Labari Daga Bauchi

Labari Daga Bauchi Media News

Ko kunji Labari abinda kamfanin tace mai na Dangote ya fara domin kawo sauki a Nijeriya?๐Ÿ‘‡
08/12/2023

Ko kunji Labari abinda kamfanin tace mai na Dangote ya fara domin kawo sauki a Nijeriya?

๐Ÿ‘‡

Sanarwar ta ce matatar man fetur ta Dangote ta sayi gangar ษ—anyen mai miliyan ษ—aya daga wasu manyan kamfanonin haฦ™o

YA'YAN SHEKH DAHIRU USMAN BAUCHI SUN ZIYARCI GARIN TUDUN BIRI YANDA AKA KAI HARI GA MASU TARON MAULAUD._______________โ€˜Y...
08/12/2023

YA'YAN SHEKH DAHIRU USMAN BAUCHI SUN ZIYARCI GARIN TUDUN BIRI YANDA AKA KAI HARI GA MASU TARON MAULAUD.
_______________

โ€˜Yaโ€™yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun kai ziyarar ta'aziya ga al'ummar Tudun Biri a Kaduna, inda wani jirgi maras matuki ya kai harin bam kan taron masu Mauludi a makon da ya gabata. Yanda mutane sama da dari s**a rasu!

Almajiran Sheikh Shekh Dahiru Usman Bauchi na cikin mutanen da harin bam ษ—in ya ritsa da su a makarantar islamiyyar da ke ฦ™arฦ™ashin kulawar babban malamin. A Garin na Tudun biri.

Fadar shugaban kasa ta musa batun rufe bankunan yanar gizo---------------Mai taimakawa Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu y...
08/12/2023

Fadar shugaban kasa ta musa batun rufe bankunan yanar gizo
---------------

Mai taimakawa Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi karin haske kan wani rahoton da aka yada na cewar CBN na shirin rufe Opay, PalmPay, Moniepoint da sauran bankunan yanar gizo.

A cewar hadimin na shugaba Tunubu Dada Olusegun, rahoton da aka yada ษ—in na kanzon kurege ne tare da yin kira ga jama'a da su rinka yin bincike kafin yada jita-jitar da bata da tushe b***e mak**a.

CIKIYA.........!!!Allah ka Bayyana IHSAN.Asiya da ake kira Ihsan ta fita cikin gida a unguwar federal Lowcost Bauchi.A s...
08/12/2023

CIKIYA.........!!!

Allah ka Bayyana IHSAN.
Asiya da ake kira Ihsan ta fita cikin gida a unguwar federal Lowcost Bauchi.
A safiyar yau. Misalin karfe
9:30

An bincika duk yanda ake tsammanin ganin ta Allah bai nufa an ganta ba.

Dan girman Allah wanda Allah ya nufa da ganin ta yana iya Kiran mahaifin ta
Malam. Mukthar Shuaibu.

Call - :
07034838385.
08067851979

Allah ya bayyana ta.

Ministan Lafiya Da Walwala Farfesa Muhammad Ali Pate Ya Gana Da Jakadar Kasar Netherlands Domin Inganta Harkokin Lafiya ...
08/12/2023

Ministan Lafiya Da Walwala Farfesa Muhammad Ali Pate Ya Gana Da Jakadar Kasar Netherlands Domin Inganta Harkokin Lafiya A Nijeriya

Ministan lafiya da walwala, farfesa Muhammad Ali Pate, ya gana da jakadar ฦ˜asar Netherlands Mista Wouter Plomp domin gina kyakkyawar alaฦ™ar da zai fidda natijar inganta harkokin kiwon lafiya a Nijeriya.

A ya yin ganawar, farfesa Pate da Mista Wouter sun tattauna akan batun samar da hanyoyin hadin gwiwa tsakanin ฦ™asashen biyu, wanda hakan zai taimaka wajen bunฦ™asa tare da inganta harkokin kiwon lafiya a Nijeriya. Farfesa Muhammad Ali Pate ya bayyana cewar, tattaunawar ya ฦ™unshi zurfafa hadin gwuiwa a tsakanin kasashen biyu domin inganta tsarin jinya, sarrafa magunguna tare da inganta baiwa mata masu juna biyu kulawa. Muhammad Ali Pate ya ce:

"Gina alaฦ™a domin cimma nasarar shirin maaikatan lafiya na Buษ—e ฦ™ofar da Masana'antun kiwon lafiya za su cigaba da zamowa abu mai muhimmanci a kokarinmu na takaita irin kalubalen da al'umma ke fuskanta a wajen neman lafiya."

Daga karshe, Muhammad Ali Pate ya isar da sakon godiyarsa wa gwamnatin kasar Netherlands a bisa ga ฦ™oฦ™arinta na inganta harkokin lafiya ta hanyar shirin "Kasuwanci da Taimako" wanda hakan ya taimaka wa kokarinmu na bunkasa binciken kiwon lafiya tare da sarrafa kayayyakin jinya, musamman jinyar cutur sankara da sauran cututtuka marassa yaduwa.

