11/11/2023
MAYK EXPRESS ONLINE RADIO KIBIYA KANO STATE.
RAHOTO NA CEWA
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) a jihar Bayelsa ta tabbatar da cewa wani jirgin ruwa ɗauke da malaman zaɓe da kayan aiki ya kife a ƙaramar hukumar Ijaw ta kudu da ke jihar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugaban sashen hulɗa da jama’a da wayar da kan al’umma na hukumar a jihar ta Bayelsa, Inec ta ce malaman zaɓen na kan hanyarsu ce ta zuwa rumfar zaɓe ta Koluama.
Sai dai sanarwar ta ce an yi sa’a babu ko ɗaya daga cikin malaman zaɓe 12 da ke cikin jirgin ruwan da ya rasa ransa.
Amma ta ce kayan zaɓe, k**ar takardar rubuta sak**ako da sauran kayan malaman zaɓen sun salwanta a cikin ruwa.
Inec ta ce duk da haka za ta yi ƙoƙarin ganin an gudanar da zaɓe a yankin.
An sace malamin zaɓe
Haka nan sanarwar ta ci gaba da cewa an sace wani malamin zaɓe da aka tura mazaɓar Ossioma da ke ƙaramar hukumar Sagbama a jihar ta Bayelsa.
Ta ce an sace mutumin ne sa'ilin da yake jiran jirgin ruwan da zai shiga zuwa inda aka tura shi, a tashar jiragen ruwa ta Amassoma.
Inec ta ce an sanar da jami'an tsaro game da ɓacewar jami'in nata.