25/04/2024
GARGADI DA TUNATARWA...
Zan baka minti 5 kayi tunani acikin rayuwarka, kan waɗannan abubuwan da zan tambayeka harma ke Yar'uwa mai karatun nan, idan kasami amsa kabarshi acikin zuciyarka, idan ko baka samu amsa ba kayi gaggawar neman taimakon Allah da kokarin gyarawa.
1. Shin ka iya karatun Alkur'ani mai girma?
2. Shin kana Sallah da Addu'a?
3. Shin kana tunanin mutuwa?
4. Shin kana neman afuwa da Tuba ga Allah?
5. Shin kana cikin mutanen dake zagin mutane a bayan idonsu?
6. Shin kana adalci a tsakanin Diyanka da Matayen ka?
7. Shin kana wani aiki na alheri da kake aiwatarwa wanda kake da yakinin zaka samu Aljannah?
8. Shin sauran shekarunka da s**a wuce ina kakkarar da su?
9. Shin kana tunanin abinda kake ci Halal ne Ko Haram?
10. Shin kana sadar da Zumunta?
11. Shin kana umurta da kyakkyawa da Hani na Muni?
12. Shin kana tunanin zaman kabari kai ɗaya aciki, wane tana di kayyi na zamansa?
13. Shin kana taimakon bayin Allah musamman talakawa da Marayu?
14. Shin ya zamanka da makwabtan ka?
15. Shin kana biyawa zuciyarka wajen sabon Allah?
16. Shin kana zama da Mutanen kirki kayi mu'amala da su?
17. Shin kana hakuri da biyayya ga iyayenka?
18. Shin kana nisantar da kanka da abinda bai shafe ka ba? Wane irin sutura kake sanyawa, shin ya saɓama Shari'a?
19. Shin wane taimako kake yiwa addinin Musulunci? Shin ta hanyar ilimin ka ne, ko Dukiyar ka, ko jikinka, ko wace hanya kake taimakon Addini?
20. Shin lokacin da kassabama Allah shin zuciyarka na rauni, da Nadama ko kuma kana jin kanka da cewa kayi dai-dai?
Ɗan'uwa kayi tunani da nazari kan wannan tambayoyin, kayi kokari ka gyara domin mu tsira tare, Ina rokon Ubangiji ya maka Albarka da iyayen ka, Allah Ubangiji ya biya muna dukkan bukatun mu Duniya da lahira. Allah yasa mu mutu muna masu imani... 📝