APN HAUSA

APN HAUSA AREWA PYRAMID NEWS HAUSA Arewa Pyramid News Hausa

Da Ɗumi-Ɗuminsa: Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci na sama da Naira bil...
09/03/2024

Da Ɗumi-Ɗuminsa: Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci na sama da Naira biliyan 2 ga mabuƙata domin ragewa al'umma radadi a watan Azumin Ramadan a fadin jihar Jigawa

Gwamnan ya raba buhunnan shinkafa dubu 150,000 sai buhun Masara guda dubu 150,000 da kwalin taliya dubu 150,000 domin sauƙaƙawa al'umma.

📸 -Kabiru Abdullahi Akwanga Reports

AlhamdullahAlhamdullahIna Maifarin ciki da Taya Dan uwan mu Kuma yayan mu Amb Hafeez Wakilin Amana Wanda MD ne na katafa...
03/03/2024

Alhamdullah
Alhamdullah

Ina Maifarin ciki da Taya Dan uwan mu Kuma yayan mu Amb Hafeez Wakilin Amana Wanda MD ne na katafare gidan Tv Mai albarka Mai suna Zamani tv domin nishadan tarwa da kuma fadakar wa kukasance da mu akoda yaushe

Sanna zaku iya Bada tallacen tallacen ku ako dayaushe

Ina Tayaka murna Allah yadafa maka yakuma Kara bukasa wanna Tasha Mai albarka

Sanna Ina Mai Bada hakuri na Rashi zuwa na wanna taro Mai tarin albarka
Ayi mun afwa Amb .....❤️🙏🥰🎁

Daga ....✍️
Amb idrees Hassan
Editor APN HAUSA reporters

YANZU-YANZU: Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bada cikiyar duk wanda ya ga waɗannan mutanen ko ya san inda za a same su y...
23/01/2024

YANZU-YANZU: Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bada cikiyar duk wanda ya ga waɗannan mutanen ko ya san inda za a same su ya gaggauta sanar da hukumar Hisbah cikin gaggawa.

1. Maiwushirya
2. Murja Kunya
3. Shakira
4. Hassan MakeUp
5. Kano State Material

Abdullahi Saleh Usman✍️

Zamu hukunta duk Limamin da aka samu da nuna bangarancin siyasa a cikin hudubar sa - Sarkin Gaya.Mai Martaba Sarkin Gaya...
23/01/2024

Zamu hukunta duk Limamin da aka samu da nuna bangarancin siyasa a cikin hudubar sa - Sarkin Gaya.

Mai Martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim ya sha alwashin hukunta duk Limamin da aka samu da nuna bangarancin siyasa akan Mumbarinsa.

Sarkin ya yi wannan gargadi ne, a yayin nadin sabon Limamin Juma'a na garin Aku dake karamar hukumar gaya, kamar yadda wata sanarwa da jami'in yada labaran fadar Auwalu Musa Yola ta tabbatar wa ATP hausa.

A yayin zaman Fadar na jiya Litinin, sarkin ya nada Dakta Aliyu Ibrahim a matsayin sabon limamin na Aku, da kuma Malam Yahuza Sulaiman a matsayin Na'ibinsa.

Dakta Aliyu Ibrahim ya kara da cewa Mumbarin huduba wuri ne, na fadin abinda Allah da Manzonsa s**ai umarni da ayi ko kar ayi, adan haka dole dukkan Limamin masarautar su bi kaidar, ko kuma su gamu da fushin masarautar.

Ya kuma jah hankalin dukkan Limamai, da su ci-gaba da fadakarwa domin samun hadin kan al'umma dama inganta zaman lafiyar yankunan Masarautar ta Gaya da jihar kano baki-daya.

A karshe sabon Limamin juma'ar na Garin Aku Malam Aminu Adamu, ya yi alkawarin bin dukkan umarnin ta Masarautar Gaya, domin kaucewa dukkan wani abu da zai iya janyo sabani a tsakanin al'umma.

