Karatu da Rubutun Hausa

Karatu da Rubutun Hausa Barka da shigowa Shafin Ka'idodin Rubutun Hausa. Zaure Na " Tambaya, Mabudin Sani. Hankali, Nazari Da Azanci... Kowa Yakan Iya Hada Su. Eh!
(10)

Amma Mutunci, Hakuri Da Adalci... Sai Nagari Kawai. Irin Mai Tausayi, Ladabi Da Alkunya Din Nan; Mai Dogaro Da Bin Ubangiji. Yana fi na, kuma ni ma ina fin shi. Shi ne abokin zama iya wuya kuma mukasanci abun tunawa a dukkannin takin rayuwa. Wanda kominshi abun burgewa ne da yabawa. Mai tafiya da takon gaskiya da maso cigaban Duk mauksanta. Gwanin iya hange da nazarin gaba a duk inda ya kasance. A

bun kwaikwayon da ke daidaituwa da wancaninshi. A bar shi, tamkar yin nesa da haske ne yayin duhu ya kewaye idanuwa. Irin duhun da ba ya barin zuciya ganin komi kuma ba mai karewa ba. Binshi sau da kafa tamkar bin madaidaiciyar hanya ne ganin yadda ya kebanta daga shirme da laifi. Sha jira kuma mai kira domin kau da kai daga laifuka iya kokari. Yana raina, kuma ni ma ina ranshi. Kuma mutum ne shi kaskantacce daga kowane irin girma kuma ba ya neman sa-hannun kowa. Ga shi mai ingantuwa ne daga darussan da wasu ke wargi da su. Da na halak, daga samon asali tushe mafi tsari da kulawa, mai duban gaske kuma mai k**anceceniya da mutanen farko wajen so da kishi. Mai sani domin sanarwa kuma mai taimako da ababen marmari masu kayatarwa. Kowa nashi ne kasancewar ba ya turin gefe. Mai wasiyantar da duniyoyi daban-daban duk da tashi daya ce kuma kadan. Arzutaccen da bai taba rasa abun cewa ba daga ilmomin rayuwa. Ba tauye kowa domin radin kanshi komi rintsi. Yana so na, kuma ni ma ina son shi. Ba daga litattafai ba, ko wasannin kwaikwayo ba ko kuma labaran duniya ba; a'a shi yana tafi da rayuwarshi ne cikin soyayya. Mai yiwuwa, wani ya ji k**ar sun yi k**a wani wajen to amma sau da yawa akan tsaya hutu yayin doguwar tafiya, shi kuma jingile ne kuma madugu. Mai tofi da albarka kuma sababben hakuri.

Adresse

Niamey

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Karatu da Rubutun Hausa publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Partager