Arewa Daily Hausa News

Arewa Daily Hausa News Domin samun sahihan labarai daga ko ina a fadin duniya, K**a daga labarai duniya, wasanni dama sauran su.

Ɗan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar ƙarfafa gwiwa kan yaƙi da cin hanciAbdulazeez Ganduje, wanda shi ne babban ɗan tsho...
17/04/2024

Ɗan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar ƙarfafa gwiwa kan yaƙi da cin hanci

Abdulazeez Ganduje, wanda shi ne babban ɗan tshohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya kai wa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci Muhuyi Magaji Rimingado.

Majiya mai karfi da tabbatarwa da jaridar DAILY NIGERIAN Hausa cewa Abdulazeez ya goyi bayan kai mahaifinsa gaban kuliya bisa zargin cin hanci da rashawa.

Kuma majiyar ta ce ya nuna ɓacin ran sa bisa cire sunansa da mahaifinsa ya yi ba da izininsa ba daga cikin daraftocin ɗaya daga cikin kamfanunkan da ake zargi da handame kuɗin al’umma.

~Daily Nigeria Hausa

Za'a Ɗauki Azumin Shekara Mai Zuwa A Ranar 1-3-2025 Kuma Azumi 29 Za'a Yi Bisa Tafiyar Duniyar WataDaga Adamu Ya'u Dan A...
17/04/2024

Za'a Ɗauki Azumin Shekara Mai Zuwa A Ranar 1-3-2025 Kuma Azumi 29 Za'a Yi Bisa Tafiyar Duniyar Wata

Daga Adamu Ya'u Dan America

Ranar 29-2-2025 ne za'a fara duban fari a kasar saudiya da Nigeria a ranan ne bayan faduwar rana a kasar saudiyya a ranar jumma'a din hasken watan ramadan ɗin zai kasance (0.5%), ya kai yadda telescope 🔭 zai iya gani cikin Sauki, idan akwai yanayi mai kyau.

Haka zalika a Nigeria kuma bayan faduwar rana hasken sa zai kasance (0.7%) ya karu da digo biyu akan na kasar saudiyya, saboda bambancin awa 2 tsakanin faduwar ranan su.

Ranar duban fari na neman jinjirin watan shawwal fa? ranar 29 ga watan ramadan din kuma bayan faduwar rana a saudiyya akwai jinjirin watan shawwal hasken sa zai kasance (0.1%), a Nigeria kuma hasken sa zai kasance (0.2%).

Hakan na nuna cewa akwai dama na yin azumi 29 a shekara mai zuwa idan mahukunta s**a yarda da ganin jinjirin wata a wannan dan karamin hasken sa.

Da fatan Allah ya kaimu, ya sa muna cikin masu rai da lafiya a lokacin, da fatan Allah ya karba mana ibadunmu baki daya ameen summa ameen.

"Na k**a matata da laifin Dan malele Nayi hakuri na cigaba da Zaman aure da itaAn tura min video batsa da matata Tayi da...
14/04/2024

"Na k**a matata da laifin Dan malele Nayi hakuri na cigaba da Zaman aure da ita

An tura min video batsa da matata Tayi da kanta, Akan in biya 1 million Ko a saka a duniya nayi hakuri Na cigaba da zaman aure da ita.

Na k**a matata da cin Amanata da dan uwana Nayi hakuri na cigaba da Zan aure da ita

Idan nayi musu kazafi Allah ya Tona min asiri tun a duniya Ku gaya min maza nawa ne masu imagine Da zasu iya hakuri k**ar yadda nayi

Idan kuna bukatar shedu Ku rubuta min witness a comment section

~ Rubutun Adam A Zango kan dalilin sakin matan sa

Meye ra'ayin ku?

14/04/2024

YANZU-YANZU: Kasashen duniya da s**a hada da Saudiyya da Rasha da kuma Qatar sun yi kira ga Iran da Isra'ila da su mayar da wukakensu cikin kube su rungumi zaman lafiya, bayan da Iran ta kai wasu jerin hare-hare ga Isra'ila a cikin daren jiya.

lran ta kaddamar da harin rokoki masu linzami zuwa cikin Kasar l$ra'iIaYakin ya canza sabon salo kenanYanzu Amerika zata...
13/04/2024

lran ta kaddamar da harin rokoki masu linzami zuwa cikin Kasar l$ra'iIa

Yakin ya canza sabon salo kenan

Yanzu Amerika zata shiga don ta taya l$ra'iIa yaki

Kasar Rasha ita ma zata shiga don ta taya Iran yaki

DA DUMI-DUMIKotu ta daure Shaharerren Dan Daudu nan Bobrisky Wata 6 a Gidan Yari ba zabin biyan Tara.
12/04/2024

DA DUMI-DUMI

Kotu ta daure Shaharerren Dan Daudu nan Bobrisky Wata 6 a Gidan Yari ba zabin biyan Tara.

YANZU- YANZU:Tsohon ministan kimiyya da fasaha a tsohuwar gwamnatin Buhari Obonnaya Onu ya rasu.
11/04/2024

YANZU- YANZU:Tsohon ministan kimiyya da fasaha a tsohuwar gwamnatin Buhari Obonnaya Onu ya rasu.

