Citizenship HAUSA

Citizenship HAUSA Sani 'Yancinmu shine neman ilmi...
(4)

Yaro yace ba zai je makaranta ba, tunda sun ki tayar da shi sallar Asubah. Labari mai cike da darasi.Wani yaro ne anyi m...
20/04/2024

Yaro yace ba zai je makaranta ba, tunda sun ki tayar da shi sallar Asubah.

Labari mai cike da darasi.

Wani yaro ne anyi masa wanka an shirya shi, ya ci abinci aka ce ya je makarantar boko, yace ba zai je ba. Aka ce me yasa? Yace saboda babana yaki tashina mu je sallar Asubah. Akayi-akayi da yaro ya je, yace wallahi ba zan je ba. In dai ana so ya je to sai dai a rika tashinsa a je sallar asubah da shi.

Washe gari, yaro aka tada shi aka tafi da shi masallaci bayan an dawo, aka shirya shi ya tafi primary. To, sai aka fara tara wadanda basu zo jiya ba, ana dukansu da bulala a hannu. Kafin azo kan yaro sai yaron yana cewa ba zaka iya duka na ba. Ashe malamin yana ji. Da ya matso sai yace da yaron me yasa kace ba zan iya dukanka ba? Yace domin nayi sallar Asubah acikin jam'i kuma na ji limamin yace duk wanda yayi sallar asubah acikin jam'i yana karkashin kariya da tsaron Allah mai girma mai daukaka. To, ta ya za'ayi ina da wannan kariya da tsaron a wurin Allah ka iya duka na? 😀😀 sai Malamin yace eh kwarai ba zan iya dukanka ba, ka tafi aji. 😀😀

WANE DARASI KA DAUKA ACIKIN LABARIN NAN.

01/04/2024

Masu gaggawa a addu'a ku saurara

01/04/2024

Shugaban wannan shafin bashi da lafiya, yana bukatar addu'o'inku.

31/03/2024

Amsa: Mun samu karin wasu ayoyi guda uku qadanda suke dauke da harafin Qaf ق har guda 10, sun zama ayoyi guda biyar kenan.

1. Baqara aya ta 246
2. Nisa'i aya ta 77
3. Ma'idah aya ta 27
4. Ali-Imran aya ta 181
5. Muzammil aya ta 20

Idan akwai wasu sai a kara mana a comment section.

31/03/2024

Surori nawa ne Makiyya da kuma nawa ne Madaniyya?

31/03/2024

Tambaya: Wace aya ce acikinta akwai harafin Qaf ق har guda goma acikinta? Kuma wace surah take? Kuma aya ta nawa?

30/03/2024

Ku taimaka mana ta hanyar inviting abokanku zuwa wannan shafin, da sharing content namu zuwa shafukanku.

FEDERAL GOVERNMENT GRANT.Ku cike wannan, ku cikewa 'yan uwanka da abokanku (LINK YANA COMMENT NA FARKO) 👇Tallafi ne da g...
30/03/2024

FEDERAL GOVERNMENT GRANT.

Ku cike wannan, ku cikewa 'yan uwanka da abokanku (LINK YANA COMMENT NA FARKO) 👇

Tallafi ne da gwamnatin tarayya za ta bayar kyauta ₦50k kamar irin wanda aka bayar na 'survival fund' a lokacin Buhari.

A tabbatar an cike komai daidai, BVN, NIMC, BANK DETAILS...

Allah ya bada sa'a

30/03/2024

Tambaya: "Kullu nafsin za'ikatul maut" ta zo guda nawa acikin Al-Qur'ani? Wace surori ne? kuma ayoyi ta nawa?

Ma Awuya Muhammad shine wanda ya lashe wata special gasa na sharing wata video a wannan shafinmu.Muna maka barka Malam M...
29/03/2024

Ma Awuya Muhammad shine wanda ya lashe wata special gasa na sharing wata video a wannan shafinmu.

Muna maka barka Malam Ma Awuya Muhammad.

Wadanda s**a yi nasarar gasar bazata 'Active Members' na wannan shafinmu mai albarka su ne kamar haka:1. Isah Ibrahim Ga...
29/03/2024

Wadanda s**a yi nasarar gasar bazata 'Active Members' na wannan shafinmu mai albarka su ne kamar haka:

1. Isah Ibrahim Gamawa 1GB

2. Zaharaddeen Sanusi da Mudaseer Ibrahim 1GB

3. Ma Awuya Muhammad 500MB

4. Mubarak Tijjani Kwa 500MB.

Mun turawa mutane 3 saura 2 saboda basu tura mana numbobinsu ba, don haka wadanda ba su bamu numbobinsu ba, sai su tura mana domin tura musu kyautarsu.

