02/05/2020
Jihar Oyo ta ce likitanta ya kamu da korona bayan ya dawo daga Kano
Dokar hana fita ita ce babbar hanyar dakile coronavirus
Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yi wa duniya fyadar 'ya'yan kadanya.
Takaitacce
Karin bayani
Cutar korona ta tilasta sakin fursunoni kusan 10,000 a Philippines
Fiye da mutum 40,000 s**a kamu da korona a Afirka
Kano ce yanzu ta biyu a yawan masu korona a Najeriya
Mutum 92 sun kamu da korona cikin sa'a 24 a Kano
Ƙwararrun likitoci sun ce cutar korona ta fantsama cikin al'umma a Kano
An amince a fara amfani da maganin Ebola Remdesivir a matsayin maganin cutar korona
Rahoto kai-tsaye
Daga Brc fm azare(94.6)
LABARAI DA DUMI-DUMI:
*Boris Johnson ya raɗa wa ɗansa sunayen likitocin da s**a duba shi
Boris Johnson da budurwarsa Carrie Symonds sun raɗa wa jaririnsu sunan Wilfred Lawrie Nicholas Johnson.
Sunayen na girmamawa ne ga kakaninsu da kuma likitoci biyu da s**a kula da Mista Johnson lokacin da yana jinyar cutar korona a asibiti, k**ar yadda Mis Symonds ta wallafa a shafin Instagram.
Ta gode wa ma'aikatan asibitin jami'ar kwalejin Landon da s**a kula da ita.
*Philippines ta saki fursunoni kusan 10,000
Kusan fursunoni 10,000 aka saki a Philippines yayin da ƙasar ke yakin daƙile bazuwar cutar a cunkosun gidajen yari.
Kotun ƙoli ce ta bayar da umurnin sakin fursunoni 9,731 musamman waɗanda ke jiran shari'a, k**ar yadda kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya ruwaito.
Cutar korona ta yadu a cikin gidajen yarin Philippines musamman waɗanda s**a fi cunkoso.
An saki fursunonin ne saboda yadda kiyaye matakin nesa nesa da juna ya gagara a gidajen yarin da s**a cika maƙil.
Gidajen yarin da cutar ta yaɗu sun hada da na tsibirin Cebu inda mutum 348 s**a kamu zuwa Juma'a. Da kuma gidan yarin Quezon City da ke Manila babban birnin ƙasar.
Zuwa yanzu mutum kusan 9,000 s**a kamu da cutar korona a Philippines, yayin da 603 s**a mutu.
*Fiye da mutum 40,000 s**a kamu da korona a Afirka
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Tarayyar Afirka ta ce zuwa yanzu mutum 40.746 s**a kamu da cutar korona a mambobin kungiyar 53.
Cutar ta kuma kashe mutum 1,689, yayin da kuma mutum 13.383 s**a warke daga cikin wadanda s**a kamu.
Alkalumman hukumar sun nuna cewa cutar ta fi yaɗuwa da kuma yin kisa a arewacin Afirka inda ta k**a mutum 15,135, ta kuma kashe 1,057.
Yankin yammacin Afirka ne na biyu inda cutar ta fi yaɗuwa.
*Jihar Oyo ta ce likitanta ya kamu da korona bayan ya dawo daga Kano
Gwamnatin Oyo ta ce ta fara samun sak**akon gwaje-gwajen cutar korona da aka gudanar.
Gwamnan jihar Seyi Makinde ya sanar a shafinsa na Twitter cewa mutum ɗaya daga cikin sak**ako biyu da aka dawo da su, wani likita ne da ya dawo daga Kano yayin da ɗayan kuma ma'aikaci ne a hukumar tsaron farin kaya.
Gwamnan ya ce har yanzu tna jiran sak**akon gwaji 300, daga cikin samfur 775 da aka ɗauka.
*Cutar korona ta ƙara k**a wani ministan Rasha
Cutar korona ta k**a ministan ayyuka na Rasha Vladimir Yakushev, kwana guda bayan cutar ta k**a Firaminista.
Cutar ta kuma k**a mataimakin ministan, k**ar yadda kafofin yada labaran Rasha s**a ruwaito.
A ranar Alhamis ne Firaminista Mikhail Mishustin ya shaida wa shugaba Vladimir Putin cewa yana ɗauke da cutar.
Yanzu shugaba Putin na tattaunawa kan tafiyar da harakokin gwamnati ta hanyar bidiyo.
cikin sa'a 24, mutum 9,623 aka tabbatar da sun kamu da korona a Rasha, kuma fiye da rabinsu a Moscow.
