News Room Radio Jigawa

News Room Radio Jigawa News Production
(3)

24/02/2024

24-02-2024 GUMEL
Nine people were prosecuted by the Sanitation mobile court for violating Sanitation rules in Gumel local Government area.
The affected people were private and commercial owners, motorcyclists and tricycles.
Passing the Judgment, the mobile court Judge, Magistrate Mannir Sarki said they were to pay fine of between one thousand to five thousand Naira or serve two weeks imprisonment for the offences.
In his part , the State Sanitation Supervisor in the area, Murtala Bako appreciated the level of cleanliness at Model Boarding Primary school and Gumel Correctional centre.
However , he called on Lautai Boarding Science Secondary School to clean the bush within the School premises.
Murtala Bako then commended the council for the provision of enough Sanitation working materials.
Similarly, Sabon Layi Community development Association has donated fifty brooms to Gumel local Government.
Chairman of the Association Malam Idris Hashim Gumel said the aim is for the association to contribute towards a clean Gumel.
IO/MAG

24/02/2024

24-02-2024 GUMEL
Kotun tafi da gidanka kan tsaftar mahalli a karamar Hukumar Gumel ta hukunta mutane tara bisa lefin karya dokokin tsaftar mahalli
Wadanda kotun ta hukunta sun hadar da masu motoci na kansu da na haya da kuma masu Babura
Alkalin kotun , Majistare Mannir Sarki yace an ci tarar kowannensu naira dubu biyar-biyar ko kuma zaman gidan yari na tsawon makonni biyu
A wani labarin kuma kungiyar cigaban Unguwar Sabon Layi a garin Gumel ta bada gudunmawar tsintsiya bandir hamsin ga karamar hukumar Gumel
Shugaban kungiyar Malam Idris Hashim Gumel ya mika gudunmawar ga mukaddashin shugaban KH Haladu Musa Mele
A jawabinsa jamiin sa ido na aikin daga jiha, Murtala Bako ya ziyarci makarantar firamaren kwana ta Gumel da kuma gidan gyaran taribiyya inda ya yaba da yadda aikin ya gudana
Ya kuma shawarci mahukuntan sikandaren kimiyya ta Lautai dasu tabbatar da share ciyayin dake harabar makarantar

24/02/2024

24-02-2024 GONA
Shugaban kwamitin aikin gona na majalissar dokokin jihar Jigawa Alhaji Hassan Sheriff Kirya ya bukaci alumma dasu rungumi sana-ar noma domin wadata kasa da abinchi
Alhaji Hassan Sheriff ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci gonar Dan Makwayon Gumel Alhaji Muhammad Idris dake garin Gilima ta karamar hukumar Taura
Yace kwamiti da kuma gwamnati suna muna da kuma maraba da samun muhimman mutane irin su Hakimi suna yin noma domin bada misali ga na baya
Dan majalissar dake wakiltar karamar Hukumar Birniwa, yace zasu gayyato Gwamna Umar Namadi domin ganin irin wadannan gonaki domin sanya albarka da kuma baiwa mutane shaawar shiga shirin noma
A jawabinsa wakilin mai martaba sarkin Gumel kuma Majidadin Gumel Alhaji Murtala Aliyu yace akwai bukatar alumma su rungumi noma domin samar da abinchi ga jiha da kuma kasa baki daya
A jawabinsa tun da farko Dan Makwayon Gumel Muhammad Idris ya bukaci gwamnati data rinka samarwa da manoma taki da Irin shuka akan lokaci
Ya kuma baiwa gwamnati shawarar yin rangwamen kayayyakin noma domin baiwa manoma damar yin noma

24/02/2024

24-02-2024 BUJI
Karamar Hukumar Buji zata sayo kayayyakin tsaftar muhalli domin saukaka ayyukan masu shara a kowanne wata.
Shugaban karamar karamar Abdullahi Suleiman Yayari ya sanar da hakan ta hannun kansilan sashen ruwa da tsaftar muhalli Alhaji Isa Jata a lokacin aikin tsaftar muhalli na karshen wata
Ya kuma yaba da irin yadda kwamitin masu ruwa da tsaki akan tsaftar muhalli ya jajircewa wajen samun nasarar aikin tsaftar mahalli a yankin
Tunda farko shugaban sashen ruwa da tsaftar muhalli Alhaji Baffa Abdullahi Kudai yace KH ta na bada kulawa akan harkokin tsaftar muhalli da kuma kiwon lafiya
Ya kara da cewar KH ta gina asibiti a Garin Karanjau da Tudun Wada
Shima da yake duba aikin tsaftar muhalli, Jamiin kula da tsaftar muhalli na maaikatar kare muhalli ta jiha Alhaji Lurwanu Aminu ya yaba da yadda aikin ya gudana a gundumomin Yayari da Buji da kuma Gantsa.

