Hausa News Media Tv

Hausa News Media Tv Wannan shafin zai rinka kawo muku ingantattun labarai da dumi-dumin su cikin harshen hausa.

Top 10 Rollercoaster Rides in the WorldRollercoaster Rides Around The WorldFor those of us that are fans of rollercoaste...
04/03/2022

Top 10 Rollercoaster Rides in the World

Rollercoaster Rides Around The World

For those of us that are fans of rollercoasters, we don't just want an average run of the mill coaster, because to be honest we are not just fans of rollercoasters, we are coaster fanatics. We want to ride the biggest, tallest and the ones which give you the most fun. Therefore, we hunted the globe for the best there is to offer. With that being said, in this article today we will be looking at the ten best rollercoasters out there to visit, and we're talking really bare knuckle riding here, so read on to learn more.

Kingda Ka is by far the biggest rollercoaster we can mention with a top speed of 128mph, and is located in Jackson, USA. This ride is the highest in the world at an astonishing 458ft with a great view, trouble is you won't get time to enjoy it, because as soon as you get to the top it's straight down. Even though this ride only lasts 28 seconds it is worth every penny, that one plunge at 128mph will stay with you for the rest of your life, until you do it again.

Second is the Top Thrill Dragster, which was the first roller coaster to top 400ft at 420ft high and can be found in the American park, Cedar Point. Acceleration is a mind blowing 120mph in just 3.8 seconds, another quick one that only lasts 30 seconds, but it's 30 seconds you won't forget.

Third on our list is Superman: Escape From Krypton found in six flags, California, and at a height of 415 feet, 100mph speed and 28 seconds long, it's just as good as Top Thrill Dragster, definitely worth the trip.

Fourth on our list is the Tower Of Terror, which is the fastest and highest coaster in Australia, and although it's only 28 seconds long it has a height of 390ft and 100mph speed. Tower Of Terror is located in Queensland and when it made its debut in 1998 it was the tallest freefall in the world with a drop of 119 metres or 390ft.

Fifth on the list is Red Fury in Spain in park Ferrari Land in Salou, and has a max speed of 112mph with a duration of only 24 seconds and 367 feet at its highest point.

Number six on the list is Fury 325 in Carrowinds Park, USA and is named due to its height of 325 feet, and maybe also because the duration of the ride happens to be 3 minutes and 25 seconds. Max speed is a racing 95mph, and there are plenty of bends to shake you up for the duration of the ride, with over 6600 feet of track you'll definitely have time to talk about this one afterwards.

Number seven on our list is Steel Dragon 2000 located in a theme park in Nagashima Spa, Japan, but it's worth the trip for a coaster that has a top speed of 153mph, height of 318ft and a duration of 4:00 minutes, now you just want to visit Japan right?

Eight on the list is Millennium Force Sandusky, USA with a height of 310ft, duration 2:20 minutes and a top speed of 93mph with a g-force of 4.5g. Nine on our list is Leviathan in Canada's Wonderland in Vaughan with a height of 306ft and a duration of 3:28 minutes and top speed of 92mph, definitely worth a visit. Number ten would have to be the Intimidator at 305ft high, and a top speed of 90mph, and a duration of 3:00 minutes and this one can be found in Kings Dominion in Doswell.

These giga coasters are just our opinion, because there are many, many others out there that deserve a mention, but thought we would list our top ten in case you missed one. These rides are not for the faint of heart, definite white knuckle rides, which all deserve a re-visit at some point in your life, or first time if you've never been.

Finally, Most of these rides are in parks where there are more than one, so it wouldn't be a one ride trip, you could actually spend a couple of weeks at some of these places, if you're like us, coaster fanatics.

๐™‡๐˜ผ๐˜ฝ๐˜ผ๐™๐™„ ๐˜พ๐™„๐™†๐™„๐™‰ ๐™ƒ๐™Š๐™๐™๐™‰๐˜ผYau Alhamis 03-03-2022 Komitin Marayu karkashin  ๐™…๐™ž๐™—๐™ฌ๐™ž๐™จ ๐™•๐™ค๐™ฃ๐™š ๐˜ฟ s**a gabatar da meeting a  Masjid Saut...
03/03/2022

๐™‡๐˜ผ๐˜ฝ๐˜ผ๐™๐™„ ๐˜พ๐™„๐™†๐™„๐™‰ ๐™ƒ๐™Š๐™๐™๐™‰๐˜ผ

Yau Alhamis 03-03-2022 Komitin Marayu karkashin ๐™…๐™ž๐™—๐™ฌ๐™ž๐™จ ๐™•๐™ค๐™ฃ๐™š ๐˜ฟ s**a gabatar da meeting a Masjid Sautus Sunnah dake Gwange Layin tanki ciki a tsakiyan birnin Maiduguri Jihar Borno, domin tattaunawa kan yadda za'a taimaki yara marayu wanda basu da gata, tattaunawar ta shafi tun daga cin su, shan su, tufafinsu da kuma iliminsu.

Kungiyar dai tuni sun fara shirye-shiryen yadda za'ayi a hada karfi da karfe wajen ganin an sharewa wannan yara bayin Allah hawaye, Musamman a wannan lokacin da ake tunkarar azumin watan Ramadana mai Albarka.

Har ila yau kungiyar tayi kira ga Al'ummar musulmai da suyi koyi da irin wannan aiki aduk inda suke su jajircewa wajen ganin an kula da ilimin marayu tareda abincinsu na yau da kullum domin hakan shi zai haifar mana da da mai ido acikin Al'umma.

