16/02/2024
Hukumar hisbah ta k**a matashiyar budurwar nan mai suna Ramlat Princess, bayan ta tallata kanta a wani faifen bidiyo tare da yada shi a shafukan sada zumunta.
An jiyo Ramlat a cikin bidiyon ta na cin alwashin duk namijin da zai aure ta, sai ya auro mata wata macen da za ta dinga yin lalata da ita.
A baya-bayan nan hukumar Hisbar ta sha kai sumame mai taken Kawar da badala, a wuraren da ake zargi ana aikata aiyukan da s**a saba da tarbiya da kuma koyar addinin musulinci.
Jihar Kano jaha ce , ta musulinci wadda ta ke tafiya da dokokin shari’ar musulinci, sai dai sak**akon matsalolin rayuwa da kuma zaman banza da rashin aikin yi, ya sanya wasu matasa sun mayar da shafukan sada zumunta wajen huce haushin su, da yin duk abunda s**a da dama.
Idan ba a manta ba, idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewar a ranar talatar da ta gabata, hukumar Hisbar ta k**a shahararriyar yar Tiktok din Murja Ibrahim Kunya, har ta gurfanar da ita a gaban wata kotun shari’ar addinin musulinci tare da aikewa da ita gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya bisa zargin aikata badala, tara batagari cikin dare da kuma tada hatsaniya da daidai sauransu.
Kawo yanzu dai hukumar ta hisbar ba ta bayyana matakin da za ta dauka ba akan Ramlat Princess, bisa zargin da ake yi mata.
A makon da muke ciki ne Mukaddashiyar babban kwamandan hukumar bangaren mata DR. Khadija Sagir Sulaiman, ta bayyana cewa za su ci gaba k**a masu hawa shafin Tiktok suna furta kalaman batsa domin ba za su daga mu su kafa ba.
Al’ummar jahar sun yi fsrin ciki da kamen da hukumar ta fara domin tauna aya don tsakuwa taji tsoro, sak**akon yadda wasu ke zargin akwai shafaffu da mai da ba a iya taba su, wanda hukumar ta musanta zargin tare da cewar babu wanda yafi karfin doka matukar an same shi da aikata laifi