24/02/2024

24-02-2024 SOJA
Wakilin mazabar Dutse a majalissar dokokin jihar Jigawa, Tasiu Ishaq Soja yace gwamna Mallam Umar Namadi ya amince da ware naira miliyan 30 daga cikin naira miliyan dari na aiyukan mazabu domin bunkasa tattalin arzikin alummar jihar nan
Tasiu Ishaq ya sanar da hakan ne ta cikin shirin Radio FM Andaza mai suna Jigawa a yau.
Yace gwamna Umar Namadi ya bullo da tsarin ne domin bada jari ga masu kananan sanaoi maza da mata domin rage radadin tsadar rayuwa
Dan majalisar yakara da cewar tuni ya gabatar da matsalolin zaizayar kasa dake damun garin Dutse ga gwamnati kuma tuni aka sanya kasafin kudin bana
Yace a aljihunsu ya gyara tuka tuka fiye da dari biyu yayinda a duk wata yake biyan kudin magani a asibitoci na kusan naira miliyan biyar da aljihunsu
Dan majalissar yana mai cewar ya gina gidajen marayu guda bakwai , yayinda ya aurar da marayu bakwai tare da yi musu kayan daki
Haka kuma yace yana da mararsa lafiya kusan 40 a kwance a asibitoci yake daukar nauyin bi ya musu kudaden magani
Tasiu Ishaq Soja ya kara da cewar karkashin aiyukan mazabu, an bada aikin gina makarantun Islamiyya da masalatai a mazabarsa daban daban
Ya bada tabbacin cigaba da zama wakilin mutanen Dutse na gari a majalissar tare da nemowa mutanen mazabarsa hakkokinsu a duk inda ya makale

23/02/2024

23-02-2023 KADUNA
Ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Jigawa tare da hadin gwiwar kamfanin kwararru na Anas Ibro International company sun gudanar da taron bita na yini uku ga shugabannin kananan hukumomi da shugabannin majalissun kamsiloli da Daraktoci da shugabannin sassan jin dadin jama-a da kuma Jamian Yada labarai na kananan hukumomi
Taron bitar mai taken nauyin da ya rataya akan shugabanni ga alumma an gudanar dashi ne a garin Kaduna.
Daya daga cikin mahalarta taron bitar kuma shugaban karamar hukumar Babura Alhaji Lawan Ismail yace sun kara samun ilmi kan yadda zasu gudanar da aiyukansu ga alumma
Yace taron bitar yana da muhimmanci ga shugabanni domin tallafawa alumma a bangarori daban daban domin samun zaman lafiya da kuma karuwar arziki
Shima da yake jawabi daraktan jin dadin jama-a na maaikatar kananan Hukumomi ta Jiha Muhammad Mukaddas yace wannan ba sabon abu bane a jihar Jigawa, kuma wannan taron bitar sake tunatar wa ce.
Muhammad Mukaddas yana mai cewar sun karu da abubuwa da zasu yi amfani dasu wajen taimakawa alumma.
Daga nan sai ya bada tabbacin isar da sakon da s**a samu a wajen bitar ga mahukunta

23/02/2024

23-02-2024 KADIRA
Hadejia Emirate Zakkat Committee has distributed zakat of farm Produce worth seven point four million naira to the needy at Kadira District in Guri local government area
Vice chairman of the committee and chief Imam of Hadejia Malam Yusuf Abdurrahman who presided over the distribution exercise, described Zakkat is one of the five pillars of Islam.
Farm produce distributed include 149 bags of Millet, 59 Bags of Rice and five hundred thousand naira cash.
Malam Yusud Abdurahaman advised wealthy in the society to give out zakkat as and when due.
On his part, the secretary of the committee Engineer Isma`ila Barde Hadejia said the alms was distributed to needy in line with Islamic injunction.
In his welcome address the District Head of Kadira, Alhaji Haruna Abbas commended Hadejia emirate Zakkat committee for its commitment towards the collection and distribution of Zakkat.
FMM/MAG/BS