Mun gode! Ku cigaba da kasancewa da mu a wannan shafinmu mai albarka, akwai shirye shirye na musamman suna nan tafe.

29/03/2024

Mutane biyu da s**a fara yin comment da kalmar Citizenship Hausa a wannan post suna da kyautar 1GB ga kowannensu.

29/03/2024

Abin burgewa ne ka ga mata a fagen ilmin addini musamman Al-Qur'ani, Maa Shaa Allah 😍😍😍

SHAWARI KAN HANYOYIN GYARAN TILAWAN QURAN MAI GIRMA 1.  Maimaita kowani Rubui sau  adadi masu yawa kaman sau 50 ko 60 ko...
29/03/2024

SHAWARI KAN HANYOYIN GYARAN TILAWAN QURAN MAI GIRMA

1. Maimaita kowani Rubui sau adadi masu yawa kaman sau 50 ko 60 ko 70 ko sama da haka karatun yazama cikin Kulawa da Nitsuwa da kuma dalibi ya zama yanason yin karatun

2. Yin Sallan dare da izu daya ko biyu ko sama da haka cikin Kulawa da hadda tareda tadabburi da nitsuwa kar ayi gaggawa

3. Rubuta Qurani a Allo inda hali tareda sanin Qaidodin Rubuta Qurani da koyon rubutashi

4. ⁠Ikhtibaar ga dalibi a qalla duk sati sau daya ayi masa tambayoyi kaman 10 ko sama da haka, Sannan Yakamata ayi ikhtibaar wa dalibi cikin Qurani aqalla tambayoyi 300 kuma Kar yayi kuskure da yawa kuskuren yazama kadan sosai

5. ⁠Musaffa tsakanin mutum biyu ko sama da haka na wasu izuzzuka amma kar arinqa bata tilawa sonsamu ya zama babu kuskure kuma ayi karatu anitse sosai da kulawa da mutashabihaat

6. ⁠Yin Musabaqan Qurani da niyyan gyara Tilawa da kuma niyyan neman yardan Allah wajen Karatun Qurani da Naci da neman Shawarin Malamai kan hakan

7. ⁠Tasmiin kowani Izu a gaban Malamai kaman 10 ko sama da haka ayi karatun cikin Nitsuwa da tajwidi sonsamu kar ayi kuskure cikin kowani izu kuma karatu cikin Nitsuwa da tajwidi da kwadayin karatu

8. ⁠Kulawa da Mutashabihaat ( Ayoyi Masu K**a ) da banbancesu, rubutasu, da kuma yawan tunosu duk lokacin buqatan haka
9. ⁠Yawan Sauraron Karatun Quran cikin Kulawa da kuma niyyan gyara tilawa

10. Lizimtan Mushaf (Qurani) guda daya Na Karatu

11. ⁠Addua

Rubutawa
Yusuf Muhammad Dukku
16- Ramadan - 1445
26- March- 2024

Babu kauyanci da ya wuce mutum bai san Allah ba. -Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami
29/03/2024

Babu kauyanci da ya wuce mutum bai san Allah ba.
-Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami

08/12/2023

Karatun Al'Qur'ani daga bakin Gwani Abdulbasit Muhammad Inuwa Gombe

Digital Skills guda 5 ga Yan mata da Matan aure ya kamata su koya domin dogaro da kansu a gida.1. Graphic Design: ana sa...
28/11/2023

Digital Skills guda 5 ga Yan mata da Matan aure ya kamata su koya domin dogaro da kansu a gida.

1. Graphic Design: ana samu 5k+
2. Content writing: ana 10k+
3. Social Media Management: 100k+
4. Web Development: karamin aiki 70k
5. Online Teaching ko Tutoring: ana samu 30k zuwa sama ya danganta mutane nawa k**e son koyawa.

Duk wadannan skills din a gida zaku yi su, ba sai kun fita ba. Kuma ana samun alkhairai acikinsu.

Idan baku iya ba, ku nemi online classes ku koya awajen kwararru.

