Valentine's Day Jewelry

Valentine's Day Jewelry wannan page
zairinga kawo muku
zafafan labarai .masu kayatarwa. Dan haka kuyi like domin samum labarai masu kyau...

09/05/2022
09/05/2022

Malam yace mutum zai iya duba farjin matar da zai aura kafin aure

24/04/2022

Mai Sanaa ya saki matarsa

22/04/2022

Best 2022 Hausa comedy

20/04/2022

Kwamaret yaji jiki

19/04/2022

Ke magajiya" Mai Sanaa ya dibo ruwa

13/04/2022

1c.H SDS
S**a shiga cikin wani babban dakin shakatawa, s**a tarar da mutane zazzaune bisa ababen zama, kowane daga cikinsu yana sanye da tufafi na alfarma masu tsadar gaske. Kallo daya za a yi musu a gane cewa babu daya daga cikinsu da ya san wani abu wai shi talauci. A gaban kowane mutum an ajiye akushin nama, da goran abin sha, da ‘ya’yan itace, da furanni masu kamshin gaske. Ga kuma kuyangi kyawawa suna kada molo suna waka da rawa a gaban wadannan mutane. Mutanen nan na zaune ne sahu-sahu, gwargwadon yawan dukiyar kowa. Manyan attajirai su ne a sahun farko, masu bi musu a sahu na bayansu, su ma masu bi musu a sahun bayansu. A gaban sahun farko akwai wani mutum dattijo mai tsawon gemu, wanda hurhura ta fara fitowa jefi-jefi a cikin gemun. Tufafinsa sun fi duka na sauran mutanen da ke wurin kyau. Yana da fuska mai annuri da yawan fara’a. Ga shi da kwarjini da farin jini. Wannan mutum dai shi ne mai wannan gida. Sindibad dan dako ya dubi dakin shakatawar nan ya yi ajiyar zuciya, ya ce a cikin ransa, “Wallahi da a ce mutuwa na yi, na tashi na gan ni a wannan wuri, da na ce Aljanna ce. Babu shakka wannan wuri fadar wani babban Sarki ce, inda yakan zo domin shakatawa.” Ya matsa gaban dattijon nan da ke gaban mutane ya durkusa ya gaishe shi, ya kuma gayar da sauran attajiran da ke cikin dakin. Ya mike tsaye a gabansu kansa a sunkuye yana duban kasa. Shugaban attajiran, dattijon da yake zaune a gaban sauran attajirai, ya umurci dan dako ya matso kusa gare shi. Ya yi masa barka da zuwa sa’annan ya sa aka kawo masa abin zama, ya umurce shi da ya zauna. Bayan ya zauna sai aka kawo masa abinci da abin sha. Dan dako ya wanke hannunsa, ya yi bismillah ya gini abinci har sai da ya kai masaba gatari. Ya wanke hannunsa ya yi hamdala, ya kuma yi wa attajirai godiya.

Mai gida ya ce masa, “Mun yi murna da zuwanka. Amma menene sunanka?”
Dan dako ya ce, “Ya shugabana, sunana Sindibad dan dako. Amma Sindibad din har ya kusa bacewa sai dai a kira ni da dan dako, domin ita ce sana’ata.”

12/04/2022

1b. HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU Da SINDABAD DAN DAKO.

Hancinsa kuwa ya ce me zai shaka in ba kamshin soyayyen nama
Da Sindibad ya ga irin wannan daula da mai gidan nan ya ke ciki sai ya daga hannayensa sama yana cewa, “Godiya ta tabbata gare ka ya Ubangijin talikai, mai arzuta wanda ya so a lokacin da ya so. Ya Ubangiji ina rokonka, ka yafe mini dukkanin zunubaina, gare ka kadai nake neman gafara. Ya Ubangiji kai ne mai yin yadda ka so ba tare da shawarar kowa ba, kuma babu wanda ya isa ya tambaye ka don me. Kai ne Ubangijin sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu. Kai ne mai arzuta wanda ka so, ka kuma talauta wanda ka so. Kai ne mai daukaka wanda ka so, ka kuma kaskanta wanda ka so. Na tabbata babu wani abin bauta wa da gaskiya sai kai. Hakika kana daukaka wanda ka so k**ar yadda ka daukaka ma’abucin wannan gida. Kana talauta wanda ka so k**ar yadda na tsinci kaina a ciki.” Sai ya wake wadannan baitoci:

Mutum nawa ke wahala tamkata,
Ga wasu sai hutu da sakewa.

Kowace rana ga ni wahalce,
Dauke da kaya babu dagawa.

Dubi wadansu suna nan kwance,
Kullum shan gara da dadawa.

Ba su tunanin daukar kaya,
Mai nauyi ko mai sabawa.
Asalinmu da kai duka daya ne,
Ruwa na maniyi mai turawa.
Banbancinmu akwai shi da dama,
Tamkar na madaci ko zumuwa.

Ya Allahu gare ka na roka,
Ba ka zalunci cutarwa.