23/02/2024

23/02/2024 CONDOLENCE
Kwamishinan ma`aikatar yada labarai na jiha, Alhaji Sagir Musa Ahmad ya bayyana rasuwar tsohon jami`in yada labarai na kananan hukumomin Guri da KiriKasamam Alhaji Sunusi A Doro da cewa babban rashin ne ga ma`aikatar yada labarai baki daya.
Kwamishinan wanda ya bayyana haka ne ta hannun daraktan yada labarai na ma`aikatar, Alhaji Isma`ila Yakubu, rasuwar ta girgiza ma`aikatan, inda ya bayyana marigayi Sunusi A. Doro a matsayin haziki ma`aikaci mai aiki tukuru.
Daga nan kwamishinan yayi addu`ar Allah ya jikansa da rahama ya kuma baiwa iyalai da yan`uwa hakurin hakurin jure rashin..
Hakazalika kungiyar yan`jaridu reshen ma`aikatar yada labarai ta jiha ta bayyana rasuwar Sunusi A. Doro da cewa babban rashin ne ga al`ummar musulmi baki daya.
Shugaban kungiyar comrade Muhammad Umar ne ya bayyana haka a sakon ta`aziyya mai dauke da sa hannun ma`ajin kungiyar Nasiru Yusuf Birnin kudu, yace za`a dade ana tunawa da irin gudunmawar da ya bayar a fannin yada labarai.
Daga nan yayi addu`ar Allah ya gafarta masa ya kuma baiwa iyalai da yan`uwa hakurin jure rashin.
Haka kuma kungiyar yan`jaridu reshen gidan rafiyo Jigawa ta mika makamanciyar wannan ta`aziyya ga iyalan marigayi.
Sakataren kungiyar Sani Muhammad Gumel wanda ya bayyana haka a sakon ta`aziyya, yayi addu`ar Allah ya jikan sa rahama.

23/02/2024

23-02-2024 KADIRA
An raba zakkar kayan amfanin gona da kudin su ya kai naira miliyan bakwai da bubu dari hudu ga mabukata a gundumar Hakimin Kadira dake yankin karamar hukumar Guri.
Kayayyakin da aka raba sun hadar da buhu 59 na shinkafa da kuma zunzurutun kudi naira dubu dari biyar.
Da yake kaddamar da rabon zakkar wakili a kwamatin zakka na masarautar Hadejia, Sheik Yusuf Abdulrahman ya bayyana zakka a matsayin daya daga cikin shika-shikakan addinin Musulunci biyar.
Yayi kira ga wanda Allah ya h**e wa dukiya su tabbatar da fidda zakka daga cikin dukiyoyin su.
A nasa jawabin sakataren kwamatin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde ya ce ana raba zakka ne ga mabukata kamar yadda Allah ya bada umarni.
Tun farko a jawabin sa na maraba, Hakimin Kadira Alh Haruna Abbas ya yabawa mai martab sarkin Hadejia bisa baiwa kwamatin zakka na masarautar damar kewayawa gundumomin hakimai domin raba zakka ga mabukata.

23/02/2024

23/02/2024 JNI/JG
Kungiyar Jama`atul Nasril Islam ta kasa reshen jihar Jigawa ta bukaci samun hadin kai da goyon bayan gidan Radiyo Jigawa wajen halartar taron lacca na azumin watan Ramadan da take shiryawa a kowace shekara.
Bukatar hakan na kunshe ne cikin takarda mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar na jiha, Malam Muhammad Ahmad Babangida.
Taron lacca da kungiyar ke gayyato malamai da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayyanawa al`ummar Musulmi falalar azumin watan Ramadan, da kuma muhimmancin hadin kai da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki da tsaro a tsakanin Musulmi.
Taron mai taken Tasirin Kafafen Yada Labarai ga harkokin addini da kyawawan al`adu a mahanga ta addini da kuma tsarin zamantakewa da tsaro da tattalin arzikin al`umma, wanda za`a gudanar a ranar 29 ga wannan watan a Sakatariyar kungiyar a kusa da gidan mai na B.A Bello dake kan hanyar zagaye a Unguwar Yalwawa a nan birnin Dutse da karfe hudu na yamma.
Daga nan sanarwar tayi fatan samun halartar wakilan kafafen yada labarai domin cimma burin da ake bukata.

