07/03/2023
Gwamnatin Najeriya na nuna damuwa kan rashin isassun kuɗin aikin ƙidayar jama'a
Clem Agba
Clem Agba/TwitterCopyright: Clem Agba/Twitter
Ƙaramin ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na Najeriya Clem Agba, ya bayyana damuwa kan tasirin da rashin isassun kuɗi da matsalar tsaro da kuma bambance-bambancen al'adu za su yi wa aikin ƙidayar jama'a da za a yi a ƙasar cikin wannan shakara.
An dai tsara gudanar da ƙidayar ne tsakanin ranakun 29 ga watan Maris zuwa biyu ga watan Afrilun wannan shekara.
Mista Agba ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wata ganawa da ya yi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da da sauran masu ruwa-da-tsaki a Abuja da nufin tattauna ɓangarorin da za su iya kawo tarnaƙi ga aikin ƙidayar.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta fitar da fiye da kashi 60 na kuɗaɗen da ake buƙata domin aikin, inda ya ƙara da cewa yanzu ana jiran masu ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su bayar da nasu kason.
Ganawar dai ita ce ta biyu da jami'an hukumar ƙidaya ta ƙasar ke yi da ƙungiyoyin da za su taimaka wajen gudanar da shirin a shirye-shiryen gabatar daƙidayar jama'ar.
Ɗaya daga cikin maƙasudin ganawar shi ne yadda za a samara kudin gabatar da ƙidayar, inda hukumar ya yi alƙawarin gudanar da komai a bayyane.
Duk da cewa an samu matsalolin tsaro a lokacin aikin gwajin da aka yi a wasu ƙananna hukumomin ƙasar, shugaban hukumar ƙidayar ya kawar da fargabar da wasu ke yi na cewa ba za a yi aikin a wasu sasan ƙasar nan.