Arewa For Asiwaju

Arewa For Asiwaju Nigerian News Hausa wata kafar labarai ce ta intanet da ke kawo sahihan labarai cikin harshen Hausa.

Manufarmu ita ce isar da labarai na gaskiya da inganci ga al’umma.

09/12/2024

Tsarabar mako daga fadar shugaban ƙasa mai ɗauke da ayyukan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar a cikin makon da ya gabata.

Sako daga ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz

Wasu daga cikin alfanun tafiyar Shugaba Tinubu Afirka ta Kudu.
06/12/2024

Wasu daga cikin alfanun tafiyar Shugaba Tinubu Afirka ta Kudu.

Mun Jinjina Da Irin Rawar  Da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin Maliya Ya Taka Wajen Dakatar Da Dokar H...
05/12/2024

Mun Jinjina Da Irin Rawar Da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin Maliya Ya Taka Wajen Dakatar Da Dokar Haraji

Sanarwa daga Kungiyar 'Concerned Northern Group for National Unity and Integration,' ranar 5 ga Disamba, 2024

Muna jinjinawa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, bisa rawar gani da ya taka wajen shiga tsakanin Shugaban Kasa, ‘Yan Majalisar Dattawa na Arewa, da sauran masu ruwa da tsaki. Jagorancinsa wajen dakatar da muhawarar Majalisar Dattawa kan kudirin gyaran haraji wanda yake ɗauke da cece kuce da sauransu.

Ta hanyar umartar Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa da su dakatar da aikin kan kudirin da kuma kafa kwamitin musamman don tattaunawa da bangaren zartarwa, shugabancin majalisar ya dauki matakin da ya dace don warware matsalolin da ke tattare da kudirin.

Muna yabawa Sanata Barau Jibrin bisa nuna jagoranci da amsa kiraye-kirayen kungiyoyi kamar kungiyar gwamnonin Arewa, ‘yan majalisun wakilai na Arewa, sarakunan gargajiya, da matasa, wadanda s**a bayyana damuwar su kan illar da kudirin zai iya yi wa tattalin arzikin yankin.

Sai dai abin takaici ne yadda wasu ‘yan siyasa da kungiyoyin siyasa s**a yi amfani da wannan rikicin don su zargi wasu shugabannin Arewa da ke aiki tukuru a boye don kare muradun yankin. Muna kira gare su da su duba al’amuran kasa daga hangen ci gaba ba wai kayan siyasa ba.

Sanata Barau Jibrin ya nuna kishin kasa ta hanyar gudanar da taruka da tattaunawa ba dare ba rana da manyan jiga-jigai a bangaren zartarwa, majalisar dokoki, da wasu gwamnonin Arewa, har ma da shugabannin ra’ayi, domin samun mafita mai amfani ga kowa.

Muna kara kira gare shi da ya ci gaba da tsaya tsayin daka kan batutuwan da ke da tasiri ga hadin kai, zaman lafiya, ci gaban kasa, da jin dadin jama’a baki daya.

A Nigeria First, muna maraba da duk wani mataki ko tsari da ya yi daidai da adalci, daidaito, da ci gaba mai dorewa ga al’ummar Najeriya.

Allah ya raya Jamhuriyar Tarayyar Najeriya!

Shugaban Kasa na Kungiya
Comrd Hamza Umar

Ƙungiyar The Arewa Leadership Awareness Forum ta jinjinawa Sanata Barau kan gabatar da ƙudirin sanya Sunan Ɗan Masani a ...
04/12/2024

Ƙungiyar The Arewa Leadership Awareness Forum ta jinjinawa Sanata Barau kan gabatar da ƙudirin sanya Sunan Ɗan Masani a Kwalejin Ilimi ta tarayya FCE da ke jihar Kano

Ƙungiyar dake fafutikar wayar da kan al'ummar Arewa kan Shugabanci-The Arewa Leadership Awareness Forum” na maraba da sanya sunan wanda ya bada gaba ɗaya rayuwar sa ga cigaban ƙasa da ilimi, amma abin baƙin ciki ne yadda Gwamnatin Jihar Kano tayi tunanin cire sunan mutum kamar marigayi Ɗan Masanin Kano wanda ya bada gagarumar gudummawa matuƙa ga cigaban yankin Arewa dama Najeriya baki ɗaya.