YANZU YANZU Babbar Motar Dakon Siminti Mallakin Kamfanin BUA Ta Fadi Akan Gadar Kabuga Dake Karamar Hukumar Gwale Cikin ...
22/01/2024

YANZU YANZU
Babbar Motar Dakon Siminti Mallakin Kamfanin BUA Ta Fadi Akan Gadar Kabuga Dake Karamar Hukumar Gwale Cikin Birnin Kano, a Safiyar Yau Litinin.

Daga amb idrees hassan
Editor APN HAUSA REPORTERS

Shin zaku'iya zama a wanna Amastayin gidan ku kuwa Kubamu amsa a comment.........
16/01/2024

Shin zaku'iya zama a wanna
Amastayin gidan ku kuwa

Kubamu amsa a comment.........

Naji Daɗin Hukunci Da Kotun Ƙoli Ta Yanke Na Jaha Uku (3) Acikin Jahohi Takwas (8) A jiya Juma'a 12 ga watan Janairun, 2...
13/01/2024

Naji Daɗin Hukunci Da Kotun Ƙoli Ta Yanke Na Jaha Uku (3) Acikin Jahohi Takwas (8)

A jiya Juma'a 12 ga watan Janairun, 2024 kotun ƙoli {Supreme Court} ta yanke hukunci Gwamnonin jahohi guda takwasa (8) a Najeriya, bayan ta saurari a ƙarar raki a wasu makonni da s**a gabata, jahohi da hukunce_hukunce s**a shafa sun haɗar da na kudanci da na arewacin ƙasar kuma daga jam'iyyun siyasa daban_daban.

Amma zan ɗauki jahohi guda uku a arewacin Najeriya na ɗanyi tsokaci akansu, farko zan fara da jahar Kano tun da jahar kano babbar jaha ce a Najeriya ba arewa kaɗai ba, a jiya juma'a 12 ga watan janairun shekara ta 2024 kotun ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir Yusif na jam'iyyar NNPP a matsayin halastaccen gwamnan Kano, bayan ta saurari ƙara a wasu makonni da s**a gabata, haƙiƙa naji daɗi da kotun ƙoli ta tabbatarwa da Abba Kabir Yusif nasararsa a bisa wasu dalilai wanda zan lissafo a gaba.

Halau a jiyan dai kotun ƙoli ta yanke hukunci a jahar Zamfara da Bauchi, a jiya kotun ƙoli ta tabbatar da Dauda Lawal na Jam'iyyar P.D.P a matsayin Gwamnan Jahar Zamfara, bayan haka kotun ƙoli ta ayyana Bala Muhammad Ƙauran Bauchi na Jam'iyyar P.D.P a matsayin Gwamnan Jahar Bauchi haƙiƙa duka wannan hukunce_hukunce da kotun ƙoli ta zartar naji daɗi Ƙwarai dagaske.

Dalili na a nan shine duka waɗannan Gwamnoni da ƙotun ƙoli ta bawa nasara, dukkansu a jam'iyyun a dawa suke, kaga hakan na nufin kenan kotu ta shirya tsaf domin ƙwatowa kowa haƙƙinsa ko da kuwa a kowacce jam'iyya yake, sannan wannan hukunci da kotun ƙoli ta yanke, zai ƙarfafa gwiwar al'umma musamman matasa masu sha'awar siyasa nan gaba, sannan zai ƙara ƙarfafa gwiwar Al'umma akan ranar zaɓe su fito su zaɓi ra'ayinsu, su zaɓi wanda suke so, koda kuwa a kowacce jam'iyuar yake. A ƙarshe ina fatan waɗannan Gwamnoni da Allah Subhanahu wata'ala ya basu nasara, Allah yabasu ikon sauke nauyin da'aka ɗora musu, Allah yayi riƙo da hannayensu.

~Abdullahi Usaini Babai Garki
Asabar, 12 ga watan Janairun 2024

LABARINA: Ku Bayyana mana Ra'ayinku game da Shirin LABARINA na Wannan mako ?
05/01/2024

LABARINA: Ku Bayyana mana Ra'ayinku game da Shirin LABARINA na Wannan mako ?