Sannan Komitin ta raba wasu mukamai wa membobinta domin samun aiwatar da aiki cikin sauki tareda tsare-tsare yadda ya kamata.

An samu halartan Shugaban Jibwis Zone D ๐’๐ก๐ž๐ข๐ค๐ก ๐Œ๐ฎ๐ก๐š๐ฆ๐ฆ๐š๐ ๐Š๐š๐ข๐ ๐š๐ฆ๐š tareda Yan majalisar sa, sannan an samu halratan manyan malamai da shugabanni na Jibwis reshen zone D.

Muna Rokon Allah ya kara mana ikhlasi kuma ya Azurtamu da abinda zamu ci gaba da taimakon bayinsa Musamman marayu da marasa galihu. Ameen

โœ๏ธ ๐™ˆ๐™ช๐™๐™–๐™ข๐™ข๐™–๐™™ ๐™‰๐™ช๐™ง ๐˜ผ๐™ก-๐™—๐™–๐™ง๐™ฃ๐™–๐™ฌ๐™ฎ
๐‰๐ข๐›๐ฐ๐ข๐ฌ ๐Œ๐š๐ข๐๐ฎ๐ ๐ฎ๐ซ๐ข ๐’๐จ๐œ๐ข๐š๐ฅ ๐Œ๐ž๐๐ข๐š

A fara duban watan Sha'aban a yau Alhamis Sultan ya umarci MusulmaiMai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar ya ...
03/03/2022

A fara duban watan Sha'aban a yau Alhamis Sultan ya umarci Musulmai

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar ya umarci Musulmai a faษ—in ฦ™asar nan da su far duban watan Sha'aban 1443AH da ga yau Alhamis.

Watan Sha'aban shi ne na takwas a jerin watannin Musulunci, wanda da ga shi sai watan Ramadan.

Sultan ya bada umarnin ne a wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban Kwamitin Shawarwari na Harkokin Addini na Masarautar Sokoto, ya sanya wa hannu a jiya Laraba.

Ya ce a na sanar da al'ummar Musulmi cewa yau Alhamis, 29 ga watan Rajab, wacce ta zo daidai da 3 ga watan Fabrairu, ita ce ranar da za a fara duban jaririn watan Sha'aban 1443 AH.

"Sabo da haka sai Musulmai su fara duban jaririn watan Sha'aban a yau kuma duk wanda ya gan shi ya kai rahoton zuwa ga Hakimin ko dagacin ko mai unguwa mafi kusa domin ฦ™arin bayani,"in ji Sultan.

Ya kuma yi addu'ar Allah Ya taimaki al'ummar Musulmi a kan yi wa addini hidima.

Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda Kenan Yayin Da Yake Daga Shayi Tare Da Dafa Indomi Da Kwai Kuma Ya Ci...
03/03/2022

Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda Kenan Yayin Da Yake Daga Shayi Tare Da Dafa Indomi Da Kwai Kuma Ya Ci A Teburin Mai Shayin Domin Nuna Kauna Ga Talakawa

Masu Karatu Me Zakuce?

Buratai Ya Nesanta Kansa Da Fitowa Takarar Shugabancin Kasa  Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin kuma Tsohon Shugaban Ha...
03/03/2022

Buratai Ya Nesanta Kansa Da Fitowa Takarar Shugabancin Kasa


Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin kuma Tsohon Shugaban Hafsan-hafsoshin Rundunar Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai mai murabus ya nesanta kansa daga kiraye -kirayen da wasu ke yi na ya fito neman shugabancin Nijeriya a zaben 2023.

A cikin sanarwar da Birgediya Janar Sani Kukasheka mai murabus ya fitar a Abuja, ta bayyana cewa Buratai na mayar da martani ne kan kiraye -kirayen da wasu โ€˜yan kasar ke yi masa na shiga jamiyyar APC mai mulki tare da tsayawa takarar kuma wallafa fastocinsa na yakin neman zaben.

Sanarwar ta kara da cewa Buratai bai taba nuna shaโ€™awar son tsayawa takarar ba, kuma bai tattuna hakan da kowa ba.

A cewar sanarwar, Buratai ya mayar da hankalinsa ne kawai a yanzu wajen yi wa Nijeriya aiki a kan matsayin mukaminsa na Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, โ€œAn jawo hankali Tukur Yusufu Buratai kan cewar wasu na kiransa da ya fito takarar kujerarar shugaban kasa a kakar zaben 2023 tare da kuma kakkafa fatocinsa kan tsawa takarar.

โ€œWannan kiraye -kirayen da kuma fastocin ba da yawun bakinsa ake yi kuma wadanda suke yin hakan sun yi bisa raโ€™ayin kashin kansu ne amma ba da umarninsa ba.โ€
Sanarwar ta kara da cewa jakadan ya gode wa โ€˜yanโ€™uwa da abokan arziki da kuma masu yi ma sa fatan alheri kan ayyukan samar da ci gaba da yake yi wa kasar nan.

A karshe, sanarwar ta ce Buratai zai ci gaba da yin biyayya tare da kuma gode wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan damar da ya ba shi na yi wa kasa hidima.

Shin zaku zabi Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriya a matsayin shugaban Kasar...
03/03/2022

Shin zaku zabi Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriya a matsayin shugaban Kasar Nigeria a Asherar 2023.

Kuma wane ci gaba kuke tunanin za'a iya samu idan ya karษ“i mulkin Najeriya?

Gwamnatin jihar zamfara ta fitar da miliyan 85 domin maulidin sheikh  Ibrahim inyass "Gwamnatin jahar zamfara ta fitar d...
03/03/2022

Gwamnatin jihar zamfara ta fitar da miliyan 85 domin maulidin sheikh Ibrahim inyass

"Gwamnatin jahar zamfara ta fitar da zunzurutun kudi har naira milliyan 85 a asusun Al'umma domin gudanar da maulidin sheikh Ibrahim inyass wadda aka saba yi duk shekara."

