03/07/2023
Dakin Jinya Na Asibitocin Jigawa.
Na dan zagaya wasu daga cikin asibitocin jihar nan bisa radin kaina, daga cikin abinda nagani nakeso ayi gyara akai harda inganta dakin jinya na maza, mata da kananan yara . Inda nakeso naga anyi wannan gyara shine wajen bada hasken lantarki, fanka, da sauran su .
Sai kaje asibiti kaga marasa lafiya sun fito waje , sun cakudu a waje daya. Idan ka tambayesu sai s**e maka zafi ne da dakin ko wari ko makamantansu. Hakan kuma yana da illa a kimiyance, domin wanda yake da rashin lafiyar da zaa iya dauka ( infectious diseases) zai iya shafawa wani mara lafiyan ko kuma dan zaman jinya. Suma kansu maaikatan lafiyan idan sunje duba mara lafiya sai kaga mutum yana kokarin gamawa da wuri saboda yanayin da dakin ke ciki .
Bisa laakari da wannan da kuma yanayin tattalin arziki da muke ciki nake ganin kamar idan aka canja system na lightening din wannan dakuna zuwa solar powered Compact fluorescents, fan da sauran cooling system zai rage radadin kudin disel da ake fitarwa kuma baya gamsarwa . Akwai air conditioning system na india da suke amfani da ruwa, mai zai hana a kawo irin su a hada su da solar system, tinda suna da araha .
Aiwatar da hakan zai taimaka sossai, maaikaci zai samu condition na duba mara lafiya a nutse, zai kawar da fitar marasa lafiya waje domin neman iska, zai rage yaduwar cututtuka, kana zai rage yawan kudin da ake konawa wajen siyan man dizel.
Good Morning, Monday Tushen Aiki
-Dr.Hafiz Mukhtar Jahun