Domin cikakken bayani ku karanta a wannan link din a kasa, bayanin (Dr) Salisu Abdurrazak Saheel
https://www.facebook.com/100010721714972/posts/2037812576586113/?app=fbl

Note: Summary ne na bayanin Dr. Saheel Abdurazak

Sama da shekaru 50, Marigayi Sa'adu Zungur yayi wannan wa'azin a sigar Wake~ Matukar a arewa da karuwai,~ yan daudu dasu...
26/08/2023

Sama da shekaru 50, Marigayi Sa'adu Zungur yayi wannan wa'azin a sigar Wake

~ Matukar a arewa da karuwai,
~ yan daudu dasu da magajiya.
~ Da samari masu ruwan kudi,
~ Ga mashaya can a gidan giya.
~ Matukar yayan mu suna bara,
~ T**i da Loko-lokon Nijeriya.
~ Hanyar birni da na kauyuka,
~ Allah baku mu samu abin miya.
~ Sun yafu da fatar bunsuru,
~ Babu mai tanyonsu da dukiya.
~ Babu shakka yan kudu zasu hau,
~ Dokin mulkin Nijeriya.
~ In ko yan kudu sunka hau,
~ Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
~ A Arewa zumunta ta mutu,
~ Sai karya sai sharholiya.
~ Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
~ Malaman karya yan damfara.
~ Sai karya sai kwambon tsiya,
~ Sai hula mai annakiya.
~ Ga gorin asali da na dukiya,
~ Sai kace dan annabi fariya.
~ Jahilci ya ci lakar mu duk,
~ Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
~ Ya daure kafarmu da tsarkiya.
~ Bakunan mu ya sa takunkumi,
~ Ba zalaka sai sharholiya.
~ Wagga al’umma mai zata yo,
~ A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
~ Zaya sha kunya nan duniya “.
~ “Mu dai hakkin mu gaya muku,
~ Ko ku karba ko kuyi dariya.
~ Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
~ Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
~ Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
~ Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
~ Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
~ waken sa mai suna “Arewa
~ Jamhuriya ko Mulukiya”
Allah Yajikan Malam Saadu Zungur
Allah kayimasa Rahama amin amin.

SABUWAR APP NA SAYAR DA DATA MAI ABUN MAMAKI.Sabuwar Application na sana'ar siye da siyarwa na data, recharge card da sa...
11/08/2023

SABUWAR APP NA SAYAR DA DATA MAI ABUN MAMAKI.

Sabuwar Application na sana'ar siye da siyarwa na data, recharge card da sauran services, ta bayyana a Playstore, da kuma Website a 9 ga watan August 2023.

Farko zaku shiga wannan Link ɗin kuyi register (Sign Up) ta website ɗinmu👇

https://salfat.com.ng/user/signup?ref=arabo48

Bayan kun kammala register sai kuje Playstore ku sauke Mobile Application namu mai suna "Salfat" ko kuma ku shiga ta wannan Link ɗin domin sauketa a wayoyinku👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.salfat

Idan kun samu wani tangarda zaku iya tuntuɓar Customers Care ta WhatsApp a waɗannan lambobin:
09065605219
07048961623
08065516999

Application ɗin tazo da tsaruka kamar haka:

1. Zakayi kasuwancin data da wannan Application namu cikin farashi mai sauƙi, zaka samu riba daidai gwargwado.

2. Zakaga Referral Link naka a Dashboard ɗinka, wannan Referral Link ɗin yanada matiƙar amfani domin dashi zaka iya samun sama da 5k a rana ɗaya

Yadda abun yake shine, duk wanda yayi register ta wannan Referral link ɗin naka har ya siya data ko ya siyar da data to kanada Commission, abin nufi anan shine idan ya siya Data 1Gb ko 500gb, 10gb kanada kason da zaka samu na kuɗi, idan zai siya data sau 100 a rana duk Transaction ɗin da zaiyi sai kasamu Commission ɗinka, haka zalika idan waɗanda s**ayi register ta link ɗinka sun kai mutum 100 kuma suna siyen data a Application ɗin to a cikin mutum ɗari ɗin nan ace ko wannen su zai siya data ko zai siyar da data 1Gb kawai a rana ɗaya, zaka samu commision ɗinka mai nauyi saboda adadin mutanen da yawa bare kuma a rana ɗaya dai mutum 100 kasan data da zasu siya sai tafi 1Gb, idan wancen ya siyar da 1Gb, wancen ƙila 10Gb, ya siyar wancen kuma ƙila 20Gb dukkansu sai kasamu Commission ɗinka.

