09/06/2023
Baiwar Iya Sarrafa Harshen Hausa.
Tunda nake ban taɓa ganin wanda Allah ya yiwa baiwa iya baiwa ta iya sarrafa harshen Hausa cikin hikima da jan hankali da kalmomi masu rikitar da tunanin mai ƙaramin kai ba, kamar Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Na karanta litattafan Hausa masu yawa, kuma nima na rubuta littafi aƙalla ya kai 15 zuwa sama, na zauna da manyan Daktoci a fannin Hausa kuma wasu daga cikin litattafai na kafin a buga sai na kaisu wajen gogaggun Marubuta domin su tantance kalmomin da ya kamata nayi amfani dasu.
Amma duk da haka Duk lokacin da nake sauraron jawabin Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, babu abinda nake tunani sai cewa " Anya Kwamared ba Farfesan Farfesoshi bane a ɓangaren Yaren Hausa ?".
Saboda idan kaji yana faɗar wasu kalmomi na Hausa sai ka rantse da wani Yaren yake faɗarasu wanda ba Hausa ba, sai bayan kayi bincike mai zurfi ka gane kalmar Hausa ce.
Misali guda ɗaya da zan bamu akwai wata kalma wacce Kwamard yake faɗa "CIN DIRIRIN DINTSI", wannan kalma na ɗauki tsawon lokaci kafin Zuciyata ta nutsu cewa kalmar Hausa ce.
Na tabbata da Kwamared ya kasance Marubucin Littafin Hausa, to babu shakka sai ya zama Zakaran Gwajin dafin da babu kamarsa a Nahiyar Afrika ta fannin tasarifi da kalmomin Hausa.
Ina roƙon Allah ya ƙarawa Kwamared Aminu Abdulsalam Lafiya da ƙarfin Imani Amin.
Ukashatu Abubakar.
Kwankwasiyya Reporters Zamfara State.