29/12/2024
Abinda ya faru yau a birnin Niamey na Jimhuriyyar Nijar inda masu zanga zanga s**a dinga ambatar sunan shugaban Najeriya suna aibata shi tare da yin zanen hotunansa suna munana shi su sani, wannan babban abin kunya ne da takaici, zagin Shugaba Tinubu a wajen 'yan Nijar su sani zagin dukkan 'yan Najeriya ne, domin a yanzu haka Bola Ahmed Tinubu shi je shugaban dukkan 'yan Najeriya.
Abinda s**a yi ya saɓa da ƙa'idar 'yan uwantaka da kuma mutuntaka dama maƙwabtaka. Ya k**ata mutanan Jimhuriyyar Nijar su sani saɓani ba aibu bane. Akwai wata ƙa"ida ta rayuwa da ta ke cewa:
“Zan iya faɗa da ɗan uwana, amma akansa zan iya faɗa da duniya”. Wannan shine taken ‘yan uwantaka. Sabani a tsakanin ‘yan uwa ɗabi’a ce da ɗan Adam ba ya iya guje mata, sai dai abin so shi ne kiyayewa da kuma ɗaukar matakin sassauta saɓanin domin wanzuwar ‘yan uwantaka.
Najeriya (musamman Arewa) da Jimhuriyyar Nijar ‘yan uwa ne da s**a haɗu a wasu abubuwa da yawa, k**a daga addini, al’ada, harshe, kasuwanci, kan iyaka, tarihi da zumuncin auratayya. A ɗabi’ance waɗannan sune abebaden da s**a fi haɗa kan bani-adama.
A ɗabi’ance, abu ne maimatuƙar wahala a ga ƙani ya fito duniya yana cin zarafin wansa saboda wani saɓani da ya shiga tsakaninsu, duk saɓanin da ba za a iya sulhunta shi a cikin gida ba, ba shakka babu amfanin fitowa da shi duniya a yayata shi matuƙar sulhu da fahimtar juna ake nema. Saboda haka, ba zai zo da mamaki ba idan makwabtan juna s**a samu sabani, sai dai babban abin nema a irin wannan hali shi ne, nuna dattako, sanin ya k**ata da hangen nesa domin akwai gobe.
Amma sam shugabannin mulkin sojan Nijar basu san haka ba, sun yi amfani da jahilcin mutanansu s**a ingazasu akan ƙiyayyar mutanan Najeriya, domin zagin shugaban Najeriya zagin baki ɗayan 'yan Najeriya ne. Allah yasa su gane.
Yasir Ramadan Gwale
28.12.2024