22-02-2023                      NUT Kungiyar malaman makaranta ta kasa reshen jihar Jigawa ,  tace tana tattara bayanan ...
22/02/2024

22-02-2023 NUT
Kungiyar malaman makaranta ta kasa reshen jihar Jigawa , tace tana tattara bayanan malamai da kuma makarantun da ake dasu a kananan hukumomin jihar nan 27 domin sabunta bayanansu
Shugaban kungiyar, Comrade Abdulkadir Yunusa Jigawa ya sanar da hakan a lokacin ganawa da wakilinmu
Yace kungiyar ta bukaci rassanta na kananan hukumomi su aike mata da yawan malamai da yawan makarantun da suke kananan hukumomi domin ajiye bayanansu
Abdulkadir Yunusa Jigawa yana mai cewar tattara bayanan ya zama wajibi domin sabunta bayanan da suke dashi tun shekaru uku da s**a gabata
Ya musanta bullar wani jaddawalin yawan malamai da kuma makarantu da suke yawo a kafar sadarwa ta Zamani, yana mai cewar jaddawalin tsoho ne da suke da shi tun shekaru uku da s**a gabata
Shugaban kungiyar malaman na Jigawa ya bukaci malamai da su cigaba da jajircewa wajen koyar da dalibai domin cimma manufar gwamnati na bunkasa Ilmi a kowanne mataki
Ya kuma nuna gamsuwar kungiyar kan yadda aka gudanar da jarrabawar maida malaman shirin koyarwa na j-teach zuwa na dindindin a fadin jihar jigawa

22/02/2024

22-02-2024 B/KUDU
Kungiyar masu motocin sufuri ta kasa reshen karamar hukumar Birnin kudu ta gudanar da addu`o`i na musamman domin neman sauki dangane da halin da ake ciki na tsadar kayan abinci da sauran kayayyalom masarufi.
A jawabin da ya gabatar shugaban Alhaji Suleiman Jibrin yace sun shirya taron addu`ar a karo na farko domin neman sauki dangane da tsadar rayuwa da kuma tunawa da yan`kungiyar da s**a rasu.
Yace haka kuma sun gudanar da addu`o`in-neman zaman lafiya mai dorewa ga kasa da jihar Jigawa da kuma karamar hukumar Birnin kudu.
A nasa jawabin tsohon shugaban kungiyar, Malam Abdullahi Suleiman yayi kira ga sauran shugabannin kungiyar na jihar an suyi koyi da takwarorinsu na karamar hukumar Birnin kudu wajen shirya irin wannan taron.
A sakon da ya aike wajen taron addu`ar shugaban karamar hukumar Alhaji Magaji Yusuf wanda ya sami wakilcin makaddashin sakatare, Alhaji Ali Abdullahi ya yabawa kungiyar bisa hangen nesan su wajen shirya wannan taron.

22/02/2024

22-02-2024 GAGARAWA
Kwamitin lura da kananan hukumomi na majalisar wakilai ta tarayya ya bayyana karamar hukumar Gagarawa a matsayin daya daga kananan hukumomin da s**a yi fice wajen gudanar da ayyukan raya kasa.
Shugaban kwamitin Mista Kayode ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wakilan kwamitin s**a ziyarci karamar hukumar Gagarawa a cigaba da ziyarar duba ayyuka a wasu kananan hukumomin jihar nan.
Yace karamar hukumar tana sahun gaba wajen bin dokoki da ka`idojin aikin gwamnati.
A jawabin da ya gabatar mataimakin shugaban karamar hukumar Alhaji Auwalu Isah yace daga cikin ayyukan da s**a gudanar na baya-baya-nan sun hadar da gina rukunin ajujuwa guda biyar hade da ofishin malamai da kammala aikin samar da hasken lantarki a Gagarawa Tasha da masaukin masu yiwa kasa hidima da kuma aikin samar da hasken lantarki daga Gagarawa zuwa Madaka.
A lokacin ziyarar tawagar yan`majalisar wakilan na tare da jami`i daga ma`aikatar ayyuka da sufuri ta jiha, Malam Safiyanu Iliya, yayin da mataimakin shugaban karamar hukumar ke tare da sakataren karamar hukuamr Abba Saled da kuma daraktan tsare-tsare, Sadi Dan`malam.

22/02/2024

22-02-2024 K/HAUSA
Kungiyar zabi son-ka ta kasa reshen jihar Jigawa ta jaddada kudurinta na marawa kokarin gwamnatin jiha wajen inganta mahalli da kuma magance kwararowar Hamada.
Mataimakin shugaban kungiyar, Ahmadu Kafinta Bulangu shine ya bada wannan tabbaci a wata ganawa da wakilinmu.
Yace kungiyar zata reni dashen bishiyoyi dubu hudu da hamsin domin dasawa a wannan shekarar da nufin dakile kwararorwa Hamada da inganta mahalli.
Yace dasa bishiya tare da kula da su, na bada gudunmawa wajen yaki da kwararowar Hamada tare da bunkasa al`amuran aikin gona.
Malam Ahmadu Kafinta Bulangu yace kungiyar zata reni dashen bishiya guda dari da hamsin a kowace karamar hukumar domin dasawa a daminar bana.
Daga nan ya yabawa gwamnatin jida ma`aikatar kare mahalli da sauran masu ruwa da tsaki bisa kokarinsu na inganta alamuran mahalli a jihar nan.

