Abba aji TV

Abba aji TV This page is the reason why I created it, to create information, to educate, to enlighten and to ple

Musulmi Na cigaba da cincirindo Suna Kwashe ƙudadensu daga bankin Polaris. “Biyo bayan hana ɗaukacin Musulmi ma'aikata n...
14/10/2022

Musulmi Na cigaba da cincirindo Suna Kwashe ƙudadensu daga bankin Polaris.

“Biyo bayan hana ɗaukacin Musulmi ma'aikata na bankin Polaris Zuwa Sallar Juma'a da Shugaban bankin ya aiwatar da hakan, Al'umma masu kishin addinin Musulunci na cigaba da cincirindo a dukkan ilahirin cibiyoyin bankin a Nijeriya Suna Kwashe Kuɗaɗen su.”

DA DUMI-DUMINSA: Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Watanni TakwasKungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya ASUU ta da...
14/10/2022

DA DUMI-DUMINSA: Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Watanni Takwas

Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni takwas ana yi, k**ar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, kungiyar ta cimma wannan matsayar ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.

Wata majiya daga Majalisar Zartarwar ASUU, ta tabbatar da janye yajin tare da bayyana cewa Shugaban Kungiyar na kasa zai fitar da sanarwa a hukumance a safiyar Juma'a.

Kungiyar ta ASUU ta fara yajin aikin ne a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022.

Yaron da a ka gani yana leburanci yana kuka yasamu tallafi.Ɗan Nigeria da a ka gansa satin daya wuce, yana aiki yana kuk...
13/10/2022

Yaron da a ka gani yana leburanci yana kuka yasamu tallafi.

Ɗan Nigeria da a ka gansa satin daya wuce, yana aiki yana kuka dan ya samu kuɗi yataimaka ma mamansa, daga karshe yasamu taimako har an sasa a makaranta. tallafin yafito ne daga ƴan Nigeria.

Sababbin bidiyon ƙaramin yaron, mai suna "ƙamoruddeen" ya wallafu a shafunan tiktok, kana yakoma makaranta cike da farin ciki.

Labarin ƙamoruddeen, ya matuƙar taɓa zuciyar mutane. bayan ya bayyana, babansa yamutu kana bayan zuwa makaranta.

Na Baku Awanni 48 Ku Rufe Kamfanin Simintin Obajana  ~Yahaya Bello Ya Faɗawa Ɗangote.Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ...
13/10/2022

Na Baku Awanni 48 Ku Rufe Kamfanin Simintin Obajana ~Yahaya Bello Ya Faɗawa Ɗangote.

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayar da umarnin rufe kamfanin siminti na Obajana cikin awanni 48.

A makon da ya gabata ne majalisar dokokin jihar Kogi ta zartar da kudirin rufe kamfanin, biyo bayan gazawa wajen amsa gayyatar da gwamnatin jihar ta yiwa Aliko Dangote shugaban rukunin.

Bayan wannan kudiri, an yi zargin cewa matasan jihar sun kutsa kai cikin kamfanin tare da far wa ma’aikata.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ta ce gwamnati ta amince da ƴancin ƴan kasa na gudanar da zanga-zanga, amma kuma ya ce dole ne a mutunta kudurin majalisar dokokin jihar.

“Gwamnan ya kuma bukaci mahukuntan rukunin Dangote da su tabbatar da cewa an rufe masana’antar siminti da ke Obajana cikin sa’o’i 48 masu zuwa domin karrama bangaren gwamnati da ya bayar da umarnin rufe masana’antar har sai kungiyar Dangote ta baiwa majalisar da takardun da ake bukata.

Gwamnatin jihar ta bukaci jama'a da su ci gaba da zama farar hula, masu bin doka da kuma ba da damar bin tsarin mulki.

“Rushe doka da oda ba za su amfanar da kowa ba, domin muna fatan ci gaba da kasancewa jiha mafi zaman lafiya a Najeriya.

“Don haka, Gwamna ya ba da umarnin a saki manyan motocin da ke lodin siminti da aka tsare a fadin jihar nan take ko dai su koma masana’antar ko kuma su tafi wuraren da za su je cikin lumana.