Yanzu yanzu ......Kwamitin gudanar da Taron Nasarawa Facebook connectTashirya tsaf Kuma ta amince Da fara siyar da tikti...
21/12/2023

Yanzu yanzu ......

Kwamitin gudanar da Taron
Nasarawa Facebook connect
Tashirya tsaf Kuma ta amince
Da fara siyar da tiktin shiga taro
Akan farashi Mai sauki naira 500 kacal

Kuhanzarta domin kar abaku labari
Zaku'iya samun tikitinku tahanu adamu Hassan ,safiya Umar sai kunzu muna maraba daku ...

Daga
Amb idrees Hassan
Editor APN HAUSA

05/12/2023

Saqon sunusi lamido sunusi khalifan tijjaniyya na Nigeria akan abinda yafaru da 'yan uwanmu musulmi kan kis@nda akayi musu.

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN "Cikin baƙin ciki tareda sallama ma qaddarar Mahalicci muke ta'aziyyya ga 'yan uwanmu ...
05/12/2023

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN

"Cikin baƙin ciki tareda sallama ma qaddarar Mahalicci muke ta'aziyyya ga 'yan uwanmu akan waƙi'ar da ta faru a Tudun biri, sannan muna kira da babban murya ga gwamnati da hukuma akan a ɗauki mataki na gaggawa"

- Sayyida Rahmatullahi Niasse RTA

YANZU-YANZU: Hafsan Sojojin Kasa Na Najeriya, Lt. General Taoreed Lagbaja ya ziyarci kauyen Tudun Biri na Ƙaramar Hukuma...
05/12/2023

YANZU-YANZU: Hafsan Sojojin Kasa Na Najeriya, Lt. General Taoreed Lagbaja ya ziyarci kauyen Tudun Biri na Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna Domin Ta’aziya Da Jajantawa Al’umma Bisa Iftila’in Tashin Bom Da Yayi Sanadin Rasa Rayukan Al’umma A Garin.

INNÁ LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN:... Kungiyar Darikar Tijjaniyya Ta Fityanul Islam Initiative Ta Kasa Tana Allah Wada...
04/12/2023

INNÁ LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN:
... Kungiyar Darikar Tijjaniyya Ta Fityanul Islam Initiative Ta Kasa Tana Allah Wadai Da Abunda Rundunar Sojojin Kasan Najeriya Su Kayi.

A daren jiya lahadi ne 03/12/2023, Rundunar sojojin kasa na najeriya sun harbo Bom akan masu murnan Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ a garin Tudun/Biri dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 50.

Muna kira da babban murya ga gwamnatin jihar Kaduna da rundunar sojojin kasan najeriya dasu binciki wannan al'amari tare da biyan diyya wanda s**a rasa iyalan su baki daya.

Daga karshe muna kira da yan'uwa Musulmai dasu kwantar da hankalin su akan al'alamari.

Ubangiji madaukakin sarki ya jikan su da rahma ya gafarta masa, Allah ya karbi shahadar su. Amiiiin Yaa ALLAH

Daga: Babangida Alhaji Maina
Fityanu Initiative Media

Duk Wanda yaga Wani posting Na Wani Abu daga wanna shafin Idrees Hassan Wanda yashafi APC Koh PDP da suna Ina supporting...
23/11/2023

Duk Wanda yaga Wani posting
Na Wani Abu daga wanna shafin
Idrees Hassan Wanda yashafi APC Koh PDP da suna Ina supporting dinsu wlh karya ne sun hacking mun account ne

Disregard any post
That show you that am supporting PDP or APC am not the one hacker's
Aka bawa kwangila wanna aiki toh kunji kunya indai idrees ne yafi kar fin ku wlh

Mu bamayi komai na Dolle
Yauwa don haka indai nine wlh ku chanja salo akaina ta wanna Baku da sa'a

Daga ✍️
Am idrees Hassan

Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara Ya Tabbatar Da Nasarar Abba Gida-gida Ya Yi Ba Korar Sa Ba, Cewar Gwamnatin KanoKwamishinan ...
22/11/2023

Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara Ya Tabbatar Da Nasarar Abba Gida-gida Ya Yi Ba Korar Sa Ba, Cewar Gwamnatin Kano

Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na jihar Kano, Barista Haruna Dederi ya ce sun gano cewa ashe hukuncin Kotun Daukaka Ƙara tabbatar da nasarar zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ba korar sa ba.