22/02/2024

22-02-2024 HOUSE
Jigawa State House of Assembly Committee on Health has called on the state Ministry of Health to ensure that the contractors handling the construction of Garki General Hospital install medical equipment for the smooth take-off of full healthcare services in the hospital.
Chairman of the committee and member representing Guri Constituency, Honorable Usman Abdullahi Tura Musari, made the call during an oversight visit to the hospital.
He said the call become necessary in view of the huge investment made by the government in the hospital.
Honorable Usman Tura said the visit was meant to interact with hospital management to provide the necessary intervention needed to improve healthcare services in the state.
Earlier, the Medical Director Garki General Hospital Dr. Adamu Muhammad Dan-Aro explained that since its take-off, the hospital was not provided with running cost.
He said the hospital is also facing shortage of water, electricity supply, laboratory equipment, kitchen, ante-natal clinic, blood bank and store.
He called for government`s intervention to allow the hospital provide full services.
COV/IMBK/B

22/02/2024

22-02-2024 COMMITTEE
Jigawa State House of Assembly Committee on Health says it will meet with hospital managers, officials of Jigawa Pharmaceutical Company and Jigawa Contributory Health Management Agency to arrive at a uniform price list for drugs and medical consumables in the state.
Chairman of the committee, Honorable Usman Abdullahi Tura Musari, made this known when he led members of the committee on an oversight visit to Ringim General Hospital.
He said the measure became necessary to ensure the provision of healthcare services to patients benefitting from social security program and other patients across the state.
Honorable Usman Tura explained that the visit was meant to acquaint committee members the successes and challenges facing hospitals in order to provide solutions that will assist government to achieve its 12 Point Agenda.
Earlier, the Medical Director Ringim General Hospital Dr. Mahmud Abdullahi Sherif pointed out that differences in price and shortages in funding coupled with inflation are seriously affecting the conduct of DRF, JCHIMA and MCHN programs.
He also advised government to address the issues of power supply and procurement of diesel, casual workers and stationary for easy management of hospitals.
COV/IMBK/BS

22/02/2024

22-02-2024 MASTER PLAN
Jigawa state government has approved the re-structuring of Dutse master plan.
Special Adviser to the Governor on Dutse Capital Development Authority, Musa Sule Dutse made this known on a Radio FM Andaza program Jigawa a Yau
He said the gesture was aimed at giving the city a facelift to compete with its contemporaries.
The Special Adviser said DCDA will undertake the renovation of three major roundabouts in Dutse and Malam Aminu Kano triangle.
He added that the agency has planned to make Dutse the state capital a befitting status to compete with other cities in the country.
MAG/BS

22/02/2024

22/2/24. HOUSE/RGH
Kwamatin kula da harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce zai gana da likitoci da jami'an Kamfanin samar da magunguna na jihar Jigawa da kuma Shirin Adashen Gata na kiwon na jihar Jigawa domin cimma matsaya kan farashin magunguna na bai daya.
Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin s**a ziyarci Babban Asibitin Ringim.
Ya ce daukar wannan mataki ya zamo wajibi domin tabbatar da samar da ayyukan lafiya masu inganci ga masu karamin karfi a fadin jihar nan.
Alhaji Usman Tura ya ce kwamatin yana gudanar da irin wannan ziyara ce domin gano nasarori da kuma kalubalan da asibitoci ke fuskanta domin lalubo mafita da za ta taimakawa gwamnati wajen cimma kudurinta 12.
Tun da farko, Babban Likitan Asibitin Ringim Dr Mahmoud Abdullahi Sherif ya ce babnbancin farashin magunguna da karancin kudaden gudanarwa hadi da hauhawar farashi na kawo cikas ga shirye shiryen kiwon lafiya na sabeta juyeta da na adashen gata da kula da lafiyar mata da yara.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta duba batun Samar da wutar lantarki da sayen man gas da batun ma'aikatan wucin gadi da kayayyakin aiki na rubuce rubuce domin samun saukin gudanar da harkokin asibiti.

