01/12/2020
BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA HON. PANTAMI
Saƙon mai sauƙin fahimta ne matuƙar ka kasance Malami na Allah, mai kuma tsoron Allahn.
Ba kuma tsayi ne da shi ba, don ba tashin-tashina zanyi maka ba kasancewar ƙarancin lokacin da wasu al'amuran ke tsimayin ɗaukina.
Kafin shigar ka cikin ƙunshin wannan Gwabnatin tun a wa'adi na farko, a baya ka kasance Malamin addinin musuluncin da ɗumbin musulmi ke tasirantuwa da lafuzanka, musamman waƴanda s**a jiɓinci s**ar Gwabnatin kan yawaitar salwantar rayukan al'umma. Wannan ina batu ne ba tare da na sanyo irin ƙaruwar da ake da kai ba ta hanyar sauraron karatuttukan ka a kafafen sadarwa. Dalilin kenan da yasa ka shahara har kayi sunan da nan da nan kowa ya sanka yake kuma iya shaida muryarka. Muryar da a yau ita ce ta zamanto abar zargi da munafunci a gurin mafi ɗumbin Musulman da suke da hankali.
Hon. (SHEIKH) Pantami, yana da kyau ace a matsayin ka na malami ka fi kowa sanin alamomin munafuki da s**a zo a cikin Hadisin Masoyin Mu (SAW).
A ranar da ta kasance ranar da majalisa za ta tantance ka, ka bayyanawa majalisa cewa kana da dabarun hanyoyin zamani bisa ma'aunin kimiyya da fasaha da za ta taimaka wajen ganin an bi sawun duk wani ɗan ta'adda, ko nace wasu Ƴan ta'adda. Amma har yanzu da kake kan kujerar MINISTA mun kasa ganin cikar wannan batun naka, wanda kai da kanka kan furta shi.
Baya ga haka, kai ka furta cewa za a rufe duk layukan wayar da akayi rijistarsu da sunan mutum ɗaya, matuƙar s**a haura guda uku. Amma a zahiri batu kuma mafi inganci har yanzu akwai irin waƴannan layukan da suke amfani, ba a rufe su ba. Ƙarawa ma, har gobe ana siyar da sabon layin waya mai rijista akansa.
Tun zamowarka MINISTA, ni dai ban ga wani sauyi da zai sanya a bambanta ka da sauran takwarorinka wajen ƙarya da yaudara ba. Domin dai har gobe ana samun matsalar Network. Kamfaninnikan waya suna satarwa jama'a kuɗin credit. Data har gobe akwai ta banza mara amfani, wacce za ka siya, amma har ta ƙare baka mori rabinta ba. Masu amfani da Glo shaida ne akan hakan.
A matsayinka na Malamin addini, dan Allah meye hukuncin mutum irin ka?
A baya kayi Kuka, kayi alƙunutu, ka sharce majina, duk don ana kashe mutane. Sai gashi kisan da ake na yanzu ya zarce na bayan, amma kuma ba muji gunjin ka ba.
Kai da kanka ka taɓa bayar da labarin irin yadda masu mulki da masu muƙamai ke sauka daga matsayin su yayin da duk s**a gaza gudanar da amanar al'umma. Amma sai ga shi ka tsinci kanka tsamo-tsamo cikin irin labaran naka, amma kuma kayi gum k**ar baka san me ke faruwa ba.
Na rantse da Allah, da waƴancan kalaman naka na baya akan Gwabnatin da ta gabata, wallahi baka da dalili na kusa ko na nesa, ko wata hujjar ci gaba da kasancewa cikin wannan Gwabnatin matuƙar da gaske kai na Allah ne ba mai fuska biyu ba.
Dan haka a shawarce cikin girmamawa, kawai ka ajiye muƙaminka na MINISTA saboda gazawarka ga cika alƙawarin da kai ka ɗauka da kanka. Muddin ba haka ba, wallahi girman ka da girman maluntarka duk sai ka rasa su. Kafin kuma kaje ka haɗu da Allah da Annabinsa Muhammadu (SAW).
Ƙaunarka nake, shi yasa na baka wannan shawarar.
©️ Na Ƴar Talla.