20/09/2021
LARURAR CIZON KARE [RABIES DISEASE]
🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕🐕
Wani lamari me saka damuwa da ya faru shine; Na wata daga irin yaran nan Mata dakan rika zuwa taimakawa wajen aikace-aikace ga Matan da mazajensu kan basu wannan damar ta daukar yan aiki, domin su ragemusu ɗawainiya sannan kuma su irin waɗannan yaran ta ɓangarensu su sami abun rufawa kansu da iyayensu asiri wajen rage wasu hidindimun daga ɗan albashin da akan riƙa basu. Toh a gidan da yarinyar ke aikin ne tsautsayi ya gitta Karen 🐕 da aka aje agidan ya cije ta.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Toh abinka da rashin sani, ko rashin tausayi, ko rashin hankali ko duk baki daya tare da nuna halin ko inkula da rashin daukar rayuwar wani da mahimmanci na wasu shashashun Matan ko Magidantan masu jin suna da rufin asiri;
Sun fa gani sun san kare ya cijeta amma dake wawaye ne, Mijin ko Matar aka rasa me ɗaukar yarinyar ya kaita asibiti domin bata kulawa ai mata allurar rigakafin cizon kare da ake kira ANTI-RABIES.... saboda basason kashe kudi, wanda na tabbata da cikin ƴaƴansu ne ya ciji wani bana tsammanin zasu ƙi yin komi akai...
Tunda kowa ya sani in kare🐕 ya ciji mutum dole ana sanarwa akai ai masa rigakafi.
Haka sai sannu akaiwa yarinyar inda ya cijetan a kafa ta samu abu ta daure kafar... ta cigaba da aikace-aikace cikin dauriya.
Saboda galibi wasu rashin imaninsu yakai ko irin wadannan yan aikin nasu basa tausayawa inbasu lafiya, infact ko hutawa s**ai saboda tsiya da talauci yai musu yawa suna ganin damar cewa zasu zame a kudin albashin aikin yaran.... Domin ni gurina duk arzikin mutum inbaida tausayi da jin qai matalauci ne.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Karshe yarinyar zuwa kashe gari da safe da bata fito ba aka duba aka sameta duk ta wani barƙale dakin ya fita hayyacinsa tana buge-buge tare da haushi irin na kare.... wanda wannan ke nuna karen na dauke da kwayoyin cutar na REBIS kuma har kwayoyin cutar sun kai ga taba kwakwalwarta sak**akon halin ko inkula da aka nuna Mata 😥
A takaice de yarinyar nan de na halin gargara yanzu... domin ba abunda likita zai iyama idan kwayoyin Rebis s**a kai ga kwakwalwa, saide kurum yai ma allurar da zata iya saka kaji bacci da sauran yan dabaru... saboda akiyaye sauran mutane daga farmakinka, sannan kaima ka sami saukin dena haushin karnukan tare da duduma kafin mutuwa tazo ta daukeka.... domin karshen abunda zai faru kenan.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Mutanen mu walau na birni ko kauyuka suna da son kiwon dabbobi amma sam basusan sharrudan ajesu ba, basusan sui musu rigakafi ba, basusan hatsarin su ba, kai hatta dabbobin da ake iya yankawa aci irinsu Rago🐏 mutanen mu basusan in basu lafiya s**aisu asibiti adubasu ai musu karin ruwa ba, ko acire musu hakori in yana ciwo abasu magani in anga basa iya cin abinci... duk da ba ko ina ake da irin wadannan asibitocin ba, da yawa sunfi gane su sayar ko su yanka. Toh ballantana dabbobi irin su kare da bacin naman su ake ba, ko rukunin Maguna 🐈
Domin hatta mage 🐈⬛ kwai hatsari tattare da ita inba rigakafi tun ma ba ga Mace me ciki ba, tana iya sanadin da zaki haifo yaro me dauke da nakasa iri iri ajika, wato wata irin suffa me ban tsoro inkika hadu da Toxoplasmosis wato kwayar cutar da ake samu a kashin magen. Don haka ake hankali da kai al'umma.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
A wannan gaɓar nakeson nusar da mutane kunga kare da kuke ganinsa ku kiyayesa, muddin ba dole ba banga amfanin ajesa agida ko anguwa ba matukar bazaka iya dawainiyar rika wankesa kana kaisa rigakafi ba... domin kana iya sanadin mutuwar bayin Allah a dalilinsa. Yafi kowa cikin dabbobi hatsarin debo kwayar cutar rabies, kuma shi inyana da ita ba wata alama zaka gani ba, saide in ya ciji wani agani.
