ASD HAUSA

ASD HAUSA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ASD HAUSA, Broadcasting & media production company, Kaduna.

Zuwa Yanzu Shin Ko Kana Ɗaya Daga Cikin Waɗanda S**a Samu Saƙon 25k Daga Babban Bankin Nigeria CBN Domin Rage Raɗaɗin Ta...
08/11/2023

Zuwa Yanzu Shin Ko Kana Ɗaya Daga Cikin Waɗanda S**a Samu Saƙon 25k Daga Babban Bankin Nigeria CBN Domin Rage Raɗaɗin Talauci?

Fitaccen mawakin Najeriya Burna Boy, ya yi asarar dala miliyan 5 na wasan da aka shirya a Dubai. Mawakin ya ki karban ta...
06/11/2023

Fitaccen mawakin Najeriya Burna Boy, ya yi asarar dala miliyan 5 na wasan da aka shirya a Dubai.

Mawakin ya ki karban tayin ne saboda an haramta shan taba a kasar kamar yadda Daily Loud ta ruwaito.

Me za ku ce?

Hotunan wata dattijuwa kenan dake tallan kayayyaki a karkashin Gadar Dantata kusa da Ofishin Glo akan titin Murtala Muha...
03/08/2023

Hotunan wata dattijuwa kenan dake tallan kayayyaki a karkashin Gadar Dantata kusa da Ofishin Glo akan titin Murtala Muhammad Way dake nan Kano.

A baya iya samari ne ke irin wannan Sana'a, amma ko me kuke ganin ya jawo tsofaffi Suma s**a fata shiga wannan Sana'ar?

📸

Wasu daga cikin jarumai daga masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood sun halarci wajen shagalin bikin   jaruma ...
28/07/2023

Wasu daga cikin jarumai daga masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood sun halarci wajen shagalin bikin jaruma Momi Gombe.

📷 Sunusi Oscar 442

Manhajar sada zumunta ta WhatsApp ta kara bijiro wa masu amfani da ita hanya mafi sauki ta yadda za a iya kallon hotunan...
27/07/2023

Manhajar sada zumunta ta WhatsApp ta kara bijiro wa masu amfani da ita hanya mafi sauki ta yadda za a iya kallon hotunan da mutum ya sanya a 'status' daga WhatsApp zuwa a shafinsa na Facebook.

DCL HAUSA

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA Ya Bayyana Cewa Yana Bukatan Kowa Ya Yafe Masa Alba...
13/07/2023

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA Ya Bayyana Cewa Yana Bukatan Kowa Ya Yafe Masa Albarkacin Alkur'ani Mai Girma, Kuma Shima Ya Yafe Wa Kowa.

Shehin Malamin Kuma Babban Jagoran Darikar Tijjaniyya A Duniya Ya Bayyana Hakan Ne A Birnin Tarayya Abuja Yau Alhamis 13/07/2023.

Tsalle Daya

Ni Ba Musulma Ba Ce, Shauƙin Soyayar Da Musulmai Suke Yiwa Annabinsu Ya Birgeni, Shi Yasa Na Rera Masa Waka, Cewar Sarah...
10/07/2023

Ni Ba Musulma Ba Ce, Shauƙin Soyayar Da Musulmai Suke Yiwa Annabinsu Ya Birgeni, Shi Yasa Na Rera Masa Waka, Cewar Sarah Aloysius Ta Cikin Shirin Fim Ɗin Daɗin Kowa

Masu karatu wanne fata kuke da shi ga Sarah da ta rerawa shugaban halitta Annabi Muhammadu S.A.W waƙa, duba da ita ba musulma ba ce?

A Wannan Zamani Mijin nagari Wahala Yake - Nafisa Abdullahi
10/07/2023

A Wannan Zamani Mijin nagari Wahala Yake - Nafisa Abdullahi

Nayi Alkawarin Bada Kyautar Gida 3 Bed Room flat a duk Unguwar da suke so A Minna da kuma Naira Miliyan Biyu 2M Gudunmaw...
10/07/2023

Nayi Alkawarin Bada Kyautar Gida 3 Bed Room flat a duk Unguwar da suke so A Minna da kuma Naira Miliyan Biyu 2M Gudunmawar Bikin Sadik Abdullahi kwatu da Hafsat Rufai idan har lamarin ya tabbata.

Inji Hon. Lado Suleja

Manhajar Threads ta kafa tarihin zama irinta ta farko da ta sami miliyoyin mabiya a 'yan kwanaki. Kuna daga cikin mutane...
10/07/2023

Manhajar Threads ta kafa tarihin zama irinta ta farko da ta sami miliyoyin mabiya a 'yan kwanaki. Kuna daga cikin mutane miliyan 100 da yanzu haka suke amfani da manhajar Threads?

Ya kuka ga manhajar?

Abu Kamar Wasa Comment Na Facebook Na Shirin hada Aure"A yau ne Shafin Tsalle Daya, Muka wallafa hoton wata Matashiya ma...
10/07/2023

Abu Kamar Wasa Comment Na Facebook Na Shirin hada Aure"

A yau ne Shafin Tsalle Daya, Muka wallafa hoton wata Matashiya mai suna Hafsat Rufai wacce take bikin ranar zagayowar haihuwar ta.

Bayan daura hoton, Sai wani Matashin Dan Siyasa mai suna Sadik Abdullahi kwatu yayi comment da cewar "ta hadu kuma yana so".