Yunƙurin ƙasƙantar da sunan mutum kamar sa ba ƙaramin hatsari bane ga al'umma, domin Ɗan Masanin Kano Gwarzo ne a Najeriya, kuma gudunmuwar sa ga Dimokuraɗiyyar Najeriya da muke taƙama muke amfana da ita ba zai taɓa misaltuwa ba.

A yayin da muke yabawa ƙoƙarin Sanata Barau Jibril na gabatar da ƙudirin da yayi na sanya sunansa a Kwalejin Ilimi ta tarayya FCE Kano domin tunawa dashi a zauren Majalisar Dattijai ba ƙaramin abin azo a yaba bane ba.

Muna kuma yin Allah wadai da babbar murya ga abinda Gwamnatin Jihar Kano ta yi na cire sunan sa don nuna rashin mutuntawa domin Gwamnatin Jihar Kano ya kamata ta fahimci cewa Sunan marigayi Maitama Sule ba zai taɓa goge wa ba a Najeriya ko a duniya baki ɗaya.

Sanya sunan sa a kwalejin Ilimi ta tarayya FCE Kano, girmamawa ce da mutuntawa bawai ga iyalansa ba ko al'ummar jihar Kano ba, har da ilahirin yankin Arewa dama ƙasa baki ɗaya.

A ƙarshe kungiyar ta ƙara jinjinawa Sen. Barau tare da yaba masa akan ƙoƙarinsa na ganin an ɗaukaka tare da mutunta sunayen manyan mutane, a saboda haka zamu cigaba da gode maka kuma kana binmu bashi, kuma muna addu'a ga Allah da ya cigaba da kare ka da kuma yi maka jagoranci a gagarumin aikin da kayi.

Sa Hannu:✍️
Comrade Abubakar Sadiq
Arewa Leadership Awareness Forum.
Secretary General.

Yau Saura Kwanaki 917 Wa'adin Mulkin shugaba Tinibu Nafarko Ya ƙare, Idan Kuma aka sake zuba masa zunzurutun kuri'u rata...
04/12/2024

Yau Saura Kwanaki 917 Wa'adin Mulkin shugaba Tinibu Nafarko Ya ƙare, Idan Kuma aka sake zuba masa zunzurutun kuri'u ratata a shekarar 2027 to ya rage saura Kwanaki 2,378. Ya koma legas.

Muhammad Cisse ✍️

MATSAYAR GAMAYYAR ƘUNGIYOYIN MUTANEN AREWA CNG KAN DOKAR SAKE FASALIN HARAJIRana: Talata 3 ga watan Disamba na Shekarar ...
04/12/2024

MATSAYAR GAMAYYAR ƘUNGIYOYIN MUTANEN AREWA CNG KAN DOKAR SAKE FASALIN HARAJI

Rana: Talata 3 ga watan Disamba na Shekarar 2024

Gabatarwa

Gamayyar Ƙungiyoyin Mutanen Arewa ta yi dubi tare da yin nazari akan cece-kucen da ake cigaba da yi kan Dokar sake fasalin haraji da Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da shi.

A yayinda Gwamnati da ƴan kan zaginta suke cigaba da cewa wannan dokar sake fasalin haraji an tsarata ne domin inganta kuɗaɗen shiga gami da haɓɓaka tattalin arziki, amma kuma a ɗayen ɓangaren da yawan ƴan Najeriya na kallon cewa wannan doka wani yunkuri ne na sanya ƙarin matsatsi ga ƴan Najeriya da ke cikin tsananin talauci inda ake so a maida su bayi a ƙasar su ta gado.

