20/08/2022
Ance bayan anyi juyin mulki na *1967*, duk lokacin da *Janar Murtala Mohammed* ya hadu da *Dan Masanin Kano,* sai ya ringa yi masa irin wasan nan na malami da dalibin sa. Ya kan ce masa, *_
"Mun dai kori, 'yan siyasa, sai aje kuma a nemi sana'a"._* Shi kuwa Dan Masani, sai ya maida masa da cewa, *_"Ai ka san akuya ko bata haihuwa, tafi kare"._* A haka suke raha duk lokacin da s**a hadu.
Rannan sai Murtala ya zama shugaban kasa, ya kuwa tashi haikan akan yaki da zalunci da rashawa da ya addabi Nigeria. Kusan komai gaskiyar ka kana shakkar ace Janar Murtala na neman ka. Kwatsam sai ya aiko a gayawa Dan Masani cewa yana neman sa a *Dodan Barracks* (fadar gwamnati da ke Lagos kafin a dawo Abuja).
Dan Masani ya kwana yana jan Lahaula, saboda bai san neman da Murtala yake yi masa ba.
Da safe ya hau jirgi, ya nufi Lagos, ya sauka a Airport, sai ya nufi Dodan Barracks. Yana zuwa aka sanar da shugaban kasa, shi kuma yace a shigo da shi ofishin sa.
Da aka kai shi gaban Murtala, s**a gaisa, sai Janar yayi masa barkwancin da ya saba yi in sun hadu:
_"Mun dai kore ku 'yan siyasa, sai a je a nemi sana'a!"_
Sai Dan Masani yayi shiru. Murtala yace,
_"Allah Ya gafarta ya kayi shiru?"_
Sai Dan Masani yace, *_"Ai kai a karnukan ma,
karen Ashabul Kahfi ne, wanda aka ce za'a shiga Aljanna da shi!"_*
Nan fa Murtala ya fashe da dariya yace masa, _"To dama ina son in baka shugaban Hukumar Koken Ma'aikata ne (Public Complaints Commission)._