22/02/2024

22/2/24. HOUSE/GGH
Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma'aikatar lafiya ta jiha ta tabbatar da ganin cewa Dan kwangilar da ke gudanar da aikin Babban Asibitin Garki ya sanya kayayyakin aiki da na'urori domin asitibin ya gudanar ayyukan sa gadan gadan.
Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan kira lokacin da kwamatin ya ziyarci Asibitin.
Ya ce kiran ya zama wajibi bisa la'akari da dinbin kudaden da gwamnati ta zuba wajen aikin Asibitin tare da saukewa jama'ar yankin nauyin tura su zuwa asibitocin Gumel da Taura dan kula da lafiyar su.
Alhaji Usman Tura ya ce irin wannan ziyara na bawa kwamatin damar tattaunawa da shugabannin asibitoci dan sanin halin da suke ciki ta fuskar ayyukansu na yau da kullum domin duba inda kwamatin zai shiga tsakani dan inganta harkokin kiwon lafiya.
Tun da farko, Babban Likitan Asibitin Garki Dr. Adamu Muhammad Dan-Aro ya ce asibitin ba ya samun kudaden gudanarwa tun daga bude shi wadda hakan ke kawo cikas a ga ma'aikata.
Ya ce haka zalika babu ruwan sha da wutar lantarki da kayayyakin gwaje gwajen tukuka da dakin girki da na ajiyar kayayyaki da ma'ajiyar jini yayin da akwai wasu na'urorin da Dan kwangila bai sa ba dan aiki da su ga kuma karancin ma'aikata.

22/02/2024

22-02-2024 DCDA
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada umarnin sake fasalin taswirar birnin jiha Dutse domin ta dace da zamani
Mai baiwa gwamna shawara kan hukumar raya birnin jiha Dutse Musa Sule Dutse ya sanar da hakan ta cikin shirin Radio FM Andaza mai suna Jigawa a Yau.
Yace wasu hukumomi ne s**a bata taswirar birnin jiha Dutse , dan haka Gwamna Umar Namadi ya bada umarnin sake fasalin taswirar domin birnin ya dawo cikin hayacinsa
A cewarsa an bata taswirar birnin jiha, ta yadda mutane suke yin abubuwan da s**a ga dama wanda hakan ya bata gari ta fuskar kasuwanci da zamantakewa
Mallam Musa Sule Dutse ya cigaba da cewar Hukumar zata gyara shatale tale guda uku da ake birnin jiha Dutse da kuma filin taro na Mallam Aminu Kano domin kara kawata shi
Yana mai cewar akwai filin hukumar da aka kewaye a kusa da gidan gwamnati wanda shima za a samar da wurin shakatawa da kuma baiwa alumma damar yin kananan kasuwanci

21/02/2024

21-02-2024 HADEJIA
The Emir of Hadejia, Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje has turbaned two Village heads.
They are village head of Baraduwa in Sarawa District and village head of Marawa in Kwatalo District in Kafin hausa local government area
The Emir represented by Galadiman Hadejia , Alhaji Usman Abdul'aziz charged traditional rulers in his domain to put more eyes on new faces coming to their localities.
Dr Adamu Abubakar Maje stressed the need for the people to contribute in ensuring peace and stability
The Emir advised district heads to be fair and just in discharging their responsibilitie while urging people to cooperate.
In their remarks, the district heads of Sarawa, Dan Makwayo of Hadejia, Alhaji Aliyu Haruna and Kwatalo, Santuraki of Hadejia, Alhaji Abdulkadir Muhammad Maishahada called on people to engaged themselves in farming activities for job creation and food security.
In their vote of thanks the village heads of Baraduwa, Alhaji Yunusa Yusha'u and that of Marawa Alhaji Haruna Abdulhamid commended the emirate for given them the mandate and promised to justify the confidence reposed on them.
MUH/MAG

21/02/2024

21/02/2024 BIDDING
Gwamnatin jihar Jigawa ta bude tayin bada kwangilar sayen sabbin motoci 16 kirar Toyota Fortuner 2023 model.
Babban sakatare a ofishin gwamna , Alhaji Abdu Garba ya bude tayin bada kwangilar a gidan gwamnati
Yace sayen motocin na daga cikin kudirin gwamna Umar Namadi na samarda kyakkyawan yanayin aiki ga kwamishinoni domin cimma kudirorinsa 12
Alhaji Abdu Garba yana mai cewar za a bada kwangilar ne bisa tsarin doka
A jawabinsa Darakta Janar na hukumar tantance aiyukan kwangila ta jiha , Dr Alkassim Muhammad yace an bude ta yin bada kwangilar ne domin yin gasa a tsakanin kamfanoni kamar yadda yake kunshe a dokar hukumar mai lamba 13 ta 2019.
A jawabinsa a madadin yan kwangila wakilin kamfanin ALHAMSAD Nigeria Limited Alhaji Musbahu Abubakar ya bayyana tsarin tayin kwangilar da cewar ya dace matuka