Sanarwar ta kara da cewa "A matsayinmu na Jiha, dole ne mu kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na kasuwanci wanda ya jawo hankalin masu zuba jari da dama a jihar a cikin shekaru bakwai da s**a gabata."

Bankin Polaris ya hana ma'aikatansa musulmi zuwa sallar Juma'a.Ma'aikatan bankin na Polaris na cikin fushin hana su zuwa...
13/10/2022

Bankin Polaris ya hana ma'aikatansa musulmi zuwa sallar Juma'a.

Ma'aikatan bankin na Polaris na cikin fushin hana su zuwa sallar Juma'a da hukumar bankin s**a yi a wani saƙo ta imel da aka aike musu a ranar Talata ta kafar imel.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan bankin ya tsegunta wa jaridar The Daily Reality cewa an gargaɗi wata ma'aikaciyar bankin kan hakan wadda mai kula da tafiyar da aikinta ya yi mata wanda shi kuma Kirista ne.

Saƙon imel ɗin yana ɗauke da saƙo k**ar haka: "an fahimci cewa a ranar Juma'a kukan bar wuraren aikinku ku tafi sallar Juma'a duk kuwa da kun san irin tasgaro da kuma tsayawar aiki da hakan ke janyowa".

"Ku sani cewa babu wata saɗara cikin ƙa'idojin bankin nan da ta ba wa ma'aikaci damar halartar wata sabga da ta shafi addini a cikin lokutan aiki".

"Duba da haka, babu dama ga kowanne ma'aikaci da yake aiki a kowanne sashe na wannan banki na aikata hakan, duk wanda kuwa ya yi kunnen-ƙashi za a ɗauki matakin gaggawa a kansa".

Wani lauya a Kano, Barista Abubakar Saleh, ya zanta da mai rahotonmu cewa wannan hani da bankin s**a yi ya saɓa da ƴancin da kundin tsarin mulki ya ba wa kowanne ɗan ƙasa na damar yin addininsa.

Haka ma wani malamin addinin Islama, Sheikh Abubakar Ayuba Tangimi, ya ce sallar juma'a wajibi ce ga kowanne musulmi. Malamin kuma ya ƙara da kawo wasu hujjoji cikin hadisai da maganganun malamai magabata kan wajibcin sallar Juma'a ga musulmi da kuma haɗarin da ke da akwai wajen ƙin yin ta.

Mutum 60 Sun karɓi Musulunci a jihar Ogun.Daga Hajiya Mariya Azare“Allahu Akhbar musulunci ya samu karuwa, yayin da ɗauk...
11/10/2022

Mutum 60 Sun karɓi Musulunci a jihar Ogun.

Daga Hajiya Mariya Azare

“Allahu Akhbar musulunci ya samu karuwa, yayin da ɗaukacin al'umman dake Oke-Odan na jahan Ogun maza da mata tare da 'ya'yansu kimanin su 60, S**a canja Addini daga kiristanci zuwa Musulunci.

Allah ya kara daukaka musulunci da musulmai.

Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarar kamfanin Meta mamallakin Facebook tana neman ya biya tarar naira biliyan 30
06/10/2022

Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarar kamfanin Meta mamallakin Facebook tana neman ya biya tarar naira biliyan 30

ALHAMDULILLAH: Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja/Kaduna Kenan Da 'Yan Bindiga S**a Sako A jiya
06/10/2022

ALHAMDULILLAH: Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja/Kaduna Kenan Da 'Yan Bindiga S**a Sako A jiya

Duk Musulmin Daya Je Aikin Hajji To Yayi Maulidi - Inji Sheikh Dahiru BauchiKarin bayani 👇🏾👇🏾
05/10/2022

Duk Musulmin Daya Je Aikin Hajji To Yayi Maulidi - Inji Sheikh Dahiru Bauchi

Karin bayani 👇🏾👇🏾

abba muhd aji, learn kanuri language, abba aji tv, Abba Aji TV

Wani Mutum Ya Mutu Bayan Shan Kwalabe Tara Na Barasa A Jihar Filato.Karin bayani 👇🏾
05/10/2022

Wani Mutum Ya Mutu Bayan Shan Kwalabe Tara Na Barasa A Jihar Filato.