Cutar na kara yaɗuwa kusan a kullum, yayin da ta kashe mutum 1,222 a Rasha.
*Mutum 43 sun kamu da Korona a gidan yarin Kinshasa
An samu mutum 43 da aka tabbatar da sun kamu da cutar korona a gidan yarin soji na N'dolo da ke birnin Kinshasa kasar Jamhuruiyyar Dimokudariyar Congo.
Jami'an lafiya da hukumomin gidan yarin na kokarin daukar matakan dakile yaduwar cutar tsakanin sauran fursunonin da ke gidan yarin.
Hukumomin sun ce suna tunanin kafa tanti a gidan yarin domin killace wadanda s**a kamu tare da kuma rage cunkoso a gidan yarin.
Tun 10 ga watan Maris, mutum 604 aka tabbatar da sun kamu da cutar a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo, kuma kashi 96 na yawan wadanda s**a kamu suna birnin Kinshasa. cutar ta kashe mutum 32 a kasar, yayin da 75 s**a warke.
*Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana karon farko
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana karon farko a cikin kusan mako Uku, hakan ya kawo karshen rashin ganinsa da ya soma daukan hankali tsakanin kasashen da ke jita-jita kan lafiyarsa.
Kamfanin dilancin labaran kasar ya ce ya kaddamar da masana'antar taki a kusa da birnin Pyongyang.
An fitar da hotunan da ke nuna shi lokacin da yake bude masana'antar cikin yanayi na fara'a tare da wasu jami'an gwamnati.
Babu dai wani bayani kuma ba a ambato inda Mista Kim ya shiga kwana biyu ba, ko dalilan rashin ganinsa har a taron kasar mai muhimmanci da aka gudanar a tsakiyar watan Afrilu.
*Amurka za ta gaggauta amfani da Remdesivir a matsayin maganin cutar korona
Hukumomi a Amurka su bada umarni a gaggauta fara amfani da kwayar Remdesivir a matsayin maganin cutar korona.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka FDA ta dau wannan matakin ne bayan gwaji ya nuna cewa maganin na rage yawan alamun cutar.
Maganin wanda tun farko an samar da shi ne domin magance cutar Ebola.
Kamfanin Gilead, wanda ya ke yinsa, ya bayyana yunkurin a matsayin mai matukar amfani kuma irinsa na farko, sannan zai bayar da kyautar kwalbar allurar miliyan daya.
Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence ya ce za a fara raba maganin zuwa asibitoci a ranar Litinin.
*Indiya ta tilasta amfani da waya mai nuna masu cutar korona
Gwamnatin Indiya ta tilastawa ma'aikata a ƙasar yin amfani da wata manhaja a wayar salula da aka samar da za ta gano mutanen da s**a kamu da cutar korona.
Wannan matakin na zuwa a yayin da gwamnatin ta fara sassauta dokar kulle a yankunan da babu cutar sosai.
Manhajar mai suna Arokya Setu, a watan da ya gabata ne aka ƙaddamar da ita. Tana sanar da masu amfani da ita idan sun yi cudanya da mutanen da gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.
Masu gwagwarmaya dai na bayyana damuwa kan bayanan da ake samu za su iya keta sirrin mutane.
*Cutar korona ta fantsama cikin al’umma a Kano – Dr Sani Gwarzo
Tawagar ƙwararrun likitoci da s**a je Kano domin kai wa jihar ɗauki, sun ce abin da ake tsoron ya faru ya riga ya faru a Kano.
Dakta Nasiru Sani Gworzo, ɗaya daga cikin tawagar ƙwararrun likitocin ya shaidawa shirin Ra’ayi Riga na BBC cewar cutar korona daga mataki na ɗaiɗaikun al’umma yanzu ta fantsama cikin al’umma.
"Zance mafi inganci yanzu, korona ita ta ke yin awon gaba da yawancin mutanen da suke mutuwa,” in ji shi.
Ya ce kafin cutar korona ana zuwa asibiti, wasu na zuwa ƙasashen waje neman lafiya amma yanzu ba wurin zuwa. Irin haka ya sa mutanen da ba ma korona ba ce suke mutuwa.
"Amma akwai korona ita kanta, domin adadin da muke gani a gwaje gwaje a baya, idan aka kai samfur 100 ana samun biyar zuwa 10 masu korona amma yanzu idan aka kai 100 za a dawo da 80 duk korona ce.
Dakta Gwarzo ya ce abubuwan da s**a gano suna da yawan gaske.
Ya ce bayan an dawo da yin gwaji a Kano, kuma za a bude sabon ɗakin gwaji wanda za a iya linka adadin yawan waɗanda ake yi wa gwaji a rana.