06/12/2022
Dr. Nasiru Yusuf Gawuna Shine Dan Takara Daya Tilo Dake Da Gogewa Da Gogayya Masu Tarin Yawa
* Ya Siffantu Da Malamai :- Yana da alaqa ta jini da malamai domin jikan Sheikh hassan gawuna ne, Ya taso a cikin harkokin addini don haka yasan darajar malamai da duk harkokin addini,
* Ya Siffantu Da Ma'aikata :- Tsohon ma'aikacin gwamnati ne wanda yayi aikin gwamnati kafin ya shiga harkokin siyasa, Hakan yasa ya san duk hanyoyin cudanyar ma'aikata da yadda za'a kawo hanyoyin chigaban ma'aikata,
* Ya Siffantu Da Yan Kasuwa :- Dan kasuwa ne wanda mulki bai hana shi yin kasuwanchi ba, don haka zai yi kokarin ganin harkokin chigaban kasuwa a fadin jihar kano,
* Ya Siffantu Da Yan Siyasa :- Dan siyasa ne daga tushe wanda ya samu gogewa mai tsayi da s**a hada da shugabanchi tun daga karamar hukuma, Wannan yasa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yasan amfanin yan siyasa da kalubalen dake cikin ta,
* Ya Siffantu Da Attajirai :- Kyakkawar dabi'a yasa attajiran jihar kano da kewaye suke son ganin yayi nasara badan komai ba sai don zai bada hadin kai don ganin an habbaka harkokin tattalin arzikin jihar kano,
* Ya Siffantu Da Talakawa :- Dr. Nasiru Yusuf Gawuna shine dan takarar gwamnan jihar kano wanda yafi kowanne kusa da talaka domin shine ya taso a cikin talakawa, Hakan yasa Idan Allah ya bashi kujerar mulki yasan duk irin kalubalen da talakawa suke ciki domin a cikin su ya taso,
* Ya Siffantu Da Matasa :- Shine shugaban kungiyoyin matasa yan wasan kwallon kafa na shekaru masu yawa badan komai ba sai dan yadda yake jan matasa a jiki hakan yasa yake jagorantar kungiyar na tsawon lokachi,
* Ya Siffantu Da Dalibai :- Tsohon dan gwagwarmayar dalibai ne wanda yana cikin daliban da s**a shugabanchi kungiyar dalibai a jami'ar Usman Fodio Sokoto Wanda tarihin jami'ar bazai manta da irin gudunmawar da s**a bayar ba.
Shine shugaban Karamar Hukumar da yafara bada Tallafin Karatu na SCHOLARSHIP a Nigeria lokacin yana Chairman a karamar Hukumar Nassarawa.
Ku huta lafiya zan dora nan gaba kadan.