21/02/2024

21/02/2024 BIDDING
Jigawa state government has opened bid for the procurement of sixteen number brand new Toyota Fortuner 2023 model.
Declaring the bidding open , the permanent secretary government house , Alhaji Abdu Garba said the procurement of the vehicles is in line with Governor Umar Namadi Administration’s resolve to create conducive working environment for the members ‘of the state executive council to achieve the administration 12 point agenda.
He said the bidding exercise is under the due process guidelines on award of contracts.
In his remark, the Director General, Due Process and Monitoring bureau Dr. Alkassim Muhammad explained that the contract is open and competitive due to the contract sum and also in compliance with the Jigawa State due Process law Number 13 of 2019.
Responding, on behalf of the bidders the representatives of ALHAMSAD Nigeria Limited Alhaji Musbahu Abubakar described the process as transparent.
NSB/MAG

21/02/2024

21-02-2024 BIRNIWA
Karamar hukumar Birniwa ta kaddamar da kwamitin amintattu na gidauniyar Waqaf da marayu da kuma masu rangwaman gata
A jawabinsa wajen bikin , shugaban masu rinjaye na majalissar kamsiloli Sani Nasir ya bukaci wakilan kwamitin dasu kasance masu tsoran Allah da gaskiya da kuma adalci wajen gudanar da aiyukansu
Ya bada tabbacin KH na ganin an yiwa gidauniyar rijista da hukumar yiwa kamfanoni rijista ta kasa tare da bude mata asusun ajiya na bankin
A jawabinsa a madadin hakiman yankin Uku, Hakimin Kazura- Dan Malikin Hadejia, Alhaji Ilyasu Habib ya yaba da daukar matakin kafa gidauniyar Waqafi domin tallafawa masu karamin karfi a yankin

21/02/2024

21-02-2024 POLIO
Kananan yara dubu sabain da takwas da dari hudu da ashirin da uku ne aka yiwa allurer rigakafin cutar shan Inna zagayen da ya gabata a kasar karamar Hukumar Kirikasamma
Kwararre mai kula da shirin a jiha Babangida Umar ya sanar da hakan a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan shirin rigakafi
Ya ce a 2023 sun fuskanci kalubale da dama musamman wajen yiwa makiyaya da kuma masu yin kaura rigakafi , dan haka a zagaye na gaba na rigakafin na watan gobe sun yi tanadi domin dakile wadannan kalubale
A nasa jawabin manajan hukumar lafiya matakin farko nayankin Musa Abdullahi Dala- Dige ya yaba da irin hadin kai da goyan bayan da KH da kuma sarakunan gargajiya ke baiwa shirin na rigakafi
Tun farko jamiin wayar da kai kan harkokin lafiya , Adamu Abdullahi yace sun kai ziyara fadojin hakimai da tashoshin mota da masalatai da sauran wuraren taruwar alumma domin wayar da kan alumma muhimmancin na rigakafi
A jawabinsa shugaban KH Kirikasamma Isa Adamu Matara ya yi alkawarin daukar nauyin tawagar da zata ziyarci wuraren zaman makiyaya da masu yin kaura a zagaye na biyu na rigakafin domin ganin an yiwa yayansu rigakafi

21/02/2024

21-02-2024 DUTSE
Shugaban karamar hukumar Dutse Mallam Bala Usman Chamo ya kaddamar da Hujjin dabbobi na bana a garin Fanisau dake mazabar karnaya
A jawabinsa wajen bikin, Mallam Bala Usman Chamo ya bukaci makiyaya dasu rungumi sabbin tsare tsare da gwamnati ta bullo dasu domin inganta lafiyar dabbobi
Ya shawarci makiyaya da manoma da su tabbatar sun kai dabbobinsu cibiyoyin rigakafin domin yiwa dabbobinsu
A nasa jawabin shugaban sashen aikin gona na yankin Muhammad Ashafa yace KH ta samar da Karin kwalaben rigakafin dabbobi akan wanda gwamnatin jiha ta bayar da kuma kwararrun malaman dabbobi domin samun nasarar hujin dabbobin
Shima da yake jawabi mai unguwar Fanisau Mallam Magaji Yusif ya bada tabbacin sanar da hukuma bullar duk wata bakuwar cutar dabbobi
A jawabinsa na godiya shugaban Miyetti Allah na yankin Alhaji Gari Gabari ya yabawa unguwar kungiyar ta jiha bisa jajircewarsu na ganin an gudanar da rigakafin na dabbobi