Pate Media Center

Gagarimin taron waliman yaye Dalibai da Mauludin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (s.a.w)------------------Jagoran maka...
08/12/2023

Gagarimin taron waliman yaye Dalibai da Mauludin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (s.a.w)
------------------

Jagoran makarantar TAHFIZUL QUR'AN Sheikh Samaila Bajoga na farin cikin gayyatan al'umman Annabi Muhammadu (s.a.w) zuwa taron yaye Dalibai da Maulud.

YAYE DALIBAI
Ranar Assabar 9/12/2023 da misalin karfe 9 na safe.

MAULUD
Ranar Assabar 9/12/2023 da misalin karfe 9 na dare.

WAJEN TARON
Harabar makarantar dake Unguwar tudun Salmanu nan cikin garin Bauchi.

Allah ya bada ikon halarta.

๐‘ช๐‘ฐ๐‘ฎ๐‘จ๐‘น๐‘ฐ ๐‘ช๐‘ฏ๐‘จ๐‘น๐‘ฐ๐‘ป๐’€ ๐‘ถ๐‘น๐‘ฎ๐‘จ๐‘ต๐‘ฐ๐‘บ๐‘จ๐‘ป๐‘ฐ๐‘ถ๐‘ต.Wannan cibiya mai aikin taimako wato Cigari charity organization ta Kai ziyara a subitin mak...
08/12/2023

๐‘ช๐‘ฐ๐‘ฎ๐‘จ๐‘น๐‘ฐ ๐‘ช๐‘ฏ๐‘จ๐‘น๐‘ฐ๐‘ป๐’€ ๐‘ถ๐‘น๐‘ฎ๐‘จ๐‘ต๐‘ฐ๐‘บ๐‘จ๐‘ป๐‘ฐ๐‘ถ๐‘ต.

Wannan cibiya mai aikin taimako wato Cigari charity organization ta Kai ziyara a subitin makara huta PHC dake Karamar Hukumar misau jihar Bauchi.

Cibiyar ta Cigari charity organization tabada tallafin magani wa mata masu ciki da kuma kayan ai huwa (delivery items) wa mata 150 kyauta a asibitin makara huta PHC misau

Minister lafiya prop. Muhummad Ali pate yasamu wakilcin Mai tallafamasa a yankin arewa maso gabas Alh Basko mangari sarkin samarin misau. Mai martaba sarkin misau Alh Ahmad S**aiman shima yayi fatan Alheri ma cigari charity organization da Addu'ar karfafa musu gwiwa

Alhamdulillahi.Bayan cikiya da muka yi An samu AFNAN cikin aminci kuma an kira Iyayen ta sun karbe ta. Allah ya kiyaye n...
07/12/2023

Alhamdulillahi.

Bayan cikiya da muka yi An samu AFNAN cikin aminci kuma an kira Iyayen ta sun karbe ta. Allah ya kiyaye na gaba.

๐Œ๐€๐ƒ๐€๐‘๐€๐’๐€๐“๐”๐‹ ๐๐”๐‘๐”๐‹ ๐๐€๐˜๐€๐ ๐ƒ๐€๐’๐’ ๐๐€๐”๐‚๐‡๐ˆ.Tana farin cikin Gayyatar ku zuwa wurin taron addu'a saukar karatu karo na 4 tare da...
07/12/2023

๐Œ๐€๐ƒ๐€๐‘๐€๐’๐€๐“๐”๐‹ ๐๐”๐‘๐”๐‹ ๐๐€๐˜๐€๐ ๐ƒ๐€๐’๐’ ๐๐€๐”๐‚๐‡๐ˆ.
Tana farin cikin Gayyatar ku zuwa wurin taron addu'a saukar karatu karo na 4 tare da Gidauniyar miliyan 30 don aikin gina makaranta.
__________

๐Œ๐€๐ƒ๐€๐‘๐€๐’๐€๐“๐”๐‹ ๐๐”๐‘๐”๐‹ ๐๐€๐˜๐€๐ ๐ƒ๐€๐’๐’ ๐๐€๐”๐‚๐‡๐ˆ. Dake unguwar Nasarawa kan tudu karamar hukumar Dass jihar Bauchi. Tana farin cikin Gayyatar ku don Bikin yaye Dalibai Mutane 40 tare kuma da Gidauniyar tara nai miliyan 30 Domin kammala aikin ginin makarantar tasu dake Dass.

Za'a gudanar da taron ranar 10/12 /2023
Lokaci - : karfe 8:00 am.
Harabar ma'aikatan Gona na karamar hukumar Dass
(BSDP)

Uban Taro mai Martaba Sarkin Dass Alhaji Dr Othman Bilyaminu Othman

Babban Ba ko na musamman Sanata Shehu Buba Umar. Mai wakiltar shiyyar Bauchi ta kudu.

Uwar gidan Gwamnan jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Abdulkadir Muhammad kauran Bauchi.

