17/05/2022
KASHEDINKA DA CIN KUDIN HARAM
Manzon Allah(ﷺ) ya ce: "Babu wani jiki da jini da za su shiga Aljannah, matuqar sun ginu a kan cin kudin zalunci, wuta ita ce ta fi dacewa da su".
Tirmidhi, Ibn Hibban da Dabarany s**a ruwaitoshi, Albany ya ingantashi.
Shaykh Ibnu Bazz Allah yayi masa rahama ya ce: Wannan wani Alqawarine na narkon azaba daga babin alqawarin azaba da gargadi/tsoratarwa, Wanda yake nufin: Duk wanda jikinsa ya tsiro da cin riba, ko kwacen kudin mutane, ko ta hanyar sata, to lallai an yi musu alqawarin narkon azaba, dan haka wajibine a kiyayesu ashiga taitayi, dole ne neman musulmi ya zama na halal, ya kiyayi zaluntar mutane, ko cin Riba, ko ha'inci a cikin mu'amaloli, ko satar kudin mutane da makamantansu.
فتاوى نور على الدرب