delta, suna yi mana zagon kasa ta hanyar farfasa hanyoyin mai. Muna yin asarar miliyoyin gangar danyen mai a kullum, a lokacin da duk dala dayan da muka samu tana da amfani. Kuma abin haushi ne a ce jihohi 27 daga cikin 36 da muke da su a Nigeria ba sa iya biya albashin ma'aikata.
"Nayi addu'a sosai, Allah ya bani Shugaban Kasa, na tsaya a 2003, 2007, 2011 da kuma 2015, Allah ya amsa addu'a ta. Ku kalli abin da nazo na samu a kasa. Amma ba zan yi nadama ko korafi ba, tunda na roki Allah ne kuma ya bani. A aikin Soja, na samu karin matsayi daga Laftana zuwa Manjo-Janar. Na rike matsayin Gwamna a 1975 a jihar da a yanzu ta haifar da jihohi 6. An daure ni na tsawon shekaru 3, na kuma rike mukamin Shugaban PTF, wanda a lokacin take da naira bilyan 53 a asusun ta.
"Allah ya albarka ce ni sosai, so ba zan taba nuna damuwa ta ko korafi ba. A duk sanda wani ya zalunci ne, ina rokon Allah ne ya bani ikon yafewa. Allah ya bani abubuwa masu tarun yawa.
"Sannan ku tuna, bayan shekaru 16, Jam'iyya guda na mulki, ba jam'iyyar da za ta zo ta samu abubuwa cikin sauki, haka halin Dan Adam yake. Muna bukatar nagartattun hannaye su rike Nigeria, kuma zamu yi amfani da wadanda suke da su a yanzu. Za su na gayyace ku ku dawo gida idan lokacin yayi, saboda haka ina so ku zama cikin shiri."
Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wannan jawabi na sa mai matukar ratsa jiki, dukkan wadannan s**a halarci zaman sun tabbatar da cewa a shirye suke don bada gudunmawarsu don ganin kasar su ta gado ta ci gaba ta kowane fanni.
β Bashir Ahmad,
Maitaimakawa Shugaba Buhari
Kan Sababbin Kafafen Yada Labarai
(Social Media).