21/02/2024

21-02-2024 GUMEL
Karamar Hukumar Gumel ta bunkasa tattalin arzikin matasa maza da mata dari biyar a kwanaki dari da s**a gabata
Mai rikon kujerar shugaban karamar Hukumar, Alhaji Haladu Musa Mele ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa na musamman kan cikarsa kwanaki dari akan karagar mulki
Yace an baiwa matasa mata tallafin naira dubu goma zuwa ashirin domin bunkasa sanaarsu ta yin awara da kuma waina
Alhaji Haladu Musa ya karada cewar suma matasa maza an basu tallafin naira dubu ashirin zuwa hamsin domin yin kananan sanaoin dogaro da kai tare da alkawarin kara zakulo wasu matasan domin amfana da shirin
Yace karamar hukumar ta gina magudanan ruwa a sassa daban daban domin magance matsalar ambaliyar ruwa a cikin unguwar Nassarawa da kan Titin Hadejia da garin Danfarantama yayinda za a cigaba da aikin na garin Bekarya
Shugaban riko na karamar hukumar ta Gumel yace sun samar da naurar somo somo a tashar ruwa ta gard line da na unguwar Kuka hudu da na masalacin Duhuwa dana katta da kai da masalacin Dantanoma da Galagamma da Unguwar masalacin Yarabawa da gidan ruwa na garin Mele da na Dan Ama da nufin bunkasa harkar bada ruwansha ga alummomin yankunan
Yace KH ta gyara tashar bada ruwansha mai amfani da hasken rana dake yan kifi da kuma tashar ruwa ta makarantar Nasoro a garin Gumel, yayinda KH ta sayo kayayyakin gyaran fanfunan tuka tuka domin gyaran tuka tukan da s**a lalace. Haladu Musa Mele yace KH ta samar da Babura ga matasan da aka koyawa gyaran tuka tuka da za a kaddamar nan bada jimawa ba

21/02/2024

20 – 02 – 2024 Due Process
A cigaba da rangadin duba aiyuka a sassan jihar nan, mai baiwa gwamna shawara kan duba aiyuka, Alhaji Usman Haladu ya kai ziyarar duba aiyuka da gwamnatin jiha take aiwatar wa a sassan jihar nan
Aiyukan da ya duba, sun hadar da aikin gina gidaje a garuruwan Dutse da Birnin Kudu da kuma aikin gina gadar kan hanyar Madobi-Baranda-Birnin Kudu da ruwan sama ya lalata a bara
A garin Birnin Kudu Alhaji Usman Haladu ya bukaci dan kwangilar dake gina rukunin gidaje da ya kiyaye da dokokin aiyukan bada kwnagila da kuma yin aiki mai inganci
Ya yaba da kokarin gwamna Umar Namadi na gudanar da aiyukan raya kasa a sassan jihar nan
A lokacin ziyaar, yana tare da daraktan gine gine na hukumar tantance aiyukan kwangila Ahmad Isah da Enginneer Shuaibu Ali da kuma Engineer Ibrahim Muhammad

21/02/2024

21-02-2024 GARKI
Shugaban kungiyar ShugabannIn asibitoci na KH Garki, Nafi,u Sahibu Kore ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da tsarin tantance wadanda s**a yi karatun aikin lafiya kafin ta dauke su aiki.
Malam Nafi,u Sahibu Kore kuma shugaban asibitin Kore ya bayyana haka ne a wata ganawa da jami,in yada labarai na yankin, Ya,u be Garba Ringim.
Yace tantance Jami,an zai bada damar daukar ma,aikata na gari kuma masu sahihan takardun karatun aikin lafiya.
Daga nan yayi kira ga yan kungiyar da sauran ma,aikatan lafiya a yankin su kara himma wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda doka tayi tanadi.
Haka kuma Malam Nafi,u Sahibu Kore ya yabawa shugaban KH Garki Alhaji Mudassir Musa Garki da manajan hukumar lafiya matakin farko na yankin, Alhaji Alkassim Abubakar Doko saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta al,amuran kiwon lafiya a yankin.

Address

JRC
Dutse

Telephone

+2347037414765

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when News Room Radio Jigawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to News Room Radio Jigawa:

Videos

Share


Other News & Media Websites in Dutse

Show All