"Maulidin zai dinga kasancewa duk shekara a ranar asabar insha Allahu."

๐˜ผ๐™ฃ ๐™๐™–๐™ฃ๐™– ๐™ฎ๐™–๐™ฃ ๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ž๐™™๐™– ๐™จ๐™๐™ž๐™œ๐™– ๐™ ๐™ค๐™ฉ๐™ช ๐™ฎ๐™–๐™ช ๐™ฎ๐™–๐™ฎ๐™ž๐™ฃ ๐™™๐™– ๐™–๐™ ๐™š ๐™œ๐™–๐™—๐™–๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™™๐™– ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™ž'๐™–๐™ง  ๐™ƒ๐™–๐™ฃ๐™ž๐™›๐™–.An hana 'yan Jarida Shiga kotu, yayin cigaba ...
02/03/2022

๐˜ผ๐™ฃ ๐™๐™–๐™ฃ๐™– ๐™ฎ๐™–๐™ฃ ๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ž๐™™๐™– ๐™จ๐™๐™ž๐™œ๐™– ๐™ ๐™ค๐™ฉ๐™ช ๐™ฎ๐™–๐™ช ๐™ฎ๐™–๐™ฎ๐™ž๐™ฃ ๐™™๐™– ๐™–๐™ ๐™š ๐™œ๐™–๐™—๐™–๐™ฉ๐™–๐™ง ๐™™๐™– ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™ž'๐™–๐™ง ๐™ƒ๐™–๐™ฃ๐™ž๐™›๐™–.

An hana 'yan Jarida Shiga kotu, yayin cigaba da zaman kotu a yau Laraba, kan Shari'ar Makasan Hanifah Abubakar.
Rahotanni sun nuna cewa, an hanasu shiga ne saboda wani Jami'in DSS yana bayar da sheda akan lamarin.

Meye zaku ce dangane da wannan lamarin?

ILLAR WAYAR SALULA GUDA GOMA (10) GA LAFIYAR JIKI:Wayar salula dai  wata abu ce da ake kiran ta da suna handset ko wayar...
02/03/2022

ILLAR WAYAR SALULA GUDA GOMA (10) GA LAFIYAR JIKI:

Wayar salula dai wata abu ce da ake kiran ta da suna handset ko wayar hannu, ta kasance fasahar da aka samu a karni na 20. Wayar salula ta zamanto wata fasaha ce wadda ta mamaye ko ina a cikin duniya, birane da kuma kauyuka.

Masana kiwon lafiya sunyi bincike sosai su kace duk da amfanin da wayar salula ke da shi ga alโ€™umma, har ila yau tana kuma dauke da wani abu wanda mai cutarwa ne ga rayuwarsu. da take iya yiwa lafiyar bilโ€™adam.

Ga kadan daga cikin illolin wayar salula ga jikin Dan Adam:

1-Cancer: Masana kiwon lafiya sun bayyana cewar duk lokacin da mutun ke magana kimanin hyper-microwabes 9000khz na garzayawa kwakwalwar shi, wanda kuma shine ya kan haddasa illolin masu yawa da s**a hada da kara yanayin da ita kwakwalwar da 1ยฐC wanda kan iya haifar da cutar kansar kwakwalwa.

2- Sleep disorders: Wannan sanin kowa dadewa amfani da ita wayar salula da mukeyi ta hanyar chating ko kira yakan sa mu dade bamuyi bacci ba cikin dare yawaitar yin haka har ta sabawa ฦ™waฦ™walwar mu abin yazama jikin mu. wani bincike ya nuna awa 2 kafin baccin na kallon fiskar waya yana shafar bacci mai lafiya sannan yahana hutu mai dadi sakamon hasken wayar da kagama daukar lokaci kana kallo.

3- Increased accident-risk : Yana kara yawaitar hatsari, binciken hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta nuna cewa daga zuwan waya zuwa yanzu hatsari ya karu fiye da kashi 3 zuwa 4 kafin wayar salula tazo, yayin da mutum yake danne dannen wayar salula tana dauke masa hankali akan hanya, har yakai ga accident.

4- Obesity: Bincike ya nuna cewa Yana kawo matsanancin qiba mara amfani saboda karancin motsa jiki sakamakon yawan kwanciya ko zama ana amfani da ita wayar kamar chatin.

5- Hearing impairment: kira a wayar salula samada awa daya (60 minutes) a kunne yana rage lafiyar ji. Yin waya yayinda take yin chaji yana kashe kunne gabadaya in andauki tsawon lokaci anayi.

6- Eye problems: Yana kawo matsalar ido, bincike ya nuna yawan dadewa ana amfani da ita wayar salula yana iya haddasa cutar ciwon ido, saboda haske da โ€œscreenโ€ na wayar ke samarwa, ba wai ga ido kawai hasken na screen ya tsaya ba, yakan kai ga jijiyoyin ido daganan kuma sai ya rasa zuwa cikin kawkwa.

7- Infertility: Rashin Haihuwa, bincike ya nuna Sinadarin radiation frequency dake fita daga wayar hannu ko komfuta musamman yawan saka wayar aljihun wando ko dora komfuta a kan cinyoyin kafa biyu yana kashe ko rage qarfin sinadaran haihuwar s***m.