Lokacin da Sindibad dan dako ya gama rera wannan waka sai ya dauki kayan dakonsa ya dora a kai zai tafi. Sai ga wani bawa ya fito daga cikin gidan, mai kyakkyawar fuska da madaidaicin jiki, da tufafi na alfarma. Ya k**a hannun dan dako ya ce, “Shigo ciki shugabana na kira.”

Dan dako ya yi tsaye ya ki shiga cikin gida, ya ce wa bawa shi sauri yake yi ya kai kayan da ke bisa kansa. Bawa ya ce babu makawa sai ya shiga cikin gida. Da dai ya ga bawan nan ba zai bar shi ya tafi ba sai ya ajiye kayansa a bakin kofa, inda wani bawa ke gadi, ya bi bawan da aka aiko s**a shiga cikin gida tare. Dan dako ya yi ta ware ido yana kallon kayan kawar da aka sanya a cikin gidan.

12/04/2022

1a. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

Daga Littafin Labarun Dare Dubu Da Daya

Sabuwar Fassarar.:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.

(Tare da Bukar Mada)

An yi wani mutum a cikin Birnin Bagadada, lokacin mulkin Halifa Haruna Rashid, mai suna Sindibad. Wannan mutum ya kasance talaka ne, ba shi da wata sana’a sai dako – watau ya rika daukar wa mutane kaya bisa kansa daga wani wuri zuwa wani wuri ana biyansa. Wata rana Sindibad ya yi dakon wasu kaya masu nauyi, lokacin kuwa ana koda rana, kafin ya isa wurin da zai kai kayan nan ya yi gumi sharkaf, ga shi kuma ya gaji likis, sai ya biyo ta gaban wani babban gida. Da ganin wannan gida na wani babban attajiri ne, mai ji kudi. An share gaban gidan tas, an zuba wa shuke-shuken da ke wurin ruwa. Kodayake ana tsananin zafin rana amma gaban wannan gida sai wata iska mai sanyi ke kadawa k**ar lokacin hunturu. Sindibad ya hangi wani dandamali a gaban gidan cikin shuke-shuken nan, ya ce a ransa, “Bari in dan zauna wurin nan in sarara kadan.” Ya ajiye kayan dakonsa ya zauna bisa dandamali yana kwasar sassanyar iskar da ke tashi, sai ya ji wani irin kamshin abinci mai dadi na jifarsa daga cikin gidan nan. Can kuma sai ya rika jin kidan molo da busar sarewa na tashi. Ya jiyo muryoyin ‘yan mata na rera wakoki, sai dai bai jin abin da suke fada saboda nisa. Daga cikin lambun gidan kuma tsuntsaye ne iri-iri bisa furannin suna ta rera nasu wakoki. Da ya duba kasa kuma sai ya ga wadansu ‘yan kananan kwari masu ban sha’awa suna ta kai da komowa a cikin ciyawar da ta fito kasan furannin. Sindibad ya yi mamaki matuka da yadda Allah mai girma da daukaka ya tsara wadannan abubuwa daki-daki, kowane gwanin ban sha’awa. Zuciyarsa ta yi fari bisa ga wadannan abubuwa da ke debe masa kewa. Amma kuma da ya tuna da halin da yake ciki na talauci sai ransa ya baci. Ya tashi ya leka cikin lambu sai ya hango bayi suna ta aiki sai ka ce gidan wani Sarki, wasu na ban ruwa, wasu na nome ciyayi, wasu na tsinkar ‘ya’yan itace.

31/03/2022

Sai nayi tusa Musa Mai Sanaa arewatvplus Ali nuhu Adam a zango rahama sadau

25/01/2022

Gara

25/01/2022

Allah ya jikan hanifa abubakar ya gafarta mata

Daya daga cikin matafiyan da s**a tsira daga hanun 'yan bindiga dadi a hanyarsu ta sokoto zuwa kudancin Nigeria Tace a g...
11/12/2021

Daya daga cikin matafiyan da s**a tsira daga hanun 'yan bindiga dadi a hanyarsu ta sokoto zuwa kudancin Nigeria
Tace a gaban idanta aka kashe mahaifiyarta da yaranta hudu

Bayan ta Sami nutsuwa tayi wannan jawabin👆👆

Danna wannan rubutun👇
https://youtube.com/channel/UCtZThx5Xa1OJlgD8vomwBYQ

Gagarumar karuwa da musulunci da musulmai s**a Sami ajihar edo kudancin Nigeria na mutun 104
11/12/2021

Gagarumar karuwa da musulunci da musulmai s**a Sami ajihar edo kudancin Nigeria na mutun 104

10/12/2021

30/10/2021

Dukiyar Nigeria Dangote Bua Mangal

12/10/2021

Gidan badamasi cut out

09/10/2021

Yadda zaka sa matarka saurin kawowa by Munirat Abdussalam

07/10/2021

Mutane sun koma dabbobi #18+

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Valentine's Day Jewelry posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Valentine's Day Jewelry:

Videos

Share

Category