Karin bayani 👇🏾

abba muhd aji, learn kanuri language, abba aji tv, Abba Aji TV

Tun Bayan Gudanar Da Tattaki Daga Kaduna Zuwa Zariya Baya Iya Gane Kowa.Wani bawan Allah Me Tattaki Daga Kaduna Zuwa Zar...
30/09/2022

Tun Bayan Gudanar Da Tattaki Daga Kaduna Zuwa Zariya Baya Iya Gane Kowa.

Wani bawan Allah Me Tattaki Daga Kaduna Zuwa Zaria Yana Cikin Tsaka Mai Wuya, Kamar Yadda Rahotonni S**a Bayyana Haka.

Wani almajirin Sheikn El-Zakzaky ke nan, Da Wasu mutane s**a haura gidansa s**a masa duka sun zata ya mutu, Jim Bayan Kwanaki Kalilan Da Yin Tattakinsa Shi Kadai Daga Kaduna Zuwa Zariya.

An Cigaba Da Bayyana Mana Cewa! Wadannan Mutanen Sun Masa Dukan Kawo Wuka, Inda S**a Barshi Nan Kwance Anzatama Ya Mutune.

Bugu Da Kari Har Yanzu Sai Ba'a San Ko Wasu Irin Mutanebane S**a Lakada Masa Wannan Dukanba, Na Ba Gaira Ba Dalili.

Yanzu haka ya zauce baya iya gane komi, k**ar yadda makusantars s**a bayyanawa Duniya Karara.

Yan sanda sun tsaya a hanya domin taimakon wani bawan Allah da s**a gani a tsakiyar daji tayarsa ta samu matsala kuma JA...
29/09/2022

Yan sanda sun tsaya a hanya domin taimakon wani bawan Allah da s**a gani a tsakiyar daji tayarsa ta samu matsala kuma JACK dinsa baya aiki

Mutumin ya ce sai da yayi ta tsaida motoci babu wanda ya tsaya ya taimaka masa har ya yanke tsammani sai Allah ya gitto da wadannan yan sanda s**a zo wucewa inda s**a tsaya s**a dauko nasu JACK din sannan s**a tsaya har saida s**a ga sun cenza masa tayar (da spare) kafin s**a tafi

Kuma a cewar Mutumin yayi-yayi su karbi kudi amma s**a ki karba s**a ce ba don kudi s**a taimaka masa ba....

Wannan wajen da aka yi wa alama da rijiya ce wacce zoben Annabi SAW ya taɓa suɓucewa daga hannun Sayyadina Uthman R.A ya...
29/09/2022

Wannan wajen da aka yi wa alama da rijiya ce wacce zoben Annabi SAW ya taɓa suɓucewa daga hannun Sayyadina Uthman R.A ya faɗa cikinta.

Garin Damasak Ranar Talata ne Al-ummar Gari S**ayi Aikin Gayya Domin Tare Ruwan Kogi da Yake Son Shiga GarinAlhamdulilla...
29/09/2022

Garin Damasak
Ranar Talata ne Al-ummar Gari S**ayi Aikin Gayya Domin Tare Ruwan Kogi da Yake Son Shiga Garin

Alhamdulillah Kawo Yanzu Dai suna Cikin Aminci

Allah Ƴa Ƙiyaye Ƴa Tsare mu Ɗa Sauran Garu-ruwa. Ɗaga Wannan Ɓala'in na (Ambaliya) Ɗa Wanda Zaƴi Ɓiyo Ɓaƴan ta

Fasto Yohanna Buru na Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry ya jagoranci mambobinsa wurin rabon alluna...
21/09/2022

Fasto Yohanna Buru na Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry ya jagoranci mambobinsa wurin rabon alluna ga almajirai a makarantun allo a Kaduna.

Buru ya ce ya yi wannan karamcin ne don karfafa hadin kai, zaman lafiya da fahimar juna tsakanin addinai a yayin da ake bikin ranar zaman lafiya ta kasa da kasa.

Kalaman ɓatanci: Kotu ta ci Abduljabbar tarar Naira Miliyan 10Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Litinin, ta c...
20/09/2022

Kalaman ɓatanci: Kotu ta ci Abduljabbar tarar Naira Miliyan 10

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Litinin, ta ci tarar malamin addinin Musulunci da ake tsare, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Naira Miliyan 10 bisa shigar da kara kan tabbatar da hakkinsa na ɗan ƙasa, inda kotun ta ce hakan rashin ɗa'a ne ga kotun.

Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke, ya bayar da umarnin a biya wadanda ake kara kudaden; da su ka haɗa da Kotun Shari’a ta Kofa Kudu, Kano, da gwamnatin jihar Kano a matsayin waɗanda a ke kara na daya da na biyu.

Mai shari’a Nwite ya kuma baiwa Kabara da lauyansa Shehu Dalhatu umarnin su biya gwamnatin jihar Naira dubu 100.

Alƙalin kotun ya ce da zarar kotu ta gamsu cewa an saɓawa tsare-tsaren kotu wajen shigar da ƙara, to kotu na da hakkin hukunta wanda ya shigar da karar.

Ya ce matakin da lauyan Kabara ya dauka na da nufin samun hukuncin da ya dace ko ta halin kaka.

Nwite ya ce shigar da kara a cikin wata kara mai lamba: FHC/KN/CS/185/2022 a Kano da kuma zuwa Abuja don shigar da ita dai wannan ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1201/2022 kan wannan batu da lauyan ya yi abin alla-wadai ne.

YANZU-YANZU| Sarkin Kano Ya Nada Sheikh Aminu Daurawa Limancin Juma'a.Yau Alhamis 15/9/2022,  mai martaba sarkin kano Al...
15/09/2022

YANZU-YANZU| Sarkin Kano Ya Nada Sheikh Aminu Daurawa Limancin Juma'a.

Yau Alhamis 15/9/2022, mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero, ya amince da nadin Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, amatsayin sabon limamin masallacin juma'a na makarantar Skyline University, dake cikin birnin kano.

HOTUNA: Lokacin da Namomin daji S**a kaiwa Mutanen da Suke daukarsu hoto farmaki na ba Sani ba Sabo a cikin daji.
15/09/2022

HOTUNA: Lokacin da Namomin daji S**a kaiwa Mutanen da Suke daukarsu hoto farmaki na ba Sani ba Sabo a cikin daji.

A maimakon Sunan Shugaba Buhari, Tashar NTA tayi Kuskure inda ta rubuta Gwamna Umaru Fintiri na Adamawa a fuskar Talabij...
13/09/2022

A maimakon Sunan Shugaba Buhari, Tashar NTA tayi Kuskure inda ta rubuta Gwamna Umaru Fintiri na Adamawa a fuskar Talabiji.

Mahukuntan Saudi Arabia sun kame wani mutum da ya gudanar da aikin Umra don neman rahama ga Sarauniyar Ingila Elizabeth ...
13/09/2022

Mahukuntan Saudi Arabia sun kame wani mutum da ya gudanar da aikin Umra don neman rahama ga Sarauniyar Ingila Elizabeth ta 2 da ta mutu a makon jiya ta na da shekaru 96.

Kotun Shari'a ta bukaci kwamishanan yan sandan Kano ya damke Ado Gwanja da wasu mutum 9 Kwanaki tara da bada wannan umur...
11/09/2022

Kotun Shari'a ta bukaci kwamishanan yan sandan Kano ya damke Ado Gwanja da wasu mutum 9
Kwanaki tara da bada wannan umurni, har yanzu hukumar yan sanda bata k**a mutum ko guda cikinsu ba

An rantsar da Charles III a matsayin sarkin Ingila.
11/09/2022

An rantsar da Charles III a matsayin sarkin Ingila.

PANTAMI ALHERI NE GA YAN NIGERIA 💥Rahoto yanuna cewa tunda akayi Najeriya ba'a taba samun ci gabanda aka samu a harkar s...
09/09/2022

PANTAMI ALHERI NE GA YAN NIGERIA 💥

Rahoto yanuna cewa tunda akayi Najeriya ba'a taba samun ci gabanda aka samu a harkar sadarwa k**ar yadda aka samu a zamanin Professor Isa Ali Pantami ba

Bincike yanuna cewa yanzu kudin shiga da Nigeria take samu a harkar sadarwa yafi kudin da take samu a man fetur, wannan yana nuna mana cewa yanzu koda babu man fetur a kasarnan harkar sadarwa kadai ma ya isa Nigeria tayi dogoro da ita k**ar yadda wasu manyan kasashen duniya suke dogoro da ita, irinsu North Korea da sauransu 👌