Ƙungiyar CNG, kamar dukkanin ƴan Najeriya, na sane da cewa ƴan Najeriya na fuskantar halin matsatsin rayuwa da s**a haɗa da talauci da rashin aikin yi da ilimi da kuma rashin nagartaccen wurin lafiya da kuma lalatattun gine-ginen gwamnati.

Sauran sun haɗa da hauhawar farashi, da yawaitar ƙarin kuɗin haraji da cin hanci da kuma kariya ga jami'an gwamnati wanda ya waɗannan s**a hana mu cigaba.

Ƙungiyar CNG bayan ta yi nazari na tsanaki akan dokar sake fasalin haraji, ta yi imanin cewa wannan zai ƙara matsatsi akan halin rayuwar da ake ciki, inda jihohi uku da birnin tarayya su kaɗai ne za su amfana da wahalhalun mu.

Shawarwari

1 Sake fasalin rarraba kuɗaɗen haraji na VAT da aka tara ga jihohi

2 Cigaba da samar da kuɗaɗen ga hukumomin da ke kawo cigaba irin su TETFUND, NITDA da NASENI

3. Dakatar da ƙara kuɗaɗen haraji na VAT tare da samo sabbin hanyoyin da zata samu Kudaden shiga

4. Tattaunawa da masana, Kungiyoyin fararen hula, da masu ruwa da tsaki a ƙasa baki ɗaya kan sake fasalin haraji.

Matsayar Gamayyar Ƙungiyoyin Mutan Arewa CNG

A dalilin bayanai da aka tattauna na sama, CNG ta yi watsi da dokar sake fasalin haraji da babbar murya Indai a yadda take ne. Domin sun nuna naƙasu ga kuɗaɗen haraji da s**a nuna dai-dai to da shigar da kowa da tabbatuwar hakan.

Wannan gwamnati tare da sake fasalin ta da dokokin sun nuna rashin tausayi tun farkon siyasar Najeriya.

Tun farkon gwamnatin nan, ta haifarwar mutane talauci da rashin tausayi wanda ya haifar da halin damuwa tare da lalata tattalin arzikin Najeriya.

CNG na tunatar da gwamnati akan wannan dokar sake fasali a ɓangaren tattalin arziki da cire tallafin mai ta haifarwa ƴan Najeriya mugun yanayi inda masu rufin asiri da arziki s**a koma maroƙa, inda talakawa s**a koma cikin mawuyacin hali.

CNG na neman cewa maganar barin Lagos a matsayin inda za'a riƙa shigo da kayayyaki dole a daina hakan, a bari a riƙa shigo da kayayyaki ta hanyar iyakoki na ƙasa da ke Kwara da Borno da Kebbi da Katsina da sauran jihohi.

Haka zalika, dole gwamnati ta kammala aikin gyara tashoshin ruwa na Baro da Lokoja da Makurdi da Warri da Calabar da Onitsha domin baiwa jihohin su samu kuɗaɗen shiga akan halin da ake ciki na barin Legas kaɗai a matsayin inda ake shigo da kaya.

CNG ta jaddada cewa dukkanin tashoshin ajiye kaya na tudu da ke a Kano da Aba da Ibadan da Jos da Katsina da Maiduguri da Kaduna dole a dawo da su aiki don tabbatar da adalci da daidaito da shigo da kowa.

A yayinda muke yabawa Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) da Majalisar Masana tattalin arziki ta ƙasa da Sarakunan Gargajiya na Arewa da wasu ƴan Majalisu da su tsaya tsayin daka don ganin ba a ƙaƙabawa ƴan Najeriya wannan halin ba, muna kira ga ƴan Majalisu da su ƙara samun gwiwa gami da ɗaukar mataki akan wannan dokar sake fasalin haraji.