8 - Infection: Wani bincike ya nuna wayar salula na dauke da Kwayoyin baktriya fiye da ban daki (toilet) sabida yawan gaisuwa da mutane sannan ka tana shi da hannun ka kafin ka wanke, wassu ma suna tabawa sannan kazo kaci abinci da hannun hakan nasa Kwayoyin cuta su samu hanyar shiga jiki.

9- Skin allergies: Wassu daga cikin wayar salula musamman bakckberry suna dauke da sinadaran nickel, chromium and cobalt wanda yakan kawo kaikayi da kurajen fata ga wassu mutanen.

10- Stress : Yawan damuwa, bincike ya nuna daukan lokoci ana amfani da wayar salula tana kawo chanza taswizar Kwakwalwa wanda hakan zai iya kawo stress.

๐˜ผ๐™‰ ๐™Ž๐˜ผ๐™ˆ๐™ ๐™’๐˜ผ๐™‰๐™„ ๐™”๐˜ผ๐™๐™Š๐™‰ ๐˜ฟ๐˜ผ ๐™”๐˜ผ ๐™ƒ๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ผ ๐™๐™‡๐™” ๐™Š๐™‘๐™€๐™ ๐˜ผ ๐˜ฝ๐™„๐™๐™‰๐™„๐™‰ ๐™ˆ๐˜ผ๐™„๐˜ฟ๐™๐™‚๐™๐™๐™„Abin Al'ajabi baya karewa, Musamman tattare da yan kasa ta Nige...
01/03/2022

๐˜ผ๐™‰ ๐™Ž๐˜ผ๐™ˆ๐™ ๐™’๐˜ผ๐™‰๐™„ ๐™”๐˜ผ๐™๐™Š๐™‰ ๐˜ฟ๐˜ผ ๐™”๐˜ผ ๐™ƒ๐˜ผ๐˜ฟ๐˜ผ ๐™๐™‡๐™” ๐™Š๐™‘๐™€๐™ ๐˜ผ ๐˜ฝ๐™„๐™๐™‰๐™„๐™‰ ๐™ˆ๐˜ผ๐™„๐˜ฟ๐™๐™‚๐™๐™๐™„

Abin Al'ajabi baya karewa, Musamman tattare da yan kasa ta Nigeria Saboda baiwa da ilimi tareda hikima da Allah ya basu.

Ayau 01-03-2022 an samu wani yaro dake Gwange sabon layi Maiduguri a jihar Borno ya kera wata hadaddiyar fly over dake dauke da motoci da kuma hanyoyi daban daban, wanda wannan yaron ya futo ne daga gidan talakawa, amma abinda yayi na ilimi ne sosai a wannan karancin shekarun nasa.

Idan kuna bukatan ganin wannan yaron zaku iya tuntubar Hausa News Media Tv ta inbox ko kuma ta what's app nata kai tsaye.

A yayin da Rasha ta mamaye Ukraine, Koriya ta harba makami mai linzami akalla guda daya, a matsayin gwaji Hafsan hafsosh...
28/02/2022

A yayin da Rasha ta mamaye Ukraine, Koriya ta harba makami mai linzami akalla guda daya, a matsayin gwaji

Hafsan hafsoshin sojojin Koriya ta Kudu sun sanar da cewa, Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami da ke gabashin gabar tekun Koriya a ranar Lahadi.

An harba makamin daga yankin Sunan na Koriya ta Arewa da misalin karfe 7.52 na safe agogon kasar, in ji rundunar hadin gwiwa.

Ministan tsaron Japan Nobuo Kishi ya ce Koriya ta Arewa ta harba "aฦ™alla makami mai linzami guda ษ—aya", wanda ya yi tafiya mai nisan kilomita 300 (mil 186) kuma ya kai tsayin kilomita 600 (mil 373), in ji CNN.

Kwamitin tsaron kasar Koriya ta Kudu (NSC) ya ce harba makamin ba abu ne da ake so ba don tabbatar da zaman lafiya yayin da duniya ke kokarin warware yakin Ukraine, a cewar fadar Blue House, ofishin shugaban kasar Koriya ta Kudu.

NSC ta kuma nuna matukar damuwa da nadama matuka dangane da harba makami mai linzami karo na takwas a bana, sannan ta bukaci Arewa da ta gaggauta dakatar da ayyukan da s**a sabawa sulhu ta hanyar diflomasiyya.

Koriya ta Arewa ta kara kaimi wajen gwajin makami mai linzami a shekarar 2022, inda ta sanar da shirin karfafa garkuwarta". a cewar kafofin yada labaran kasar.

DAILY TRUE HAUSA ta ruwaito cewa A cikin makonni hudun farko na shekarar 2022 kadai, Koriya ta Arewa ta kaddamar da gwaje-gwajen harba makami mai linzami guda bakwai, amma babu daya daga cikin makamanta masu cin dogon zango.

Manazarta sun ce karin gwajin da aka yi a bana ya nuna cewa Kim yana kokarin cimma burin cikin gida da kuma nuna wa duniya da ke kara tabarbarewa cewa Pyongyang karanta yakai tsaiko

"Pyongyang tana da kyakkyawan tsari na soji. Karfin gwamnatin Kim da sahihancinsa na da nasaba da gwada harba makamai masu linzami."

โ€˜Rikicin Rasha Da Ukraine Zai Kawo Tsadar Burodi A Najeriyaโ€™โ€˜Rikicin Rasha Da Ukraine Zai Kawo Tsadar Burodi A Najeriyaโ€™...
28/02/2022

โ€˜Rikicin Rasha Da Ukraine Zai Kawo Tsadar Burodi A Najeriyaโ€™

โ€˜Rikicin Rasha Da Ukraine Zai Kawo Tsadar Burodi A Najeriyaโ€™
Burodin ayaba
Burodin ayaba

Sunday Michael Ogwu Da Sani Ibrahim P**i
Mon, 28 Feb 2022 05:49:07 GMT
Akwai yiwuwar rikicin da ake fama da shi tsakanin kasashen Rasha da Ukraine ya sa farashin burodi ya yi tashin farashin gwauron zabo a Najeriya.