Sanarwa Daga shugaban makaranta shugaba Mal bilyaminu Hassan. Allah ya bada ikon halarta Amin.

Matasan Gidan KomishinaKananan hukumomin jihar Bauchi Hon Ahmad Aliyu Jalam sun samu tallafi_________A yau ne shugaban m...
07/12/2023

Matasan Gidan Komishina
Kananan hukumomin jihar Bauchi Hon Ahmad Aliyu Jalam sun samu tallafi
_________

A yau ne shugaban matasa Gidan Komishinan kananan hukumomi da masarautu gargajiya jihar Bauchi Hon Ahmad Aliyu Jalam. Malam Manniru Abdullahi 2Number ya tara masatasa dan tallafa masu k**ar yanda ya saba.

Matasan sun kasance masu tallafa masa ko wani Lokaci kan lamuran da s**a shafi siyasa da ayyukan yau da kullum.

FANNIN ILIMI:Cikin ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi take ci gaba da gudanarwa karkashin ma'aikatar CSDA------------A Ga...
07/12/2023

FANNIN ILIMI:
Cikin ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi take ci gaba da gudanarwa karkashin ma'aikatar CSDA
------------

A Garin GYARA karamar hukumar BOGORO shiyar Bauchi ta kudu hoton farko na makarantar da aka taras da ita ce, cikin mawuyacin hali. Hoto na biyu aikin da yanzu haka ake ci gaba da yi na gyaran ta.

Sabon Garin Sara a karamar hukumar Giade a shiyyar Bauchi ta Arewa. Aikin ajujuwa uku ne aka yi a karkashin ma'aikatar CSDA.

A Garin Tudun wada karamar hukumar Warji shiyar Bauchi ta tsakiya an kammala aikin gina sabuwar makaranta ga Alumman wannan gari karkashin ma'aikatar CSDA

07/12/2023

Daga bakin al'umman garin PANDUM karamar hukumar Darazo a shiyar Bauchi ta tsakiya kan sabon asibitin da Gwamnan jihar Bauchi ya gina musu karkashin ma'aikatar CSDA

CIKIYA.......!!!Cike da jimami Iyayen AFNAN suna cikiyar ta yarinya ce yar shekara 5Ta fita a gida tun Jiya da safe a un...
07/12/2023

CIKIYA.......!!!

Cike da jimami Iyayen AFNAN suna cikiyar ta yarinya ce yar shekara 5

Ta fita a gida tun Jiya da safe a unguwar Dawaki har yanzu ba'a same taba anje duk yanda ake tsammanin ta babu Labarin ta.

Duk Wanda Allah ya nufa da ganin ta ya taimaka ya kira 08054109668

Allah yasa a dace!!

07/12/2023

KAI TSAYE..

Yanzu haka shugaban matasa Gidan Komishinan kananan hukumomi jihar Bauchi Malam Manniru Abdullahi 2Number ya tara masatasa dan tallafa masu kaunar yanda ya saba.

07/12/2023

Cikin tarin ayyukan da Gwamnan jihar Bauchi ke ci gaba da aiwatarwa a fannin LAFIYA ILIMI DA RUWAN SHA karkashin ma'aikatar CSDA a fadin shiyoyi uku na jihar Bauchi.
-----------

Al'umman Unguwar GANJUWA a karamar hukumar Bauchi sun miฦ™a godiyar musamman ga Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi.

Cikin hotuna wasu kadan daga cikin ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi ke ci gaba da aiwatarwa a Kauyuka da karkara a fadi...
07/12/2023

Cikin hotuna wasu kadan daga cikin ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi ke ci gaba da aiwatarwa a Kauyuka da karkara a fadin shiyoyi uku na jihar Bauchi karkashin ma'aikatar CSDA
--------

GARIN JAR KASA A KARAMAR HUKUMAR MISAU SHIYAR BAUCHI TA TSAKIYA
Yanzu haka ana aikin fadada asibitin garin don samar musu da sashin karษ“ar haihuwa, karkashin ma'aikatar CSDA

GARIN GANDI A KARAMAR HUKUMAR TORO SHIYYAR BAUCHI TA KUDU
Bayan samar da fili fallau a yanzu haka gwamnatin jihar Bauchi karkashin ma'aikatar CSDA tana kan aikin gina musu sabon asibiti

GARIN JADORI KARAMAR HUKUMAR GAMAWA A SHIYAR BAUCHI TA AREWA
Yanzu haka suma gwamnatin jihar Bauchi karkashin ma'aikatar CSDA tana kan aikin fadada asibitin garin don samar da sashin karษ“ar haihuwa.

AIKIN ALHERI YAKE YI.....Bashi ya nemi a rubuta baKawai wanda yayi musu neS**a fadi domin wasu suyi koyi._________Ba'a r...
06/12/2023

AIKIN ALHERI YAKE YI.....
Bashi ya nemi a rubuta ba
Kawai wanda yayi musu ne
S**a fadi domin wasu suyi koyi.
_________

Ba'a raina aikin Alheri kuma ba sai masu kudi ba ne ke iya aikin Alheri.