A wani taron manema labarai a jiya Talata, Dederi ya ce hukuncin, gwamna Abba ya ce a baiwa Naira miliyan daya kuɗin tara ba wai shi ya bayar ba

Ya ce gwamnatin Kano ta gano cewa bayanin da su ke cikin kundin hukuncin ya saba da sanarwar da alkalami kotun daukaka kara s**a yi a ranar Juma’a da ke tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.

Sai dai kuma Dederi ya ce sahihin kwafin na hukuncin kotun daukaka kara ya nuna cewa kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun ta ƙasa ta yanke.

Dederi, wanda ya nuna mamaki da takaici a kan lamarin, ya ce za su rike wannan a matsayin shaida da za su kai korafinsu zuwa kotun koli.

CIKIN HOTUNA: Ku kalli yadda aka ƙawata sabon shatale-talen da ke ƙofar gidan gwamnatin jihar Kano wanda ake jiran buɗew...
21/11/2023

CIKIN HOTUNA: Ku kalli yadda aka ƙawata sabon shatale-talen da ke ƙofar gidan gwamnatin jihar Kano wanda ake jiran buɗewa kwanan nan.

Me za ku ce?.

YANZU-YANZU: Zan tabbatar jihar Zamfara ta zama ta ɗay a ɓangaren harkar ilimi a Najeriya". In ji gwamna Dauda Lawal na ...
21/11/2023

YANZU-YANZU: Zan tabbatar jihar Zamfara ta zama ta ɗay a ɓangaren harkar ilimi a Najeriya". In ji gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Wane fata kuke masa?.

An yi jana'izar Daraktan Finafinan Hausa marigayi Aminu S. Bono a gidansu da ke unguwar Dandago a birnin Kano.Allah ya g...
21/11/2023

An yi jana'izar Daraktan Finafinan Hausa marigayi Aminu S. Bono a gidansu da ke unguwar Dandago a birnin Kano.

Allah ya gafarta masa Amin.

20/11/2023
20/11/2023
In Dai Saboda Muna Yiwa Wannan Bawan Allahn (Kwankwaso) Biyayya Ne Yasa a Duniya Za'a Hanamu Wani Abu To Aje Allah Ya Ra...
20/11/2023

In Dai Saboda Muna Yiwa Wannan Bawan Allahn (Kwankwaso) Biyayya Ne Yasa a Duniya Za'a Hanamu Wani Abu To Aje Allah Ya Raka Taki Gona.

~ HE Abba Kabir Yusuf.

"Duk wanda ke murna saboda zalunci ya yi masa rana, to wata rana sai ya yi kukan neman adalci ya rasa". In ji ɗan jarida...
20/11/2023

"Duk wanda ke murna saboda zalunci ya yi masa rana, to wata rana sai ya yi kukan neman adalci ya rasa". In ji ɗan jarida Jaafar Jaafar.

Munayiwa ma'abota bibiyar shafin APN HAUSA Albashir cewa tashar zata dawo aiki sosai, tare da kawo muku labaran ilimanta...
19/11/2023

Munayiwa ma'abota bibiyar shafin APN HAUSA Albashir cewa tashar zata dawo aiki sosai, tare da kawo muku labaran ilimantarwa, faɗakarwa, da nishaɗantarwa.

Wazai bawa Allah rance 📍📍Yahaya Ibrahim KanteDalibine dake jami’ar ilimin kimiyya da Fasaha dake nan Hagar Bauchi wato A...
15/11/2023

Wazai bawa Allah rance 📍📍
Yahaya Ibrahim Kante
Dalibine dake jami’ar ilimin kimiyya da Fasaha dake nan Hagar Bauchi wato ATBU Bauchi
Mutum ne kamar kowa kuma duk duniya Babu Wanda Yafi karfin Jarabawa, shekara 2 kenan Kante Yana Ajiye karatunsa Saboda Larura ta karaya da ya samu saka makon Hatsari Da Yayi Na Mashin.

