11/04/2023
Amfanin Zogale Ga Fatar Dan Adam
Wani lokaci abubuwa masu girma s**anzo a karamar suffa, k**ar dai zogale, da ya kasance ƙananan ganye mai tarin albarka da kara lafiya. Kazalika ba kadai ganyen bane mai amfani, kowanne ɓangare na wannan tsiro, tun daga iri, furanni, tushensa, har ma da sassakensa, an san su wajen adana phytonutrients, amino acid, minerals, antioxidants, wanda ke taimakawa wajen rigakafin, kumburi, da rage yawan s**arin jini da matakan cholesterol.
Zogale na daga cikin abincin da ake ta’ammali da su sosai, ana yawan amfani dashi a matsayin wani bangare na girkin yau da kullum, a wasu lokutan ma akan busar da shi a mai dashi hoda domin barbadashi a girki don karin dandano.
Amma sai dai kash har yanzu mutane ba su gama gano amfanin wannan tsiro mai dinbin mamakiba. Wannan amfanin kuwa shine fitar da mai daga cikin ‘ya’yanta, wanda ke da ɗimbin amfani ga fata.
“Man zogale ko man ben, yana da hormones na shuka da ake kira cytokines waɗanda ke taimakawa girman cellular da kuma hana lalacewar tissues din fata," in ji masanin abinci mai gina jiki, kuma ƙwararre a ilimin aromatherapy Janice Rosenthal, wanda ya kirkiri Garden of Essences.
Ga kadan daga cikin amfanin wannan Mai na zogale a fatar mutum:
Vitamin C na man zogale yana ƙarfafa collagen, yana taimakawa wajen rage yamutsewar fata. Man zogale mai cike da bitamin da sinadirai masu yawa yana samar da ingantattun sinadaran kula da fata, godiya ga abubuwan da ya kunsa irin su antioxidants, antibacterial, da abubuwan gina jikin sa. “Ben oil” ya taimakawa man zogale wajen zama babban makami dan gujewa tsufan fata, kuma gashi da fa'ida ga gashin kan mutum.
Amfanin bai tsaya iya nan ba. Rosenthal ya kara da cewa, amfani da man da aka fitar daga zogale yana kuma taimakawa wajen kawar da kananan matsalolin fata k**ar su kurajen fuska da kuma rage duhun fata, kuma an san magungunansa da taimakawa wajen kauda kumburin ciki da waje.
Yanzu da kuka kara sanin amfanin wannan tsiro, lokaci ya yi da zaku ga fa'idodin zogale da kanku masu ban mamaki.
• Erno Laszlo, (Man Cleansing): Wannan man ba iya cire dattin fuska yake ba, yana kuma saka laushin fata da Hanata bushewa.
• HUM Nutrition Raw Beauty (Koriyar Hoda): Shan kofi daya na Wannan hoda na kawarda abubuwan dake lalata, kuzari, da haɓaka kyan fata har guda 39.
• Decleor Hydra Floral Anti-Pollution Hydrating Gel-Cream: Kare fata daga gurɓacewa, wannan gel-cream din wato man shafawa yana kauda bushewar fata.
Baya ga tarin sinadirai marasa iyaka, Shin kun san cewa zogale tushen bitamin A ne, wanda ke inganta lafiyar gani. Shin ko kun san cewa binciken kimiyya na baya-bayan nan yana ganin zogale a matsayin hanyar magance ciwon s**ari, kuma an tabbatar da cewa yana rage yawan glucose a cikin jini?
Shin kun san cewa daya daga cikin mafi kyawun fa'idodin zogale shine yana haɓaka ƙarfin garkuwar jiki?
Shin ko kun san cewa an gudanar da bincike da dama akan yuwuwar zogale ya kasance a matsayin maganin cutar daji?
A ƙarshe, ina ganin zogale yana daya daga cikin manyan tsirrai da amfaninsu bazai Taba misaltuwa ba. Ku Gwada ƙara shi a cikin abincin ku, ku kuma yarda da ganyen, don ganin abubuwan al'ajabi.