Hassan Nagabale Gamawa. Matashi ne mai Karamin karfi dake aikin
Gadi kuma ake biyan sa Karamin kudin da bai wuce 10k ba. Sai dai Allah yasa masa zuciyar taimako kuma ya iya sana'ar hannu
Sai yayi amfani da dan abinda ke hanun sa yana Sayen abun gyara Famfo yana bi yana gyarawa cikin Unguwanni. Haka jama'a s**a ta neman sa yana gyara musu ba tare da ya karbi ko CC ba a karamar hukumar Gamawa jihar Bauchi.

Yanzu haka ya samu Nasara gyara famfuna masu yawa kyauta kuma al'umma na tayi masa son barka.

Cikin Unguwani da ya gyara sun hada da - :

(1)Anguwar Sarkin Noma Gamawa(2)Anguwar Gara Gamawa(3)Anguwar Abuja Gamawa(4)Anguwar Ibrahim Ibrahim Gamawa(5)Anguwar Kotu Gamawa(6)Anguwar Chadi Gamawa(7)Babban Massallacin Juma'a Gamawa.(8)Day Primary School Gamawa(9)Famfun Gololo Road Gamawa(10)Anguwar KyarkyarUdubo(11)
Anguwar Gabar Udubo(12)Anguwar Borehole Gamawa.

Allah ya saka masa da Alheri.

KYAN ALKAWRI.... Shugaban riko na karamar hukumar kirfi ya cika Alkawrin da yayi na sayen sabon Transformer (Injin wuta)...
06/12/2023

KYAN ALKAWRI....
Shugaban riko na karamar hukumar kirfi ya cika Alkawrin da yayi na sayen sabon Transformer (Injin wuta)
_________

Yau Laraba 6/12/2023 Maigirma Shugaban Riฦ™o na ฦ˜aramar hukumar Hon Abdulqadeer Umar Dewu (Madugun ฦ˜asar Kirfi) ya cika alkawarinsa na sayan SABUWAR TRANSFORMER wa al'umman unguwar Katsinawa agarin Bara dake ฦ˜aramar hukumar Kirfi Kamar yanda yayi musu alkawari.

Alummar da s**a amfana Sunyi murna, sunyi godiya tare da addu'an Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya biya maka buฦ™atunka na duniya da lahira.

Umar Waziri Bara
(Sarkin Samarin Bara).
6th Dec, 2023.

An roki Gwamnan jihar Bauchi ya Kara dubi kan Ayyukan hanyoyi km 200Da za'ayi.Tsohon Komishinan kananan hukumomi na jiha...
06/12/2023

An roki Gwamnan jihar Bauchi ya Kara dubi kan Ayyukan hanyoyi km 200
Da za'ayi.

Tsohon Komishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Hon Ismail Muhammad Isah Wakilin tsafi.

Muna Rokon mai girma Gwamna ya duba aikin hanyar shiyyar Bauchi ta Arewa Ayyukan hanyar da aka bayar yayi kadan in anyi La'akari da aikin da aka bayar a shiyyar Bauchi ta kudu da Bauchi ta tsakiya.


๐Ÿ‘‡
https://fb.watch/oK1wojjIcN/?mibextid=Nif5oz

06/12/2023

The family of Comr. Ilyasu Ibrahim Zwall cordially invites you to honor the presence of the Wedding Fatiha of his Daughter, Dr. Fatima Ilyasu Ibrahim Zwall (Wahida).

Which will take place as follows:

Date: Sat. 9th December, 2023
Time: 11:00am
Venue: Ibrahim Bako Juma'at Mosque Bauchi, Bauchi State.

Accept this as a formal invitation
Thank you

MAI GIRMA GWAMNA DAN GIRMAN ALLAH A TUNA DA WANNAN AIKINT**I GAMBAKI ZUWA CHINADE MAI TSAYI KM 15. ______________Mai Gir...
06/12/2023

MAI GIRMA GWAMNA DAN GIRMAN ALLAH A TUNA DA WANNAN AIKIN
T**I GAMBAKI ZUWA CHINADE MAI TSAYI KM 15.
______________

Mai Girman Gwamnan Jahar Bauchi Sen. Bala Muhammad Abdulkadir (Jagaban Katagum) Hakika wannan hanyar tana da matikar muhimmanci a rayuwar al'ummar wannan yankin na Bauchi ta Arewa. Karamar hukumar katagum. Domin yawan manoma dake amfani da hanyar dan fitar da kayan gonar su zuwa kasuwa.

Hakika samar da wannan hanyar zai taimaka sosai dan inganta rayuwar su wajen samun saukin rayuwar su.

Bisa yadda muka ga ka maida hankalinka kan abinda al'ummar sa ke bukata yake aiwatar masu na Alheri.

