05/03/2022
Illolin shan magungunan Bature ba bisa ka'ida ba
Shan magani ba tare da ka'ida ba yana daya daga cikin manyan kuskuren da mutanen mu, ke aikatawa a kuda yaushe, wanda hakan ke haifar da matsaloli nan da can. Wasu matsalolin nan take ake iya fahimtar su, wasu kan suna daukar lokaci mai tsawo.
Menene magani
Magani wani sinadari ne wanda ake amfani dashi wajen warkar da cutuka ( maganin cuta).
Muna da magunguna iri daban daban, kowane magani yana da yadda yake aiki, inda yake aiki,matsalolin da zai iya haifarwa a jikin mutum da ma yadda zaibi ya fita daga cikin jiki.
Kamar yadda jikin mutum yake da sassa daban daban, haka magani ma yake aiki a kowanne sashi na jikin dan adam.
Haka kuma akwai magungunan da mutanen suke sha a lokaci daya, wanda wadannan magunguna aikin su iri daya ne. Ma ana ina kasha daya bai k**ata ka sha daya ba, misali magungunan ciwon jiki, ciwon kai, zazzabi da sauransu. Zaka ga mutum ya dauki ciwo takwas mai 100mg yasha tare da diclofenac shima 100mg yasha bayan dukkan su abu daya ne. Ko kuma kaga mutum ya hada su da fildine yasha, da sauran maka manta misalai irin wadannan. Wanda hakan yana daya daga cikin hatsarin kamuwa da cutar ulcer.
Haka magunguna masu É—auke da sinadarin caffeine k**ar su sudrex,cafenol, Panadol extra da sauransu wanda dukkansu abu daya ne yayi su. Paracetamol da caffeine ne kawai acikin su
To be continued insha Allah
Like and share