Bayan da Jajirtacciyar Baiwar Allah nan, Mai Gidauniyar bada tallafi musamman ga marayu Hajiya Safiya Nasidi taga Comment din.Sai ta ce ta bashi auren nata, domin acewar ta diyar ta ce.

Kuma ta kira Limamin Tsalle Daya inda ta tabbatar da cewa indai Sadik da Gaske yake yi ita zata dau ragamar bikin.

Shin wani shawara zaku baiwa Matashin?

Daga shafin Tsalle Daya

Yawan amfani da fetur ya ragu matuka a NijeriyaMe ya jawo hakan?
10/07/2023

Yawan amfani da fetur ya ragu matuka a Nijeriya

Me ya jawo hakan?

Shugaban kasa Bola Tinubu ya aike da sunayen wadanda yake son nadawa mukamin ministoci ga hukumomin DSS da EFCC.Me ake f...
10/07/2023

Shugaban kasa Bola Tinubu ya aike da sunayen wadanda yake son nadawa mukamin ministoci ga hukumomin DSS da EFCC.

Me ake fatar samu daga sabbin ministocin Tinubu?

LABARI DA ƊUMI ƊUMI: Za a Yiwa Ɗan Daudu Ɗin Nan Bobrisky Dashen Mahaifa A Ingila.Labarin dake Shigo mana yanzu ya tabba...
10/07/2023

LABARI DA ƊUMI ƊUMI: Za a Yiwa Ɗan Daudu Ɗin Nan Bobrisky Dashen Mahaifa A Ingila.

Labarin dake Shigo mana yanzu ya tabbatar mana an samu nasarar yiwa rikàƙƙén Ɗan dàudú ɗin nan dake zaune a jihar legas wato Bobrisky tiyata a mazaunansa dakuma al auwarsa. yanzu haka a ƙasar ingila.”

Rahoton ya tabbatar da cewa yanzu Bobrisky baida maraina sannan an ɗebe su gaba ɗaya sannan an kara masa girman mazaunansa, an kuma yi masa dashen nono a kirjin jinsa, abinda ya rage kawai shine za ai masa dashen mahaifa ta yadda zai iya samun ciki har yakai ga Haihuwa.”

ALFIJIR HAUSA ta tattare cewa Bobrisky ya kashe maƙudan miliyoyin kuɗaɗe domin ganin an sauya masa duk wasu halittunsa na tashi daga jinsin maza zuwa ta mata, “inda ya kara bayyana cewa a shirye yake ya ci gaba da ɓatar da maƙudan sama da waɗanda ya kashe a baya don ganin Tabbatar an dasa masa mahaifa har ya kai ga haihuwa.”

Me nene ra'ayoyin ku kan wannan aikin na ƙarshe da za a yiwa Bobrisky ɗin?

ALFIJIR HAUSA

ALLURA CIKIN RUWA: Rukayya Muhammed Mai Gida Da Mota Da Jarin Milyan HamsinWanne fata zaku yiwa Matashiyar?
09/07/2023

ALLURA CIKIN RUWA: Rukayya Muhammed Mai Gida Da Mota Da Jarin Milyan Hamsin

Wanne fata zaku yiwa Matashiyar?

Da mu da ku ku zo mu yi tsinuwa ga juna kan duk wani mai zagin sahabbai ko raina matan Annabi, Allah ka tsinewa duk mai ...
09/07/2023

Da mu da ku ku zo mu yi tsinuwa ga juna kan duk wani mai zagin sahabbai ko raina matan Annabi, Allah ka tsinewa duk mai zagin sahabban Mànzón Âllàh - Sheikh Zakzaky.

ALFIJIR HAUSA

"GARIN DA YAFI KO WANI GARI TARIHI A AREWACIN NAJERIYA"Garin Zungeru dake Karkashin Karamar Hukumar Wushishi ta Jihar Ne...
09/07/2023

"GARIN DA YAFI KO WANI GARI TARIHI A AREWACIN NAJERIYA"

Garin Zungeru dake Karkashin Karamar Hukumar Wushishi ta Jihar Neja A yankin Arewa Maso tsakiyar Najeriya, Gari ne wanda babu yadda tarihin kasan nan zai kammalu ba tare da ita ba.

A wannan Gari ne aka hada yankin kudanci da Arewacin Najeriya A Shekarar 1914 kuma anan ne aka baiwa kasar nan suna ta ( Nigeria).

Akwai abubuwan tarihi masu matukar muhimmanci a Garin daya kunshi Ginannen kasuwa na farko A yankin Arewa wanda Lord Lugard ya Gina, Majami'a ta farko A Arewa, dama dai sauran su.

A Garin Zungeru ne aka haifi Shugaban kasa na farko A Najeriya Dakta Nnamdi Azikiwe.

Amma sai-dai duk da wanann irin Gundumuwar da Garin ta bayar babu wani cigaba data samu ta fannin ababen more rayuwa da makamantan su.

~ Tsalle Daya

Wata Kotu A Jihar Kano Ta Dakatar Da Gayyatar Da Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Jihar ta yiwa Ganduje Kan Bidiyon Dala.
07/07/2023

Wata Kotu A Jihar Kano Ta Dakatar Da Gayyatar Da Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Jihar ta yiwa Ganduje Kan Bidiyon Dala.

Address

Kaduna
123456789

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ASD HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to ASD HAUSA:

Videos

Share