Hanyar zata tahada kananan hukumomi biyu Katagum da Giade wanann hanya ta tashine daga kwanar Gambaki tabiyo Gambaki tabiya cikin kasar Zirami ta Shiga har cikin garin Chinade mai tsawon KM 15

Hakika samar da wannan hanyar zai faranta zukatan alumma masu yawa kuma ya samar da saukin sufuri tsakanin alumma.

Yarima Gambaki
Secretary Madara Chinade Youth Progressive Forum
6/12/2023.

Inna lillahi wa Inna ilaihir Raji'un!!! Allah yayi rasuwama Hajiya Habiba sabo Gabarin mahaifiyar Hon Salisu Sabo.Janaโ€™i...
06/12/2023

Inna lillahi wa Inna ilaihir Raji'un!!!

Allah yayi rasuwama Hajiya Habiba sabo Gabarin mahaifiyar Hon Salisu Sabo.

Janaโ€™iza karfe 2:00 a Babban masallaci fadan Bauchi.

Ubangiji Allah ya jikan sa da rahama yasa Aljanna fiddausi ce makomar ta.

A Nijeriya muryoyin manyan malamai a kasar ya zo ษ—aya kan batun kisan masu taron Maulud a jihar Kaduna-----------Dukkan ...
06/12/2023

A Nijeriya muryoyin manyan malamai a kasar ya zo ษ—aya kan batun kisan masu taron Maulud a jihar Kaduna
-----------

Dukkan bangarorin jagorancin daga bangaren ฦŠariฦ™ar Tijjaniyya Izalah Kaduna Jos da kadiriyya sun nuna takaici da kuma Alhini kan abinda ya faru na sake bama bamai kan masu taron Maulud a jihar Kaduna.

Tun da fari Sheik Dahiru Usman Bauchi wanda yake jagora a ฦŠariฦ™ar Tijjaniyya ya miฦ™a saฦ™on taaziyata ga iyalai yan uwa da masoya kan wannan Ibtila'in, tare da neman gwamnati ta yi bincike da kuma biyan diyya ga wadanda lamarin ya shafa.

Itama kungiyar izala reshen Kaduna karkashin jagorancin Sheik Bala lau sun fidda jawabin manema labarai kan wannan batu yanda s**a jajantawa wadanda lamarin ya shafa tare da neman yin binciken kan lamarin.

Sheik Yusuf Sambo Riga Chikum daya daga cikin masu fada aji a tsagin Izalah shiyyar Jos ya yi Allah wadai da wannan lamari na hari kan masu Maulud ษ—in da sojoji s**a yi (bisa kuskure) tare da neman a gaggauta daukan Kwak kwaran mataki.

Inna Lillahi wa Inna Ilaihi rajiun Allah Ya yiwa Shugaban Karamar Hukumar Gombe Alhaji Aliyu Usman Haruna, (Ali Ashaka) ...
05/12/2023

Inna Lillahi wa Inna Ilaihi rajiun

Allah Ya yiwa Shugaban Karamar Hukumar Gombe Alhaji Aliyu Usman Haruna, (Ali Ashaka) rasuwa yau a kasar Misra Egypt. Bayan fama da doguwar jinya a can.

Allah Ya gafarta masa Yasa ya huta. Mutum ne na mutane mai k**ala da sanin ya k**ata.

AN SANYA ALAMONIN KAN HANYA DOMIN KIYAYE AFKUWAN HADARIA MARARRABAN LIMAN KATAGUM._________Babban matsalar rashin alamom...
05/12/2023

AN SANYA ALAMONIN KAN HANYA DOMIN KIYAYE AFKUWAN HADARI
A MARARRABAN LIMAN KATAGUM.
_________

Babban matsalar rashin alamomin kan hanya ya sanya ana yawan samun hadura a kan hanyar mararraban Liman Katagum karamar hukumar Bauchi.

Hakan ya sanya alummar yankin Taron wayar dakai don saka wasu alamomi akan hanyar Dan kawo karshen matsalan da ake samu tsakanin direbobi da makiyaya akan labi dake Hanyar Mararraban liman Katagum

Sanata Shehu Buba Umar ya dauki nauyin in aikin fidda alamomin karkashin jagorancin Alh Baba Sarkin Fawan Yalwa shugaban kungiyar SANATA SHEHU BUBA PROJECT 2027

05/12/2023

CIGABA DA RABON TALLAFI GWAMNA BALA ABDULKADIR YA SAKE MIKA TALLAFI MILIYAN 800M
_____________

Masu karbar Fansho na jihar Bauchi zasu amfana da tallafin miliyan 500m yayin da yan fansho Daga kananan hukumomi s**a samu tallafin Naira miliyan 300m.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad kauran Bauchi ya bada Tallafi a cigaba da rabon tallafi domin rage radadi halin da ake ciki a kasa.

Ofishin mai baiwa Gwamnan jihar Bauchi shawara kan harkokin yada labarai da Sadarwa Comr Mukthar Gidado.