Wayarka ko a kunne ko a kashe zaka dinga samun kuɗi ko da ba ka sayar da data.

Ku hanzarta... A dama da ku.

AMFANIN CHATGPT1. Ƙirƙirar daftarin aiki: Ana iya amfani da ChatGPT don samar da takardu kamar rahotanni, gabatarwa, da ...
11/08/2023

AMFANIN CHATGPT

1. Ƙirƙirar daftarin aiki: Ana iya amfani da ChatGPT don samar da takardu kamar rahotanni, gabatarwa, da shawarwari ta hanyar shigar da wasu mahimman bayanai kawai da barin ChatGPT ta yi sauran.

2. Amsa Imel: Ana iya amfani da ChatGPT don samar da ingantattun amsoshi na imel, adana lokaci da tabbatar da cewa ana sarrafa mahimman hanyoyin sadarwa cikin sauri da ƙwarewa.

3. Data Analysis: ChatGPT na iya yin nazarin ɗimbin bayanai da gano mahimman tsari da fahimi, tare da taimakawa ƙungiyoyi don yin mafi kyawun zaɓin da aka sarrafa bayanai.

4. Harkokin Kasuwanci: Haka nan ana iya amfani da ChatGPT don haɓaka sabbin ra'ayoyin kamfani ta hanyar ba da wasu bayanai game da masana'antu da kasuwa da barin ChatGPT don samar da ra'ayoyi da ra'ayoyi masu zuwa. Wannan na iya taimaka wa 'yan kasuwa da shugabannin kasuwanci don fito da sabbin kayayyaki, ayyuka, da himma.

5. Code Generation: ChatGPT yana ba da damar ƙirƙirar Coding, gano kuskure, da gyarawa. Ta hanyar neman ƴan bayanai game da ayyukan da ake buƙata, zai iya samar da lambar da za a iya amfani da ita wanda mai haɓakawa zai iya gyarawa da haɓakawa. Ta hanyar gano lahani na gama gari da lahani a cikin codeing da kuma ba da jagora kan yadda ake gyara su, ChatGPT kuma ana iya amfani da su don cire shirye-shirye.

6. Koya ma yarurruka (languages): Chatgpt tana jin shahararrun yarurruka da dama. Za ka iya ce mata ta rubuta ma wake akan soyayya da sunan masoyan kuma ta rubuta ma da Larabci ko da Yaren da kake so. Kai hatta Li'irabi Chatgpt tana yi.

7. Rubuta littattafai: Chatgpt za ta taimaka maka wajen rubuta littafi ko wani project. Har tables of content tana yi.

8. Lissafi: kowace lissafi ce zata warware ma acikin dakikai 5.

Kaɗan kenan daga aikin Chatgpt na OpenAI.

Ku biyo ni domin jin yadda za'a yi rijista da fara aiki da ita a kyauta.

✍️ Arabo M Auwal

𝗠𝗘𝗡𝗘𝗡𝗘 𝗖𝗛𝗔𝗧𝗚𝗣𝗧?𝗰𝗵𝗮𝘁𝗴𝗽𝗧  na'ura ne wanda 𝐎𝐏𝐄𝐍𝐀𝐈 ya haɓaka kuma aka ƙaddamar a cikin Nuwamba, shekara ta 2022. An gina shi...
04/08/2023

𝗠𝗘𝗡𝗘𝗡𝗘 𝗖𝗛𝗔𝗧𝗚𝗣𝗧?

𝗰𝗵𝗮𝘁𝗴𝗽𝗧 na'ura ne wanda 𝐎𝐏𝐄𝐍𝐀𝐈 ya haɓaka kuma aka ƙaddamar a cikin Nuwamba, shekara ta 2022. An gina shi a saman GPT-3.5 na OpenAI da GPT-4 na iyalai na manyan nau'ikan harshe kuma an daidaita shi sosai (hanyar canja salon koyo ) ta amfani da dabaru na kulawa da ƙarfafawa. [𝐖𝐈𝐊𝐈𝐏𝐄𝐃𝐈𝐀].

An ƙaddamar da ChatGPT azaman samfuri a ranar 30 ga Nuwamba, 2022, kuma cikin sauri ya jawo hankali don cikakkun amsoshinsa da fayyace amsoshinsa a faɗin fannonin ilimi da yawa. Rashin daidaiton gaskiyar sa, duk da haka, an gano shi zaman babban koma baya. Bayan fitowar ChatGPT, an kiyasta ƙimar OpenAI akan US$29 biliyan a 2023. (𝐰𝐢𝐤𝐢𝐩𝐞𝐝𝐢𝐀 )

Anyi ta ne don ta saukaka mana wajen yin bincike.