A karshe, Gamayyar Ƙungiyoyin Mutan Arewa CNG na yin kiran gaggawa da a dakatar da wannan dokar sake fasalin haraji domin a samu tattaunawa ta masana gami da samun bayanan masu ruwa da tsaki da ƴan Najeriya baki ɗaya don ganin an ƙaddamar da tsarin dokar haraji mai cike da gaskiya a ƙasar.

Sa Hannu:✍️
Kwamarad Jamilu Aliyu Charanchi
Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Mutanen Arewa ta ƙasa CNG

DOKAR HARAJI: Abinda Sanata Barau Ya Yi Ba Da Maŕaba Da Cìn Amànaŕ AŕèwàDaga Datti AssalafiyShekaran jiya an tafka muhaw...
29/11/2024

DOKAR HARAJI: Abinda Sanata Barau Ya Yi Ba Da Maŕaba Da Cìn Amànaŕ Aŕèwà

Daga Datti Assalafiy

Shekaran jiya an tafka muhawara a Majalisar Dattawa kan sabon dokar haraji na Shugaban Kasa Tinubu.

An yi musayen kalamai masu zafi tsakanin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Senator Barau Jibrin Maliya da Senator Ali Ndume.

Ta bayyana a fili Sanata Barau Jibrin yana goyon bayan kudurin Tinubu ne ba talakawan Nigeria ba, akan hakan yaci mutuncin Senator Ali Ndume ya gwale shi.

'Yan Arewa ba zasu ga fitina da tashin hankali mafi muni ba sai idan an amince da wannan sabon kudirin haraji na Tinubu, amma duk da wannan shi Senator Barau Jibrin bai dameshi ba, saboda wai yana son Tinubu ya wuce masa gaba a tsayar da shi takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2027 idan Allah Ya kai mu.

Ya kamata mutanen Arewa mu canza tunanin mu, kar neman biyan bukata yasa mu yi watsi da bukatar yankin mu, babu wani alheri a yin hakan.

Senator Barau Jibrin Maliya kaji tsoron Allah, kar ka yarda Tinubu yayi amfani da kai don cimma sabon tsarinsa na haraji, ba sai ka yi abinda zai jefa yankin ka na Arewa cikin bala'i zaka samu biyan bukata na zama Gwamnan jihar Kano ba, abinda kake kokarin aiwatarwa cin amanar Arewa ne.

Yaa Allah Ka haŕamta wa Tinubu da wadanda zai yi amfani da su samun nasara akan sabon haraji.

Muhimman nasarorin da Shugaba Tinubu ya samarwa Nigeria a taron G20 da ya gudana a Kasar Brasil👇👇.
26/11/2024

Muhimman nasarorin da Shugaba Tinubu ya samarwa Nigeria a taron G20 da ya gudana a Kasar Brasil👇👇.

24/11/2024

Rikicin Masarautar Kano: Hira ta musamman tare da Hon. Hassan Saleh Jirgi inda ya musanta abunda Kwankwaso ya fada akan Shugaba Tinubu nada hannu akan rikicin fadar jihar kano.

AN ZABI HON RABI'U SAYYADI KABO A MATSAYIN CHAIRMAN NA KUNGIYAR 'YAN TAKARAR PDP NA MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KANO A ZABEN...
23/11/2024

AN ZABI HON RABI'U SAYYADI KABO A MATSAYIN CHAIRMAN NA KUNGIYAR 'YAN TAKARAR PDP NA MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KANO A ZABEN 2023

A yammacin Asabar, 'yan takarar PDP na Majalisar Dokokin Jihar Kano na shekarar 2023 sun gudanar da taro a Tahir Guest Palace, Kano. Bayan tattaunawa mai zurfi kan al'amuran da s**a shafi wannan kungiya, an cimma wadannan matsayoyi:

1. Rushewar Tsohon Shugabanci Kungiyar:
Kungiyar ta yanke shawarar rushe tsohon shugabanci na baya, wanda Muzakkir Rabi'u yake jagoranta. Wannan mataki ya zama dole sakamakon rashin ingantaccen shugabanci da rashin kwarewar aiki daga bangaren shugabancin da kuma rashin biyayya ga jam'iyya da kuma jagororin jam'iyyar PDP.

