17/11/2023
SAKON BARKA DA RANAR JUMA'A DAGA OFFICE NA DG/SSR ALHAJI Ssa Baban Tatu GARKO .🕋🕌📿
Idan Allah ya rufama bawa asiri kai kuma ka dage sai ka tona mashi asiri to zaka tona ma kanka asiri. Haka Idan Allah Yayima bawa suttura, kai kuma kanaso ya tozarta to bazai tozarta ba, kaine zaka kunyata.
Duk yadda zaka yima karya ado tana nan a kayarta, haka zalika duk yadda zakayi kokarin juya gaskiya zuwa karya to bazaka iya juyata ba tana nan a gaskiyar ta.
Abunda nikeso ku gane kowa ya tsaya matsayin da Allah ya aje shi wanda Allah S.W.A yakeso yaje wani mataki, babu wanda ya isa ya hana, hassada tana cutar da al'umma wajen maida kansu baya, domin wanda kake yima hassada gaba zaka turashi kai kuma kanayin baya. NASIHA CE
Allah ya kara Daukaka mu ya karemu daga sharrin Mahassada, mazanbata da munafukai 🤲🤲.
Juma'at Kareem🕋🕌📿
_DG.Baban Tatu Garko Reporter's IIter's II