Burodi dai na daya daga cikin abincin da aka fi amfani da su a gidajen โ€™yan Najeriya da dama; ba talaka ba mai kudi.

โ€˜Rikicin Rasha Da Ukraine Zai Kawo Tsadar Burodi A Najeriyaโ€™
Burodin ayaba
Burodin ayaba

Burodi dai na daya daga cikin abincin da aka fi amfani da su a gidajen โ€™yan Najeriya da dama; ba talaka ba mai kudi.

Rasha dai ita ce kasar da ta fi kowace kasa fitar da alkama a duniya, inda take samar da sama da kaso 18 cikin 100 na alkamar da ake amfani da ita a duniya.

Hakan dai na nufin muddin yakin ya shafi samar da alkamar kasar, akwai yiwuwar farashinta ya karu a kasuwannin duniya, ciki har da na Najeriya, lamarin dai kan iya haifar da karin kudin duk wani dangin abincin da ake sarrafawa daga alkamar.

A tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 dai, farashin burodi ya karu da sama da kaso 80 cikin 100 a Najeriya.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ce alkama ita ce abinci na uku da aka fi amfani da shi a kasar, yayin da kasar ke iya noma kaso daya cikin 100 kacal nata, ake shigo da akasarinta kuma daga ketare.

Hakan dai ya sa Najeriya kashe sama da Dalar Amurka biliyan biyu a kowace shekara wajen shigo da alkama daga kasashen waje.

A shekarar 2019 kadai, Rasha da Ukraine sun samar da daya bisa hudu na alkamar da aka yi amfani da ita a fadin duniya, kamar yadda Cibiyar sa ido kan Harkokin Tattalin Arziki (OEC) ta tabbatar.

Tuni dai Kungiyar Masu Gasa Burodi ta Najeriya (AMBCN) ta ce babu makawa yanayin zai kara farashin burodin a Najeriya kowane lokaci daga yanzu.

Source Aminiya.

๐™๐š ๐š ๐ฒ๐ข ๐ณ๐šษ“๐ž๐ง ๐ฌ๐ก๐ฎ๐ ๐š๐›๐š๐ง ๐๐š๐ฃ๐ž๐ซ๐ข๐ฒ๐š ๐ซ๐š๐ง๐š๐ซ 25 ๐ ๐š ๐…๐š๐›๐š๐ซ๐š๐ข๐ซ๐ฎ๐ง 2023Hukumar zaษ“e a Najeriya INEC ta sanar da jadawalin babban zaษ“...
26/02/2022

๐™๐š ๐š ๐ฒ๐ข ๐ณ๐šษ“๐ž๐ง ๐ฌ๐ก๐ฎ๐ ๐š๐›๐š๐ง ๐๐š๐ฃ๐ž๐ซ๐ข๐ฒ๐š ๐ซ๐š๐ง๐š๐ซ 25 ๐ ๐š ๐…๐š๐›๐š๐ซ๐š๐ข๐ซ๐ฎ๐ง 2023

Hukumar zaษ“e a Najeriya INEC ta sanar da jadawalin babban zaษ“e na 2023, inda za a gudanar da zaษ“en shugaban ฦ™asa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.

Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.

Kazalika, za a gudanar da zaษ“en 'yan majalisun tarayya tare da na shugaban ฦ™asar.

Zaษ“en gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ษ—in.

A cewarsa, an zaษ“i ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaษ“e, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaษ“en aฦ™alla kwana 260 kafin kaษ—a ฦ™uri'a.

Ya ฦ™ara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaษ“en "a lokacin da ya dace".

Source BBC HAUSA

Dan Gwamna Ganduje zai maka mahaifinsa a kotu bisa kin biyansa kudin kwangila da ya aiwatar Babban dan Gwamnan Jihar Kan...
26/02/2022

Dan Gwamna Ganduje zai maka mahaifinsa a kotu bisa kin biyansa kudin kwangila da ya aiwatar

Babban dan Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Abdulazeez Ganduje, ya yi barazanar kai mahaifinsa kotu in har baโ€™a biya shi cikon kudin da yake bi na kwangila ba.

A ranar 7 ga Mayu 2021 ne dai Ganduje ya bawa kamfanin Abdulazeez mai suna Global Firm Limited kwangila ta naira miliyan 189 kuma aka biya shi naira miliyan 82 bayan ya fara aikin.

Amma sai dai gwamnan daga bisani ya ki biyansa cikon kudin duk da ya gama aikin.

Wata majiya ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA cewa rashin biyan nasa cikon kudin na da alaka da kai karar mahaifiyarsa Hajiya Hafsat Ganduje da ya yi ga hukumar EFCC a shekarar da ta gabata.

A zantawar da jaridar DAILY NIGERIAN ta yi da Abdulazeez, ya tabbatar da cewa ya yi duk iya kokarin da zai yi kudinsa su fito amma sun ki fitowa.

Ya kuma shaidawa wakilinmu cewa rashin biyan nasa na da alaka da takardar da ya kai EFCC, kana kuma da turjiya da ya yi wajen kin bada na-goro ga Gidauniyar Ganduje (Ganduje Foundation).