2. Fidda Sabon Shugabanci:
Domin farfado da ayyukan kungiyar tare da tabbatar da wakilci mai inganci, an zabi Hon. Rabi’u Sayyadi Kazode tsohon ɗan takarar majalisar jiha a ƙaramar hukumar Kabo a matsayin sabon shugaban kungiyar.

3. Yarda da Sabon Shugaba:
Mambobin kungiyar sun bayyana gamsuwarsu da cancantar Hon. Rabi’u Sayyadi Kazode wajen jagorantar kungiyar cikin nasara. Sadaukarwarsa da amincewar da aka yi masa cikin kungiyar ne s**a tabbatar da dacewarsa da wannan matsayi.

4. Daurewa Kan Hadin Kai da Ci Gaba:
Kungiyar ta sake jaddada kudurinta na kara karfafa hadin kai da kuma ci gaban manufofin PDP a Jihar Kano. Mambobi sun yi alkawarin aiki tare karkashin sabon shugabanci domin cimma burin da aka sanya gaba.

Kungiyar ta kuma nuna godiyarta ga dukkan mambobi saboda jajircewarsu da kuma goyon bayan da suke bayarwa ga manufofin jam’iyyar PDP.

Sa Hannun PRO Na Kungiyar
Abdullahi Dalhatu Awilo

Ina Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Shugaban Majalisar Dattijai Akpabio Da Mataimakinsa Barau Jibrin Maliya Su Sauka Daga M...
19/11/2024

Ina Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Shugaban Majalisar Dattijai Akpabio Da Mataimakinsa Barau Jibrin Maliya Su Sauka Daga Mukamansu ~ Hon Rabi'u Sayyadi

Tsohon ɗan takarar majalisar jiha a ƙaramar hukumar Kabo Hon Rabi'u Sayyadi Kazode yayi kira na musamman ga shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa da su gaggauta sauka daga muƙamansu tunda sun zama yan amshin shata.

Babu shakka, yanayin wahalar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki a halin yanzu ya kai matsayin da ba zai yiwu shugabannin kasa su zuba ido ba tare da daukar matakai masu tsauri ba. Duk da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman karin bashin Naira tiriliyan 1.7, bai kamata majalisar dattijai tayi shiru ba tare da tsayawa tsayin daka wajen kare muradun ‘yan kasa ba.

Wannan bashin da shugaban ke shirin ciyowa ba karamin mayar da kasar baya zai yi ba, domin shekara da shekaru kenan ana ciyo bashi amma kullum wahalhalune ke kara yawaita a cikin kasarmu Najeriya, yan siyasarmh sun koma ba da naira dubu biyar ga yan kasa, yayin da suke kara kashe kasar da bas**a masu tarin yawa.

Mun lura cewa shugaba Godswill Akpabio da mataimakinsa Barau Jibrin Maliya ba sa taka rawar da ake tsammani daga gare su wajen jagorantar majalisar dattijai domin kare hakkin al’umma. A matsayinsu na shugabannin majalisar, ya kamata su kasance masu kare muradun kasa, ba kawai masu biye da duk wani abu da shugaban kasa ya gabatar ba.

Wannan yanayi na nuna cewa ba su da karfin gwiwar jagoranci, kuma hakan ya sa dole mu yi kira garesu su sauka daga mukamansu, domin bada dama ga wasu da za su iya fuskantar matsalolin da s**a addabi kasa da kuma daukar matakan gyara.

A wannan yanayi mai tsanani, Najeriya tana bukatar shugabanni masu hangen nesa da kishin kasa, wadanda za su tsaya tsayin daka wajen kare muradun talakawa, ba wadanda za su zuba ido don tabbatar da biyan bukatun wasu kalilan.

Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta duba wannan batu sosai, tare da tabbatar da cewa talakawa sun samu mafita daga wannan wahala ta tattalin arziki da rashin jagoranci nagari.

Dole mu yi magana, domin Najeriya ta fi kowa da komai muhimmanci a wajenmu!

16/11/2024

HIRA TA MUSAMMAN DA SHUGABAN NNPC MELE KYARI GAME DA SAMUN NASARAR KARIN HAKO DANYEN MAI DA KAMFANIN YA YI, DAGA GANGA 1.4 MILIYAN ZUWA 1.8 MILIYAN A KOWACCE RANA.

A YI SAURARO LAFIYA

WATA SABUWA: Ƙungiyar matasaɲ jam'iyyar APC ta jihar Jigawa ta yi kira da a kori Ministan tsároʻ, Badaru kan zargin cin ...
15/11/2024

WATA SABUWA: Ƙungiyar matasaɲ jam'iyyar APC ta jihar Jigawa ta yi kira da a kori Ministan tsároʻ, Badaru kan zargin cin dunduniyar jam'iyyar

Kungiyar matasan jam’iyyar APC da ke jihar Jigawa, ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba batun nadin ministan tsaro, Badaru Abubakar, saboda rashin gamsuwa da ayyukansa da kuma zargin rashin biyayya ga jam’iyyar da ma yi mata kafar ungulu.

Da yake jawabi ga ’yan jarida da masu Zàñga-zàñĝar a Dutse babban birnin jihar Jigawa a ranar Juma’a, kodinetan kungiyar, Ahmad Magaji Bashir ya ce abin da Ministan Tsaro ya yi, ya kawo cikas ga kokarin jam’iyyar APC tare da bata sunan jam’iyyar a Jigawa.

Mun nuna takaicin yadda Badaru ya gaza goyon bayan manufofin jam'iyyar APC a jihar da kuma yadda yake shinshina tare da muradin mara baya ga jam’iyyar adawa ta PDP a jihar.

Bashir ya zayyana korafe-korafe da dama da s**a hada da zargin rashin goyon bayan Badaru ga ‘yan jam’iyyar APC da kuma ra’ayin sa ga ‘yan PDP a jihar. Kungiyar matasan ta kuma yi karin haske kan rahotannin da ke nuna cewa an yi kaca-kaca da allunan tallace-tallacen jam’iyyar APC da ke dauke da hotunan Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban kasa Shettima da ake zargin akwai hannun ministan Badaru a ciki.

“Mun damu matuka game da rashin jajircewar ministan ga manufofin jam’iyyar APC da tsare-tsarenta, da muke takaicin hakan a tsakanin mu.

"Ayyukan nasa da alama sun saba wa muradun jam'iyyar a Jigawa da Nijeriya gaba daya."

Kungiyar ta bayyana damuwarta kan cewa kasancewar Badaru a cikin tafiyar Shugaba Tinubu na iya yin illa ga martabar APC a Jigawa da ma kasa baki daya, ta kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da ya gaggauta daukar matakin magance lamarin.

“Muna rokon Shugaba Tinubu ya sake duba nadin minista Badaru. Ci gaba da rawar da yake takawa a gwamnati na iya kawo cikas ga ayyukan jam’iyyar tare da kawo cikas ga kokarin hadin guiwarmu,” in ji kungiyar.

Kungiyar matasan ta jaddada kudirinta na mara wa gwamnatin shugaba Tinubu baya amma ta jaddada bukatar samun kwakkwaran jagoranci a cikin jam’iyyar APC domin dawo da kwarin guiwa da hadin kai a tsakanin mambobin jihar Jigawa.

Me zaku ce?