A takaice dai Chatgpt wata manhaja ce da zaka yi mata kowace iriyar tambaya za ta amsa maka acikin dakikai kaɗan.

Ku biyo ni a rubutu na gaba, don jin amfanin ta da yadda ake buɗe wa da fara aiki da ita

✍️ Arabo Modibbo

TINUBU YA NAƊA NUHU RIBADU A MATSAYIN MAI BASHI SHAWARA A HARKOKIN TSARO (NSA).Tinubu ya zabi Ribadu tsohon Babban shuga...
03/06/2023

TINUBU YA NAƊA NUHU RIBADU A MATSAYIN MAI BASHI SHAWARA A HARKOKIN TSARO (NSA).

Tinubu ya zabi Ribadu tsohon Babban shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta (EFCC) a matsayin NSA. Malam Nuhu Ribadu ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabo shi a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), wata majiya mai tushe ta bayyana hakan.

Hukumar ta NSA tana aiki ne a matsayin babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da hada kan hukumomin tsaro daban-daban, da samar da bayanan sirri, da kuma tsara tsare-tsare na magance kalubalen tsaron kasar nan, an zabi Sufeto Janar na ‘yan sanda mai ritaya a kan wasu ‘yan takara biyu, tsohon ministan Cikin gida da tsohon babban hafsan soji, Janar Abdulrahman Dambazau (rtd), da kuma babban darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar. Tinubu ya tantance dukkan ‘yan takarar guda uku kafin ya zabi Ribadu, wanda ake yi wa lakabi da kwarewa a fannin tsaro da tabbatar da doka da oda.

Matsayin NSA yana buƙatar mutum wanda zai iya tafiyar da al'amuran tsaro masu rikitarwa da kuma ba da shawara mai kyau ga shugaban kasa. Tinubu na ganin irin kwarewar Ribadu da sadaukar da kai ga aikin gwamnati, duk kuwa da kasancewarsa tsohon dan sanda, wanda hakan na iya yiwuwa a ce masa mukamin NSA ya kasance a bisa al’adar mutanen da ke da tarihin soja.

01/06/2023

“Kada ka ji bakin ciki idan mutum ya fifita wani a kanka, domin ba za ka iya gamsar da biri cewa zuma ta fi ayaba daɗi ba.”

Wacce sana'a ce Dalibin Jami'a (musamman dalibin Injiniyarin da likitanci) zai yi wanda ba zai yi distracting nashi sosa...
19/05/2023

Wacce sana'a ce Dalibin Jami'a (musamman dalibin Injiniyarin da likitanci) zai yi wanda ba zai yi distracting nashi sosai ba a karatunsa kuma baya buƙatar jari sosai.

Kowa ya bada ta sa da ya sani domin duka mu amfana.

AMA Telecom Plus tana saida Data a farashi mai sauki.MTN da Airtel Networks500Mb N1501GB N2502GB N5003GB N8005GB N130010...
05/05/2023

AMA Telecom Plus tana saida Data a farashi mai sauki.

MTN da Airtel Networks
500Mb N150
1GB N250
2GB N500
3GB N800
5GB N1300
10GB N2600

Glo Network
1GB N300
2GB N600
3GB N900
5GB N1500
10GB N3000

9Mobile Network
1GB N350
2GB N750
3GB N1100
5GB N1800
10GB N3500

Sannan tana biyan NEPA Bill, Star time, Dstv, da Gotv.

Domin Sayan Data kira wannan layukan 08111661087 ko 07037337528 ko 08088985696 ko kuma ta lambar WhatsApp 07037337528 ko kuyi masa magana ta Facebook nashi mai Suna Arabo Modibbo. Mun gode.

BREAKING: INEC declares Governor Fintiri of Adamawa State re-elected after a dramatic poll. The PDP candidate scored 430...
18/04/2023

BREAKING: INEC declares Governor Fintiri of Adamawa State re-elected after a dramatic poll. The PDP candidate scored 430,861 votes to defeat APC's Aisha 'Binani' Dahiru who got 398,738.