Hakika PANTAMI ya taka rawar gani don ganin an inganta harkar sadarwa a kasar nan, kafin zuwan PANTAMI kamfonin sadarwar kasarnan suna cin karensu babu babbaka, bana mantawa kafin zuwan PANTAMI ina siyan MTN Data 1Gb akan naira 1000 lokacin kuma ana 3G, daga baya nafara harkar (Data Vending) wato harakar sayarda Data na turawa, alokacin ina sayarda ko wani 1Gb akan naira Dari 600

Daga zuwan PANTAMI sai abu ya canza har kamfononin sadarwa s**a fara sayarda Data 1Gb akan Naira dari #200 mu kuma (Data Vendors) muka fara sayarwa akan Naira 300 ko wani Gb, gashi kuma kwanannan Gwamnatin tarayya da karawa kamfononin sadarwar kasarnan haraji su kuma s**a ce sai sun nunka duk wani abu da ya shafi sadarwa har gwamnati ta rattaba hannu ta amince da karin kudin kira da na Data daga karshe PANTAMI yazo ya dakile wannan shirin nasu

Gaskiya bazan iya bayyana dukkan Canje canje da aka samu a harkar sadarwa daga zuwan PANTAMI ba saide muce Allah ya daukaka shi yasa ya wuce haka, ya kuma yawaita mana irinsa a gwamnatin Nigeria

✍️ Abu Aysha

SHIRU KAKE JI, KAMAR BA ABIN ALKHAIRI YA YI BA.Ministan sadarwa na Nigeria Prof.  Isah Ali Ibrahim Pantami ya tsaya tsay...
09/09/2022

SHIRU KAKE JI, KAMAR BA ABIN ALKHAIRI YA YI BA.

Ministan sadarwa na Nigeria Prof. Isah Ali Ibrahim Pantami ya tsaya tsayin daka, ya aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar korafi akan cewa ka da a kara haraji a harkar sadarwa.

Ministan ya nunawa shubaga Muhammadu Buhari cewa idan aka shigo da haraji, an kara jefa al’umma da tattalin arziki a cikin matsala.

Duk da Irin wanna abin Alkhairi da wannan Bawan Allah ya yi kowa yaja bakin sa yayi shiru. inda ace kuma wani abin sharri ne ba wannan ba, da yanzu kowa ya dauka har Wanda baya posting ma sai yayi saboda bakar kiyayya da hasada. k**ar yadda kuke fitowa kuna tsine masa Albarka, tunda dai wannan abin Alkhairi yayi, kuma ya shafi kowa da kowa k**ata yayi a cire hasada a fito a yaba masa. ana son idan ka fadi sharrin mutum, idan yayi Alkhairi ma ka fada. domin ko wani mutum a duniya yana da nashi Alkhairi sannan kuma yana da sharri.

wato su fa mutane, idan kace zaka faranta musu, zaka musu abin da suke so don su yabeka, to wallahi baka san rayiwa ba, kuma ka batawa kanka lokaci, mutane ba'a iya musu. wannan abu ya saka na Kara daukan darussa.

Allah ya taimaki Isah Ali, ya tsare shi daga sharrin munafukai da kuma ainahin mahasada Amin.

Allahu Akbar-Wanda Ya Fara Fassara Kur'ani Zuwa Turanci Wannan  Shine Wanda Ya Fassara Al kur'ani Mai Girma Tare Da Shar...
09/09/2022

Allahu Akbar-Wanda Ya Fara Fassara Kur'ani Zuwa Turanci

Wannan Shine Wanda Ya Fassara Al kur'ani Mai Girma Tare Da Sharhi Cikin Harshen Turanci Wanda Ake Amfana Dashi A Ko'ina A Fadin Duniya Yanzu Haka Yusuf Ali Wanda Aka Haifeshi A Shekarar 1872 Ya Kuma Rasu A Shekarar 1953.

Ya Allah Ka Jikan shi Da Rahama.

Address

Moduganari Bus Stop
Maiduguri
600251

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abba aji TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abba aji TV:

Videos

Share

Category

Nearby media companies


Other TV Channels in Maiduguri

Show All

You may also like