Daga Yau Alhaji Dudu Rahama ba ɗan Adawa bane ,faɗar Alhaji Dudu a yayin sanarwar sa ta
canza sheƙa.
A jiya Asabar 12/11/22, Alhaji Dudu Rahama yayi sanarwar canza sheƙa daga jam'iyyar RDR Canji mai Adawa zuwa jam'iyyar PNDS TARAYYA Mai mulki .
A da ,Alhaji Dudu, fitaccen ɗan Adawa Ne wanda ya kwashe shekaru masu yawa yana yin ta,kuma babban Na hannun daman Mahaman Usmane Na jam'iyyar RDR.
Yayin da yake jawabinsa Na canza sheƙa da ya gudanar jiya a Zinder a gaban Manema labarai,Alhaji Dudu ya ƙara tabbatar da cewa ya bar adawa,kuma ya koma ɗan jam'iyyar PNDS Mai Mulki.Ko ta maka daɗi ko kar ta yi maka daɗi,ba abinda ya shamin kai a cewarsa.
Lamarin canza sheƙar na Alhaji Dudu ya ɗauki hankalin masu Nazarin siyasa,kamar yadda wani mai Nazarin siyasa a ƙasar ke cewa akwai yuwar shima mai gidan Na Dudu(Mahaman Usmane) ya bi Jam'iyyar Mai mulki amma ta ƙarƙashin ƙasa.
Jam'iyyar CPR Inganci ta ƙasum Moctar, Reshen Birnin Yamai, a yau Asabar 21/10/22 Ta gudanar da wani babban taron sabunta manbobin komitin jam'iyyar.
Dr Yacouba Ne aka zaɓa shugaban jam'iyyar na Da'irar birnin yamai.
A yayin wannan taron, shugaban jam'iyyar Na ƙasa Ƙasum Moctar ya gudanar wani jawabin zaburarwa , tare da ƙara ƙarfafa wa ya'yan jam'iyyar gwiwa.👇
wasu yan gundumar kwalo,ya'yan jam'iyyar Moden Lumana,Amin-Amin,da kuma pjp Dubara,sun canza sheka zuwa jam'iyya mai mulki PNDS Tarayya.
Jam'iyyar ta PNDS ta gudanar da wani babban taron marhabantarsu,tare da yi masu Albishir cewa,a cikin tafiyar ba sa da bambanci da daɗaɗɗun mabiya jam'iyyar.
Alƙali Mai shigar da ƙara ya gudanar da wani taron Manema labarai a ranar 26/03/22 domin Bama ƴan Jarida haske Dangane da mutanen da aka kama a yayin zanga-zangar da ta biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugaban Ƙasar a shekarar 2021.