CIGABA DA RABON TALLAFI GWAMNA BALA ABDULKADIR YA SAKE MIKA TALLAFI MILIYAN 800M_____________Masu karbar Fansho na jihar...
05/12/2023

CIGABA DA RABON TALLAFI GWAMNA BALA ABDULKADIR YA SAKE MIKA TALLAFI MILIYAN 800M
_____________

Masu karbar Fansho na jihar Bauchi zasu amfana da tallafin miliyan 500m yayin da yan fansho Daga kananan hukumomi s**a samu tallafin Naira miliyan 300m.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad kauran Bauchi ya bada Tallafi a cigaba da rabon tallafi domin rage radadi halin da ake ciki a kasa.

Ofishin mai baiwa Gwamnan jihar Bauchi shawara kan harkokin yada labarai da Sadarwa Comr Mukthar Gidado.

KISAN MASU TARON MAULUD A KADUNA...!!!Shugaba Tinubu ya yi umarni yin bincike.Ministan tsaron kasa Badaru ya yi alkawari...
05/12/2023

KISAN MASU TARON MAULUD A KADUNA...!!!

Shugaba Tinubu ya yi umarni yin bincike.

Ministan tsaron kasa Badaru ya yi alkawarin biyan diyya.

TA'AZIYYA CIKIN JIMAMI INA MATUKAR ALHINI GAMI DA  KADUWA TARE DA MAMAKIN YADDA AKA KASHE MUTANE SAMA DA 80 A TUDUN BIRI...
05/12/2023

TA'AZIYYA CIKIN JIMAMI INA MATUKAR ALHINI GAMI DA KADUWA TARE DA MAMAKIN YADDA AKA KASHE MUTANE SAMA DA 80 A TUDUN BIRI CIKIN KARAMAR HUKUMAR IGBORI DAKE JIHAR KADUNA
__________

Comdr Abdulrazak sani AlbanyChairman mafita ga matasan Arewa maso gabas 08102710732

Na Kadu Sosai, Kuma Nasha mamakin yanda Jami,an tsaro s**a sake bomb akan mutane Wanda yayi sanadin mutuwar mutane tare da jirkita Al,ummah dadaman Gaske
Kuma manyan wannan yanki sun ja bakin su sunyi shiru

1,Manyan gidan jaridun kasar Nan

2,Sarakunan da malaman addinai
3, dattawan Arewa
Kowa yaja bakin sa yayi shiru

Saboda Wanda aka kashe Yan Arewa ne marassa gata

Lokacin da aka kashe mutun daya mawaki akudan cin Nageria gaba daya Al, ummah da jaridun kasar Nan ko Ina katabah maganar akeyi .

Harta Majalisan tarayya sai da s**ayi zaman jimami na minti 1

Muna kira ga gwamnatin tarayya da na jihar Kaduna su tabbatar sunyi bincike tare da hukunci me tsanani akan duk Wanda yake da Hanu akan wannan ta,addan cin ran mu Yana da matukar muhimman ci Kuma hakkine ga gwamnati takare mana lafiyan mu

Amadadin ni kaina da iyalaina da matasa Arewa maso gabas Muna Mika sakon ta, aziyyar mu ga Yan uwan mu Yan Arewa Da iyalai Wanda s**a rasa ransu Allah yamusu gafara Allah yajikan su

05/12/2023

Jawabin SLA Hon Majama'a MatoKAI TSAYE...
Taron wayar dakai da saka wasu alamomi akan Hanyar Mararraban liman Katagum Dan kawo karshen matsalan da ake samu tsakanin dire obi da makiyaya akan labobi dake Hanyar Wanda Sanata Shehu Buba Umar ya dauki nauyin a karkashin jagorancin Alh Baba Sarkin Fawan Yalwa shugaban kungiyar SANATA SHEHU BUBA PROJECT 2027

05/12/2023

KAI TSAYE...
Taron wayar dakai da saka wasu alamomi akan Hanyar Mararraban liman Katagum Dan kawo karshen matsalan da ake samu tsakanin direbobi da makiyaya akan labi dake Hanyar Mararraban liman Katagum Wanda Sanata Shehu Buba Umar ya dauki nauyin a karkashin jagorancin Alh Baba Sarkin Fawan Yalwa shugaban kungiyar SANATA SHEHU BUBA PROJECT 2027

Sarkin garin SIRIN TAFAZUWA karamar hukumar GANJUWA ya miฦ™a saฦ™on godiya ga Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir-...
05/12/2023

Sarkin garin SIRIN TAFAZUWA karamar hukumar GANJUWA ya miฦ™a saฦ™on godiya ga Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir
-----------------

Cikin ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi take gudanarwa karkashin hukumar CSDA a fadin shiyoyi uku na jihar Bauchi, suma al'umman garin SIRIN TAFAZUWA karamar hukumar GANJUWA a shiyar Bauchi ta tsakiya sun amfana da aikin gina musu sabon asibiti da famfon tuka tuka.

Bisa ga wannan ne sarkin garin da al'umman sa s**a miฦ™a saฦ™on godiya ta musamman ga maigirma Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi kan wannan kunci da ya cire su a cikin sa.