A takardar da ya rubutawa maaikatar Ilimi ta Jihar Kano ta hannun lauyansa Barista Umar Shehu, Abdulaziz ya ce idan ba'a biya shi kudin nan cikin kwana bakwai ba, to kuwa zai dauki matakin sharia.

Source: Daily Nigerian Hausa

๐‹๐€๐๐€๐‘๐ˆ ๐‚๐ˆ๐Š๐ˆ๐ ๐‡๐Ž๐“๐”๐๐€A jiya Jumma'a 25-02-2022 tawagar mai girma Jarman Sokoto ๐€๐ฅ๐ก๐š๐ฃ๐ข ๐”๐ฆ๐ฆ๐š๐ซ๐ฎ๐ง ๐Š๐ฐ๐š๐›๐จ ๐€.๐€, s**a kawo ziyara ...
26/02/2022

๐‹๐€๐๐€๐‘๐ˆ ๐‚๐ˆ๐Š๐ˆ๐ ๐‡๐Ž๐“๐”๐๐€

A jiya Jumma'a 25-02-2022 tawagar mai girma Jarman Sokoto ๐€๐ฅ๐ก๐š๐ฃ๐ข ๐”๐ฆ๐ฆ๐š๐ซ๐ฎ๐ง ๐Š๐ฐ๐š๐›๐จ ๐€.๐€, s**a kawo ziyara babban birnin Maiduguri Jihar Borno a bisa gayyatan Mai Martaba Shehun Borno ๐ƒ๐ซ ๐€๐ฅ๐ก๐š๐ฃ๐ข ๐€๐›๐ฎ๐›๐š๐ค๐š๐ซ ๐ˆ๐›๐ง ๐’๐ก๐ž๐ก๐ฎ ๐†๐š๐ซ๐›๐š๐ข ๐„๐ฅ-๐€๐ฆ๐ข๐ง ๐„๐ฅ-๐Š๐š๐ง๐ž๐ฆ๐ข.
Bayan ziyara ta Musamman da s**a kaiwa mai girma Shehun Borno Sannan tawagar tasu ta sauka a masallacin indimi islamic trust dake titin Alhaji Muhammadu Indimi acikin Babban birnin Maiduguri domin gabatar da Nasiha wa Al'ummar Jihar Borno.

Babban Shehin Malami Uba Abin koyi Dattijon Arziki ๐๐ซ๐จ๐Ÿ๐Ÿ ๐Œ๐š๐ง๐ฌ๐ฎ๐ซ ๐’๐จ๐ค๐จ๐ญ๐จ shine ya gabatar da Wa'azi tareda bada shawarwari Musamman wa yan uwa AHLUS-SUNNAH wajen ganin anyi riko da sunnah a aikace, shehin malamin yayi kira da aji tsoron Allah sannan a rike Gaskiya da Rikon Amana sannan a yawaita tuba a koma zuwaga Allah kuma aci gaba da yin aikin Alkhairi domin aikin Alkhairi yana kore mummuna.

Daga karshe Shugaban zakka da wakafi na jihar Sokoto yayiwa Matasa Nasiha akan a tashi a nemi sana'a ta halal domin samun cika wato ainihin cika-cikan Musulunci biyu da s**a rage mana acikin guda biyar.

Sheikh Abubakar Kyari Maiduguri Shugaban Imam Malik Islamic Center dake Maiduguri Jihar Borno, shi yayi ta'aliki tareda jinjina wa babban shehin malamin namu Dattijon Arziki ๐๐ซ๐จ๐Ÿ๐Ÿ ๐Œ๐š๐ง๐ฌ๐ฎ๐ซ ๐’๐จ๐ค๐จ๐ญ๐จ bisa alkhairansa da kuma gudummawar da yake bawa addinin Musulunci, shehin malamin yace idan zai kirga Alkhairan Proff bazasu kirgu a baki ba domin ya wuce yanda Dan Adam yake tsammani.

Daga karshe Shugaban Gidan rediyo da talabijin na jihar Borno (BRTV) Alhaji Adamu Isa Abadam shi yayi jawabin rufewa tareda godiya ga wannan tawaga mai Albarka da ta sauka a jihar Borno a babban birnin Maiduguri.

Muna Addu'a Allah ya basu ladan ziyara cikakke sannan ya maidasu cikin iyalansu lafiya.

โœ๏ธ ๐Œ๐ฎ๐ก๐š๐ฆ๐ฆ๐š๐ ๐๐ฎ๐ซ ๐€๐ฅ-๐›๐š๐ซ๐ง๐š๐ฐ๐ฒ
Editor and Writer Darul Ahkam Global Media.

Masu niyyar yin Aure a wannan shekaran, Maza da mata. Allah ya cika muku burinku.
25/02/2022

Masu niyyar yin Aure a wannan shekaran, Maza da mata. Allah ya cika muku burinku.

25/02/2022

Za mu sayo naโ€™urorin harba makamai daga Turkiyya don maganin 'yan binidiga - El-Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ya koka cewa matsalar hare-haren โ€˜yan fashin daji na dada kamari a shiyyar kuma kasar ba ta da isassun jamiโ€™an tsaron ke iya magance ta.

Kan haka ne ya ce shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na yankin s**a yanke shawarar shigowa da naโ€™urorin harba makamai da ake iya sarrafawa daga nesa daga kasar Turkiyya domin taimakawa sojojin saman a kasar wajen murkushe su.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a dazu yayin wani taron manema labarai a fadar Shugaban kasar da ke Abuja.

Ga dai Karin bayaninda ya yi wa Haruna Shehu Tangaza wakilin BBC HAUSA.