Rebis hatsabibiyar kwayar cuta ce da inta shiga jiki ahankali take rubanya acikin jijiyoyi har ta samu takai ga kwakwalwa🧠, domin kwakwalwa itace babbar target din cutar, shyasa duk wannan rigakafin ana Maza ayi ne kafin kwayiyoyin s**ai ga kwakwalwa
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Kwayar Rebis Virus ce, wanda duk abunda akace virus to yana da wuyar sha'ani domin magani bai cika tasiri kansa wanda shiyasa hatta cutar Kanajmau ka gaza samar da Maganinta.
Toh shima Rebis da kake gani bata jin wani magani, saboda kwayar cutar tana da SILKE wato k**ar kace "Bullet Proof" wanda a likitance mukan kira "Inclusive Bodies" da babu wani magani dake da karfin fasa wannan silken ballantana ya cimma virus din ya kashesa... yadda kaga bindiga bata fasa Bullet Vest.
Shyasa babban Mahimmin abu ai maza ai riga kafin dakile tafiyar virus din.
■ Idan Kare Me kwayar cutar ya cije ka a ƙafa toh ana tsammanin virus din zai isa ga kwakwalwa cikin Awa 24 da cizon
■ Idan Kare Me kwayar cutar ya ciji mutum a hannu toh ana tsammanin virus din zai isa ga kwakwalwa cikin Awa 12 da cizon.
■ Idan Kare Me kwayar cutar ya ciji mutum a jika ko wajen fuska toh ana tsammanin virus din zai isa ga kwakwalwa cikin Awoyi 4 da cizon.
Wannan tasa aje gaggawa, domin waccan yarinyar banda sun nuna ko inkula da ya cijeta a kafa bai k**ata akyale har dare yai taje ta kwanta ahaka ba.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Idan virus din yaje kwakwalwa k**ar yadda nace Babu abunda likitoci zasu iyayi sai addu'a da fatan sassauci gurin ubangiji, amma de 99.9% Mutuwa ce ke biyo baya. Kuma Eh ba karya bane haushin kare da haniniya zakaji mutum nayi intaje kwakwalwa, ana dannesa yana fisgewa...
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
KUNSAN WANI KARIN HATSARI
Duk wanda karen ya ciza tohfa kuma masu bashi kulawa asanda virus din yaje kwakwalwa sai kunyi a hankali dashi, inba haka ba duk wanda ya tsirtawa miyau har ya yawun ya shiga idonsa, bakinsa ko hancinsa tohfa shima ya harbu... ballantana ya gatsawa mutum cizo... cikin kasa da awa 4 kuma kuna iya zamowa a halin da yake.
Shyasa suke dalalar yawu yadda kare keyi, tare da tsoro in s**aga kofin ruwa, da jijjiga, KOH FA A GADON ASIBITI SAI AN HADA DAURESU, Saboda bala'in abun da irin yadda suke kai wawura.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Don haka sakon anan; Adena wasa da karnuka, babu wani batun jarumta malam; in kare ya biyoka wanda baka tabbacin komi kansa na rigakafi taka da gudu 🏃♂️ba yawa bane kare kaine ne. Yana cewa Wooum kaima ce masa Wooum... daga nan duqa kasa k**ar zaka dau dutse... zakaga yaja da baya.. saboda karw yafi tsoron jifa sama da ka dau abun duka... yana ja da baya karkai sauri dagowa kuma yin k**ar irin kyak dinnan zai kara baka tazara daganan maza ka rika tafiya ahankali kana yi kan duqawa... kana bashi tazara runtuma da gudu kurum ka auka wani gidan ko cikin mutane.
Duk sanda kare yai cizo karka tsaya tunanin kudi, ko kidney dinka zaka sayar gara ai ciniki ka sayar aima rigakafin... don kasan irin mahimmancin da take dashi.
Don Allah Jama'a ku dena aje karnuka haka kurum alhalin bazaku iya lura dasu ba, kuna saka rayuwar al'umma cikin hatsari gaskiya.
Allah kuma tsaremu amin
✍🏼
[Ibrahim Y. Yusuf]