A baya dai muna da asibiti amma ya lalace lalacewar da ya kai matakin da babu halin a masa kwaskwarima, sai sabo Gwamnan jihar Bauchi ya sa ma'aikatar CSDA ta gina mana yanzu haka mun samu sauki da kuma gushewar fargaba a wannan fanni na kiwon lafiya a garin SIRIN TAFAZUWA.

Muna Godiya bisa samar da ruwan sha a asibitin da kuma cikin gari wa wannan Gwamna ya mana.

๐€๐‹๐ˆ๐˜๐” ๐Œ๐”๐‡๐€๐Œ๐Œ๐€๐ƒ ๐€๐‹๐ˆ ๐™๐€๐ˆ ๐€๐๐†๐–๐€๐๐‚๐„ - :________๏ผก ๏ฝ๏ฝ๏ฝ„๏ฝ๏ฝ„๏ฝ‰๏ฝŽ๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ๏ฝŒ๏ฝ๏ฝŽ - :Mal Muhammad Aliyu(Mai jama'a) da kumaAlrm Malam ilyasu Us...
05/12/2023

๐€๐‹๐ˆ๐˜๐” ๐Œ๐”๐‡๐€๐Œ๐Œ๐€๐ƒ ๐€๐‹๐ˆ ๐™๐€๐ˆ ๐€๐๐†๐–๐€๐๐‚๐„ - :
________

๏ผก ๏ฝ๏ฝ๏ฝ„๏ฝ๏ฝ„๏ฝ‰๏ฝŽ
๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ๏ฝŒ๏ฝ๏ฝŽ - :

Mal Muhammad Aliyu
(Mai jama'a) da kuma
Alrm Malam ilyasu Usman Gital.

๐€๐”๐‘๐„๐ ๐˜๐€๐˜๐€๐ ๐’๐”-:
Aliyu Muhammad Aliyu
(Mal Abba) da Amaryan sa
Rukayya Iliyasu Usman Gital.

๐‘๐€๐๐€. Asabar 23/December /2023
๐‹๐Ž๐Š๐€๐‚๐ˆ - : 10:00 am
๐–๐”๐‘๐ˆ-: Sardauna Quarters bayan Nitel Bauchi.
09055243136

05/12/2023

Kai Hari ga masu taron maulaud a jihar kaduna.

Shekh Dahiru Usman Bauchi ya nemi shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin Gaggawa kan hakan. Ta bakin Babban Dan sa shekh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi.

AN DAKATAR DA KARATU A JAMI'AR ATBU BAUCHI NA TSAWON MAKO GUDA_________Jamiโ€™ar Abubakar Tafawa Balewa ATBU  Bauchi ta da...
05/12/2023

AN DAKATAR DA KARATU A JAMI'AR ATBU BAUCHI NA TSAWON MAKO GUDA
_________

Jamiโ€™ar Abubakar Tafawa Balewa ATBU Bauchi ta dakatar da karatu na tsawon mako guda a dalilin zanga-zanga da ษ—aliban jamiโ€™ar s**a yi bayan kashe wani ษ—alibin jamiโ€™ar da ฦดan Daba s**a yi.

Bisa ga sanarwar rufe jamiโ€™ar dake dauke da sa hannun mataimakiyar rajistarar makarantar Fatima Abdullahi wanda da โ€˜aka wallafa a shafin makaranta muka gani ya nuna cewa Jamiโ€™ar ta dakatar da karatu daga ranar 4 zuwa 10 ga Disemba.

Jamiโ€™ar ta dauki wannan mataki domin guje wa matsalar karya doka a makarantar.

Jamiโ€™ar ta ce daga ranar Litini za ta dauki mataki mai tsauri kan duk dalibin da ta k**a a harabar jamiโ€™ar.

Joseph Agabaidu wanda ke karantun kwas din โ€˜Applied Geologyโ€™ dake mataki na 500L ya gamu da ajalinsa ranar Asabar yayin da yake hanyarsa ta dawowa gidansa dake kasuwar Yelwan Tudu da misalin karfe bakwai na yamma.

Agabaidu ya rasu bayan โ€˜yan daba sun daษ“a masa wuka.

ฦŠaliban jamiโ€™ar sun fusata ne ganin k**ar ba a dauki wani mataki a kai ba. Wanda s**a bayyana fishin su da ya janyo aka kulle jami'an ana tsaka da karatu.

KISAN MASU TARON MAULUDI A JIHAR KADUNA GWAMNA JIHAR YAYI ALKHAIRIN YIN BINCIKE TARE DA DAUKAR MATAKI KAN LAMURAN. _____...
05/12/2023

KISAN MASU TARON MAULUDI A JIHAR KADUNA GWAMNA JIHAR YAYI ALKHAIRIN YIN BINCIKE TARE DA DAUKAR MATAKI KAN LAMURAN.
______________

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya umarci hukumomin tsaro da na gwamnati da du gudanar da bincike game da kisan dandazon ฦดan maulidi da a Kace sojojin Najeriya ne s**a yi kuskuren ษ—irka musu bamabamai.