24/02/2022

Yadda mai girma Gwamnan Jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya tabbatar Al'umma cewa a yanzu bashida burin zama Shugaban kasa ko kuma mataimakin Shugaban kasar Nigeria kamar yadda wasu suke ikirarin hakan a kudancin kasar.

Me zaku iya cewa dangane da ra'ayin mai girma Proff.

24/02/2022

Yadda ake bin layi wajen shan man petir a Garin Maiduguri.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo SAN tare da Gwamna Zulum da Sanata Kashim Shettima kenan yayin da s**a ba...
24/02/2022

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo SAN tare da Gwamna Zulum da Sanata Kashim Shettima kenan yayin da s**a bar NAF Base zuwa wajen kaddamar da ayyuka a Birnin Maiduguri.

24/02/2022

Kai tsaye kaddamar da Ayyukan Gomnan Jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum, wanda mataimakin Shugaban kasar Nigeria Professor Yemi osibanjo yake budewa.

Ku kasance tare damu Yau Alhamis da misalin 12:00pm domin ganin yadda Mataimakin Shugaban kasar Nigeria Professor Yemi o...
24/02/2022

Ku kasance tare damu Yau Alhamis da misalin 12:00pm domin ganin yadda Mataimakin Shugaban kasar Nigeria Professor Yemi osibanjo zai bude wasu Ayyukan da mai Girma Gwamnan Jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya kaddamar acikin Babban birnin Maiduguri Jihar Borno.

Majalisar Wakilan Najeriya ta karษ“i rahoto 68 kan gyaran Kundin Tsarin Mulki.Majalisar Wakilan Najeriya ta karษ“i rahotan...
23/02/2022

Majalisar Wakilan Najeriya ta karษ“i rahoto 68 kan gyaran Kundin Tsarin Mulki.

Majalisar Wakilan Najeriya ta karษ“i rahotanni 68 na ฦ™udirorin yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima a yau Laraba.

Majalisar ta saka ranar 2 ga watan Maris a matsayin ranar da 'yan majalisar za su fara jefa ฦ™uri'a na tsawon kwana biyu kan batutuwan da gyaran zai shafa kamar yadda jaridar BBC HAUSA ta rawaito.

Mataimakin Kakakin Majalisa Ahmed Idris Wase ne ya gabatar da rahotannin wanda kuma shi ne shugaban kwamatin gyaran.

Tanadin Kundin Tsarin Mulki ya buฦ™aci cewa duk ฦ™udirin da ke son sauya wani ษ“angare na kundin sai ya samu amincewar biyu cikin uku - 240 na wakilai 360 - kafin ya zama doka.

Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya buฦ™aci dukkan wakilan da su halarci zaman da za a yi ranar Laraba da Alhamis na 2 da 3 ga watan Maris.

Ke Duniya!Tsohon Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara Mahadi Ali Gusau kenan Yayin fitowarsa daga Gidan Gwamnati Bayan Tsige...
23/02/2022

Ke Duniya!

Tsohon Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara Mahadi Ali Gusau kenan Yayin fitowarsa daga Gidan Gwamnati Bayan Tsige shi daga mukaminsa..

Allah ka kyautata bayan mu๐Ÿ™

SฬณHฬณIฬณNฬณ YฬณAฬณUฬณSฬณHฬณEฬณ RฬณAฬณBฬณOฬณNฬณ KฬณAฬณ DฬณAฬณ CฬณIฬณNฬณ IฬณRฬณIฬณNฬณ WฬณAฬณNฬณNฬณAฬณNฬณ HฬณAฬณDฬณAฬณDฬณDฬณEฬณNฬณ AฬณBฬณIฬณNฬณCฬณIฬณNฬณ?
23/02/2022

SฬณHฬณIฬณNฬณ YฬณAฬณUฬณSฬณHฬณEฬณ RฬณAฬณBฬณOฬณNฬณ KฬณAฬณ DฬณAฬณ CฬณIฬณNฬณ IฬณRฬณIฬณNฬณ WฬณAฬณNฬณNฬณAฬณNฬณ HฬณAฬณDฬณAฬณDฬณDฬณEฬณNฬณ AฬณBฬณIฬณNฬณCฬณIฬณNฬณ?

๐‹๐š๐›๐š๐ซ๐ข ๐ฆ๐š๐ข ๐ณ๐š๐Ÿ๐ข: ๐Œ๐š๐ฃ๐š๐ฅ๐ข๐ฌ๐š๐ซ ๐๐จ๐ค๐จ๐ค๐ข๐ง ๐™๐š๐ฆ๐Ÿ๐š๐ซ๐š ๐ญ๐š ๐ญ๐ฌ๐ข๐ ๐ž ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ข๐ฆ๐š๐ค๐ข๐ง ๐ ๐ฐ๐š๐ฆ๐ง๐š ๐๐š๐ ๐š ๐ค๐ฎ๐ฃ๐ž๐ซ๐š๐ซ๐ฌ๐š. Gidan talabijin na TVC sun rawaito...
23/02/2022

๐‹๐š๐›๐š๐ซ๐ข ๐ฆ๐š๐ข ๐ณ๐š๐Ÿ๐ข: ๐Œ๐š๐ฃ๐š๐ฅ๐ข๐ฌ๐š๐ซ ๐๐จ๐ค๐จ๐ค๐ข๐ง ๐™๐š๐ฆ๐Ÿ๐š๐ซ๐š ๐ญ๐š ๐ญ๐ฌ๐ข๐ ๐ž ๐ฆ๐š๐ญ๐š๐ข๐ฆ๐š๐ค๐ข๐ง ๐ ๐ฐ๐š๐ฆ๐ง๐š ๐๐š๐ ๐š ๐ค๐ฎ๐ฃ๐ž๐ซ๐š๐ซ๐ฌ๐š.