Ƙarin Bayani Kan Zaman INEC Na Yau Talata.A zaman ganawar hukumar zabe mai zan kanta ta kasa da s**ayi a yau 18 ga watan...
18/04/2023

Ƙarin Bayani Kan Zaman INEC Na Yau Talata.

A zaman ganawar hukumar zabe mai zan kanta ta kasa da s**ayi a yau 18 ga watan Afrilun 2023, wanda s**a tattauna kan batun zaben Adamawa, hukumar ta cimma matsaya kamar haka:

1. Hukumar Zabe ta rubuta wasika ga Inspecta General na Yan Sandan Nigeriya cikin gaggawa da yayi bincike tare da gurfanar da Commissioner Zaben Jahar Adamawa Br Hudu Yunusa Ari.

2. Sannan hukumar zaben ta bukaci Secretary Gwamnatin Tarayya daya ja hankalin mahukunta kan halayyar Commissioner zaben jahar Adamawan, domin ɗaukar mataki akan shi.

3. A karshen zaman hukumar Zaben ta cimma matsayar cigaba da tattara sakamakon zaben jahar Adamawa a duk lokacin da baturen zaben jahar ya ayyana.

Fassara: Comrd Mubarak Aliyu Sabo Yaro

© INEC

Ta Leƙo Ta Koma A Adamawa...Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana cewa anja an hakalinta akan abinda wani Jami'inta ya...
16/04/2023

Ta Leƙo Ta Koma A Adamawa...

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana cewa anja an hakalinta akan abinda wani Jami'inta yayi a jihar Adamawa na bayyana sakamakon zaɓe duj kuwa da yake cewa ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.

Hukumar zaɓen ta INEC ta bayyana cewa abinda baturen zaɓe ya bayyana bai Inganta ba, dan haka an dakatar da bayyana sakamakon zaɓen kuma an gayyace su zuwa Offishin Hukumar dake Abuja da gaugawa.

Za'a Bayyana Sakamakon bayan anyi bincike.

Dole Sai Aishatu Binani Ta Lashe Duka Kuri'un Da Ake Sake Yin Zabensu Yau Kafun Tayi Nasarar Zama Gwamnan Jihar Adamawa ...
15/04/2023

Dole Sai Aishatu Binani Ta Lashe Duka Kuri'un Da Ake Sake Yin Zabensu Yau Kafun Tayi Nasarar Zama Gwamnan Jihar Adamawa

✍️ Comr Abba Sani Pantami

A zaben Inconclusive da ake gudanarwa yau a jihar Adamawa da wasu jihohin dole sai Aishatu Binani ta lashe sama da kaso 90 na kuri'un da ake gudanar da zaben kafun ta cike gurbin kuri'un da Gwamna Fintiri yake bata.

Bayan ta maye gurbin kuri'un da ake bata sannan sai a fara lissafin yawan kuri'un da za ta bashi kafun ta lashe zaben zama Gwamnan jihar.

A zaben da ya gabata Aishatu Binani tana da kuri'u 390,275 shi kuma Gwamnan jihar ya nada kuri'u 421,524 dai-dai.

Gwamna Fintiri ya bawa Binani tazarar kuri'u 31,249 inda a yau ake sake zaben Mutane 37,016 dai-dai.

Cikin mutane 37,016 da ake sake zaben su ba lallai ne dukkansu kowa ya fito ba, wasu sun rasu wasu katinsu ya bata wasu kuma haka kawai ba zasu fito zaben ba.

Akallah ace mutane 35,000 sun fito zaben to dole sai Binani ta lashe duka kuri'un wa 'yanda s**a fito zaben kafun tayi Nasara, wanda nida kai munsan abune mai matukar wahala duba da Gwamna mai karfin iko da yake kan mulki ne ake fafatawa dashi.

Don haka masu tada jijiyan wuya akan Binani zata lashe zabe suma daina tun da wuri, duk da munsan Allah ne yake bada mulki amma akwai abunda kai da ka gani kasan dole a karbi kaddara akanshi.

Dan shekara sha hudu 14 ne ya zo na daya a Gasar Al-Qur'ani ta duniya na Dubai na bana Wanda aka gama sati daya da ya wu...
10/04/2023

Dan shekara sha hudu 14 ne ya zo na daya a Gasar Al-Qur'ani ta duniya na Dubai na bana Wanda aka gama sati daya da ya wushe, mai suna Saleh Ahmad Takrim Dan kasar Bangladesh.

Address

Yola

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Citizenship HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Citizenship HAUSA:

Videos

Share