Za mu gama da Lakurawa nan ba da jimawa ba – RibaduMai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu...
14/11/2024

Za mu gama da Lakurawa nan ba da jimawa ba – Ribadu

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen kungiyar yan ta’adda da ake kira ‘Lukarawa’ a shiyyar Arewa maso yammacin nan ba da jimawa ba.

Ribadu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci shugaban kasa Tinubu a wajen bikin bude babban taron kwastam na shekarar 2024, ranar Laraba, a Abuja.

“Za mu fatattaki wadanda ake kira Lukarawa daga kasarmu. Za mu kunyata masu s**ar mu kuma zamu rufe bakunansu. Boko Haram da s**a addabi kasarmu a baya, yanzu tserewa suke. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu kasashe makwabta saboda basu da damar yin ta’addancin su a Najeriya” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa, alamun na ƙara nuna cewa al’amura na cigana da inganta ta fuskar tattalin arziki a ƙasar nan wanda kowa zai iya gani, inda ya ba da misali da yadda ake hako danyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da babban bankin Najeriya (CBN) ke yi a cikin irin wannan kokari.

“Hakar danyen mai ya kai ganga miliyan 1.8 a kowacce rana. sannan kuma an tsaftace babban bankin kasa; babu wanda ke ɗaukar kobo daga babban bankin. Mun yi alkawarin cewa za mu gyara kasar nan, kuma za mu yi hakan domin Shugaba Tinubu bai taba zama mutum mai gazawa ba,” inji shi.

"Aikin da ke gabanmu na bukatar taron-dangi ne, kuma ni ne ke jagorantar wannan gamayyar ma'aikatan a matsayina na shuga...
12/11/2024

"Aikin da ke gabanmu na bukatar taron-dangi ne, kuma ni ne ke jagorantar wannan gamayyar ma'aikatan a matsayina na shugabanku". -Shugaba Tinubu.

Bayanai masu mahimmacin da yan Nigeria ya kamata su sani akan "Tax Reform Bill" da shugaba Tinubu ya tura majalisa.Tax R...
11/11/2024

Bayanai masu mahimmacin da yan Nigeria ya kamata su sani akan "Tax Reform Bill" da shugaba Tinubu ya tura majalisa.

Tax Reform Bill wata hanyace da zata kawoma talakan Nigeria sauki a bagarori da dama.

Karanta Karin bayani akan Tax Reform Bill

Najeriya za ta jaddada goyon bayan ta kan ƴancin Falasdinu a taron ƙasashen musulmi da za a yi a RiyadhShugaba Bola Ahme...
09/11/2024

Najeriya za ta jaddada goyon bayan ta kan ƴancin Falasdinu a taron ƙasashen musulmi da za a yi a Riyadh

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron haɗin gwiwa na kasashen Larabawa da Musulunci da za a gudanar a Birnin Riyadh dake Saudi Arabiya dan tattauna batutuwan da s**a shafi gabas ta tsakiya.

Shugaba Tinubu zai jadada goyon bayan Najeriya kan yancin Falasɗinawa a taron wanda ya samu gayyatar sa daga Yarima Mohammed Bin Salman a birnin na Saudiyya.

Daga yan tawagar shugaban ƙasa akwai manyan jami'an Gwamnati da s**a haɗa da ministan harkokin wajen kasar Ambasada Yusuf Tuggar, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu; Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris; da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Mohammed Mohammed.

Ku kasance da Ministan Kula da Lafiya na Najeriya a cikin shirin "Primetime" na Arise TV tare da Charles Aniagolu da mis...
06/11/2024

Ku kasance da Ministan Kula da Lafiya na Najeriya a cikin shirin "Primetime" na Arise TV tare da Charles Aniagolu da misalin karfe 8:00 na daren yau.

Inda zai yi bayani kan irin namijin kokarin da s**a yi a karkashin gwamnatin tarayya.

Address

Wuse Ademola Adetokunbo Crescent
Abuja
900285

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa For Asiwaju posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa For Asiwaju:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Abuja

Show All