Gidan talabijin na TVC sun rawaito cewa, yanzu labari ya shigo cewa, mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya rasa kujerarsa bayan da majalisar dokokin jihar ta zauna a yau Laraba.

Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da kwamitin tsige mataimakin gwamnatin ya mika rahoto ga majalisar dokokin jihar, kamar yadda rahotanni s**a kawo a baya.

Kwamitin na mutum bakwai da aka kafa domin binciken laifuffukan da ake zargin mataimakin gwamnan a karkashin jagorancin Mai shariโ€™a Halidu Soba mai ritaya, ya mika rahotonsa ga majalisar dokokin jihar, inji gidan talabijin na Channels. Kakakin majalisar, Nasiru Muaโ€™zu ne ya karbi rahoton da mai shariโ€™a Soba ya gabatar a harabar majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar. Wani mamba a kwamitin Oladipo Okpeseyi ya shaidawa shugaban majalisar cewa, kwamitin ya gudanar da aikinsa cikin tsanaki tare da binciko cikakken gaskiya.

Kotu ta ษ—aure mutumin da ya ฦ™ara aure ba tare da amincewar uwargidansa ba.Jaridar BBC HAUSA ta rawaito cewa wata kotu a ...
22/02/2022

Kotu ta ษ—aure mutumin da ya ฦ™ara aure ba tare da amincewar uwargidansa ba.

Jaridar BBC HAUSA ta rawaito cewa wata kotu a P**istan ta ษ—aure wani mutum wata shida a gidan yari saboda ya ฦ™ara aure ba tare da amincewar matarsa ta farko ba.

Kotun da ke Lahore ta yi watsi da ikirarin mutumin mai suna Saqib cewa addininsa ya ba shi ฦดanci a matsayinsa na musulmi.

Matarsa Ayesha Bibi, ta yi nasara a kotun, bayan ta yi iฦ™irarin cewa ฦ™arin auren ba tare da amincewarta ba ya saษ“a wa dokar iyali ta P**istan.

Kotun ta ci tarar mijin dala dubu biyu.

Masu fafutikar kare haฦ™ฦ™in mata, sun ce hukuncin zai karya guiwar mazan da ke da niyyar ฦ™arin aure, kuma zai buษ—e wa mata ฦ™ofar kai mazajensu kotu.

A P**istan maza na auren fiye da mata ษ—aya, amma dole sai namiji ya nemi amincewar matarsa ta farko kafin ya auri ta biyu.

Yanzu Saqib na da damar ษ—aukaka ฦ™ara kan hukuncin kotun.

An daษ—e majalisar harkokin addinin Islama a P**istan na ฦ™alubalantar dokar iyali ta P**istan tare da bawa gwamnati shawarwari da s**a shafi harakokin addini.

Babban Magana.

๐™๐š๐›๐ž๐ง 2023: ๐‘๐š๐›๐ข๐ฎ ๐Œ๐ฎ๐ฌ๐š ๐Š๐ฐ๐š๐ง๐ค๐ฐ๐š๐ฌ๐จ ๐ฒ๐š ฦ™๐š๐๐๐š๐ฆ๐š๐ซ ๐๐š ๐ฌ๐š๐›๐ฎ๐ฐ๐š๐ซ ฦ™๐ฎ๐ง๐ ๐ข๐ฒ๐š๐ซ ๐ฌ๐ข๐ฒ๐š๐ฌ๐š.Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewancin Najeri...
22/02/2022

๐™๐š๐›๐ž๐ง 2023: ๐‘๐š๐›๐ข๐ฎ ๐Œ๐ฎ๐ฌ๐š ๐Š๐ฐ๐š๐ง๐ค๐ฐ๐š๐ฌ๐จ ๐ฒ๐š ฦ™๐š๐๐๐š๐ฆ๐š๐ซ ๐๐š ๐ฌ๐š๐›๐ฎ๐ฐ๐š๐ซ ฦ™๐ฎ๐ง๐ ๐ข๐ฒ๐š๐ซ ๐ฌ๐ข๐ฒ๐š๐ฌ๐š.

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewancin Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana jagorantar wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.

Fitattun mutane da ฦดan siyasa da s**a halarci taron sun haษ—a da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.

Ana gudanar da taro ne a International Conference Centre da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

A jawabin Kwankwaso, ya ce wasu ฦดan Najeriya ne da s**a damu da abin da ke faruwar a ฦ™asar s**a haษ—a kai don ceto ta daga mawuyacin halin da ta shiga.

Ya ce yunฦ™uri ne na ฦดan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.

A cewar Kwankwaso za su duฦ™ufa wajen farfaษ—o da tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar ฦดan kasa a birni da karkara.

Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Kwankwaso ya ce za su yi wa makiyaya gata na ganin cewa ba a cinye musu burtalai ba, sannan za su bai wa manoma dukkan kariyar da suke bukata.

Tsohon gwamnan na jihar Kano, wanda dan jam'iyyar PDP ne, bai bayyana mukamin da yake son nema ba a wannan sabuwar kungiya ta siyasa.

Sai dai ana rade radin cewa zai fita daga jam'iyyar PDP sakamakon rashin jin dadin abubuwan da ke faruwa a cikinta. Kodayake bai tabbatar da hakan ba.

Wane fata zaku masa?

Address

Lagos Street Maiduguri
Maiduguri
600215

Telephone

+2348029552895

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa News Media Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa News Media Tv:

Videos

Share

Nearby media companies


Other Maiduguri media companies

Show All