Ance wai Sojojin Najeriya sun yi wa wasu mutane musulmi masu taron bikin maulidi a Tudun Biri, dake ฦ™aramar hukumar Igabi, jihar Kaduna. ne wai bisa kuskure.

Ance Sojojin cikin kuskure sun yi wa mutane ruwan bamabamai daga sama tunanin su ฦดan bindiga ne.
Kamar yadda aka rawaito.

Rahotanni sun kiyasta yawan mutanen da aka rasa ya kai mutum sama da 100.

Gwamna Sani ya yi alhinin wannan rashi da aka yi sannan ya ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da abin da ya auku, sannan kuma tabbatar da irin haka bai sake aukuwa ba

Bayan haka gwamna Sani ya umarci da a garzaya da wadanda s**a ji rauni asibitin Barau Dikko domin a duba su a kuma ba su magani.

โ€œNa ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin. Mun kuduri aniyar hana sake afkuwar wannan balaโ€™i tare da tabbatar wa alโ€™ummarmu cewa za a ba da fifiko wajen kare su a ci gaba da yaki da โ€˜yan taโ€™adda da โ€˜yan fashi da sauran miyagun laifuka.

Gwamna Sani a madadin alโ€™ummar jihar Kaduna ya mika taโ€™aziyya ga iyalan waษ—anda s**a rasu tare da adduโ€™ar Allah ya sama ma wadanda s**a jikkata da kuma gaggawar samun lafiya.

โ€œGwamnatin jihar Kaduna ta yi alhinin asarar rayuka da aka yi, kuma ta jajirce wajen ganin mazauna yankin sun ci gaba da rayuwa tare da gudanar da sanaโ€™oโ€™insu na halal ba tare da tsoro ba.

Gwamnan yayi alkawarin daukan mataki kan Lamarin.

MAI TALLAFAWA MINISTAN LAFIYA PROF ALI PATE  HON ABBA GARO  BASKO MANGARI. YA ZIYARCI KAFAR LABARI DAGA BAUCHI MEDIA DOM...
04/12/2023

MAI TALLAFAWA MINISTAN LAFIYA PROF ALI PATE HON ABBA GARO BASKO MANGARI. YA ZIYARCI KAFAR LABARI DAGA BAUCHI MEDIA DOMIN MARTANI KAN WASU MAGANGANU - :

A yau Hon Abba Garo Basko Mangari. Ya sake ziyaran kafar Labari Daga domin ๐‘ด๐‘จ๐‘น๐‘ป๐‘จ๐‘ต๐‘ฐ - 2)
kan wasu maganganu da ake yi kan Minista Lafiya da walwalar Jama'a Prof Ali Pate. wasu maganganu da ake yi kan Minista Lafiya da walwalar Jama'a Prof Ali Pate.

๐Ÿ‘‡
https://fb.watch/oK1CUO-3wO/?mibextid=Nif5oz

TSOHON KOMISHINAN KANANAN HUKUMOMI YA ZIYARCI KAFAR Labari Daga Bauchi DOMIN BADA SANARWA GA GWAMNATIJIHAR BAUCHI.Tsohon...
04/12/2023

TSOHON KOMISHINAN KANANAN HUKUMOMI YA ZIYARCI KAFAR Labari Daga Bauchi DOMIN BADA SANARWA GA GWAMNATI
JIHAR BAUCHI.

Tsohon Komishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Hon Ismail Muhammad Isah Wakilin tsafi. Lokaci mukin M A Abubakar (SAN) ya kawo ziyara kafar Labari Daga Bauchi Media yanda ya baiwa Gwamnatin jihar Bauchi shawara kan bashin da aka ciyo kan manyan ayyuka da za'ayi a jihar Bauchi.

๐Ÿ‘‡
https://fb.watch/oK1wojjIcN/?mibextid=Nif5oz

04/12/2023

๏ผฌ๏ผฉ๏ผถ๏ผฅ
๐‘ด๐‘จ๐‘น๐‘ป๐‘จ๐‘ต๐‘ฐ - 2)
Tare da Hon Abba Garo Basko Mangari.

Martani . Tirmi na (2) kan wasu maganganu da ake yi kan Minista Lafiya da walwalar Jama'a Prof Ali Pate.

04/12/2023

๏ผฌ๏ผฉ๏ผถ๏ผฅ
๐๐€๐˜๐˜๐€๐๐€ ๐‘๐€'๐€๐˜๐ˆ..

Tare da Tsohon Komishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Hon Ismail Muhammad Isah Wakilin tsafi.

Address

DADA Plaza, OPPOSITE FARIYA FOUNDATION
Bauchi
ABUBAKARUMARSTATESECRETARIAT740261

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labari Daga Bauchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Labari Daga Bauchi:

Share


Other Bauchi media companies

Show All