Akwai yiwuwar abu biyu Zai iya faruwa dashi idan ba’a yi aikin kafar nanba ko ta lalace kuma yabar karatunsa.

Y’an Uwa da Abokan Arziki muyi yin kuri don ceto shi daga wannan jarabawar, mai taro da Sisi, Allah Ya Bamu Iko Ameen Ya Allah

Account details
Account Number:5747216010
Account name:Yahaya Ibrahim
Bank :FCMB
Phone number:08065531144

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Umarci A Liƙawa Rarara Takardun Sammaci A Dukkan Gidajensa Dake A faɗin Najeriya Babbar Kotun Majis...
13/11/2023

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Umarci A Liƙawa Rarara Takardun Sammaci A Dukkan Gidajensa Dake A faɗin Najeriya

Babbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke Lafia, a jihar Nasarawa, ta umarci a liƙawa Fitaccen Mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara, takardar sammacin kiran Kotun, a dukkannin gidajensa, da ke faɗin Najeriya.

Kotun ta bada wannan umarni ne, sakamakon gaza samunsa fuska-fuska domin miƙa masa takardar sammacin da Kotun ta aike masa, kan ƙarar da Fitaccen Ɗan Jaridar nan (Mamallakin Jaridar Rariya Online), Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya shigar da shi a gabanta, ya na neman Kotun ta sanya a tsare shi, bisa wasu kalamai da ya furta da Alhaji Sani Zanginan ke musu kallon kalaman tunzuri.

Lauyan mai ƙara, Barista M.A Barde, shi ne ya tabbatar da wannan umarni da Kotun ta bayar, ya yin da ya ke zantawa da Manema Labarai, jim kaɗan bayan fitowa daga zaman Kotun, a yau (Litinin).

Kotun ta kuma sanya, ranar 4 ga watan gobe na Disamba, a matsayin ranar komawa Kotun, domin cigaba da sauraron shari’ar.

Sai dai, a wata tattaunawar wayar tarho da Jaridar ATP Hausa ta yi da Mawaƙin, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya bayyana cewar, takardar Kotu bata riske shi ba. Amma zai sanar da Lauyansa, domin ya bincika.

Idan za a iya tunawa, Mawaƙi Rarara, ya furta wasu kalamai da ake ganin cin zarafi ne, ga muhibbar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a ya yin wani taron Manema Labarai da ya gudanar, a jihar Kano, tun a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata. Inda me ƙara (Sani Ahmad Zangina) ya kasance daga jerin mutanen da ke kallon kalaman na Rarara a matsayin kalaman tunzura al’umma. APN Hausa reports

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamna a Kogi da Bayelsa bayan jam'yyar APC ta lashe zaɓen na jihar Imo.
12/11/2023

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamna a Kogi da Bayelsa bayan jam'yyar APC ta lashe zaɓen na jihar Imo.

Gwamnan wanda ya samu wa’adi na biyu a kan karagar mulki ya cinye dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar.Comr idrees hassan...
12/11/2023

Gwamnan wanda ya samu wa’adi na biyu a kan karagar mulki ya cinye dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Comr idrees hassan
APN HAUSA reporters

Kukarasa mana Karin maganar na Ina amfani kyau........
08/11/2023

Kukarasa mana Karin maganar na

Ina amfani kyau........

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta ta gina sabbin gadojin sama biyu a shatale-shatelen Tal'udu da na Dan Ag...
05/11/2023

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta ta gina sabbin gadojin sama biyu a shatale-shatelen Tal'udu da na Dan Agundi da ke kwaryar Birnin Kano. Me zaku ce? APN Hausa kabiru Abdullahi Akwanga

Address

Dutse LGA
Dutse
222

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when APN HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to APN HAUSA:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Dutse

Show All