An gudanar da Sallar Idi a kasar Dubai, Daular Larabawa.
10/04/2024

An gudanar da Sallar Idi a kasar Dubai, Daular Larabawa.

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Saratu Gidado wadda ta fi shahara da suna Daso ta rasu ne cikin bacci, k**ar yadda ...
09/04/2024

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Saratu Gidado wadda ta fi shahara da suna Daso ta rasu ne cikin bacci, k**ar yadda majiyoyi daga dangi da iyalanta s**a tabbatar

Muna fatan Allah Ya gama rai da rahamarSa.

Yadda al'ummar Musulmi a ƙasar Nijar sun gabatar da ƙaramar Sallah biyo ganin jinjirin watan Shawwal.
09/04/2024

Yadda al'ummar Musulmi a ƙasar Nijar sun gabatar da ƙaramar Sallah biyo ganin jinjirin watan Shawwal.

Yanzu haka da sanyin safiyar yau Talata, mabiyan Sheikh Musa Lukuwa Sokoto sun cika ciki da wajen masallacin shi domin g...
09/04/2024

Yanzu haka da sanyin safiyar yau Talata, mabiyan Sheikh Musa Lukuwa Sokoto sun cika ciki da wajen masallacin shi domin gudanar da idin karamar Sallah.

Ba a Ga Watan Sallah A Najeriya Ba Inji Fadar Sarkin MusulmiKwamitin duban wata na fadar mai martaba Sarkin Musulmi Muha...
08/04/2024

Ba a Ga Watan Sallah A Najeriya Ba Inji Fadar Sarkin Musulmi

Kwamitin duban wata na fadar mai martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ba a samu ganin jinjirin watan Shawwal ba a yau 29 ga watan Ramadan.

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa Sambo Wali Junaidu ta ce Sarki Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya ya amince da rahoton kwamitin.

Saboda haka ya yi matsaya cewa watan Ramadan zai cika kwanaki 30 kuma ranar Laraba 10 ga watan Afrilu, ita za ta kasance 1 ga watan shawwal kuma ranar sallah karama a Najeriya

Ba wannan ne karon farko da ake yin Azumi talatin ba a Najeriya.

✍️ KBC Hausa

DAƊUMI-ƊUMI: Dr. Idris Dutsen Tanshi ya koma garin Bauchi, inda yanzu haka dandaz0n almajiransa s**a fito d0min tarbansa...
08/04/2024

DAƊUMI-ƊUMI: Dr. Idris Dutsen Tanshi ya koma garin Bauchi, inda yanzu haka dandaz0n almajiransa s**a fito d0min tarbansa

Wane fata zaku yi masa?

YANZU-YANZU: Saudiyya ta fitar da sanarwa cewa bata ga Jinjirin Watan Shawwal ba, din haka sallah ranan laraba zai kasan...
08/04/2024

YANZU-YANZU: Saudiyya ta fitar da sanarwa cewa bata ga Jinjirin Watan Shawwal ba, din haka sallah ranan laraba zai kasance a kasar.

Akwai yanayi mai kyau na iya ganin jinjirin wata a yankin Arewa da Yammaci na kasar Saudiyya, inji masu kula da ganin ji...
08/04/2024

Akwai yanayi mai kyau na iya ganin jinjirin wata a yankin Arewa da Yammaci na kasar Saudiyya, inji masu kula da ganin jinjirin watan.

YANZU-YANZU: hotuna daga Tumair inda ake cigaba da binciken jinjirin watan Shawwal a kasar Saudiyya.Ku cigaba da bibiyan...
08/04/2024

YANZU-YANZU: hotuna daga Tumair inda ake cigaba da binciken jinjirin watan Shawwal a kasar Saudiyya.

Ku cigaba da bibiyan shafin mu domin samun sahihan labarai akan ganin jinjirin watan Shawwal din.

Hotuna daga wasu tituna na birnin madina, bayan kammala addu'a ta Al'qur'ani mai girma acikin wannan dare.
07/04/2024

Hotuna daga wasu tituna na birnin madina, bayan kammala addu'a ta Al'qur'ani mai girma acikin wannan dare.

Duk wanda yayi Sallah a ranar Talata yayi Sallah a cikin watan Ramadana tsundum, don haka kaffara ta k**ashi sai ya biya...
07/04/2024

Duk wanda yayi Sallah a ranar Talata yayi Sallah a cikin watan Ramadana tsundum, don haka kaffara ta k**ashi sai ya biya Azumi 60, Inji masanin taurari Sheikh Salihu.

Sheikh Salihu, ya kara da cewa, ba yadda za'a yi aga wata a lokacin faduwar rana domin ko na'ura ma ba zata iya hango jaririn watan ba.

Wani rikici irin na siyasa ya hudo kai a jihar Kaduna da ke tsakiyar Najeriya, bayan da Gwamnan Jihar Uba Sani ya ce gwa...
31/03/2024

Wani rikici irin na siyasa ya hudo kai a jihar Kaduna da ke tsakiyar Najeriya, bayan da Gwamnan Jihar Uba Sani ya ce gwamnatinsa ba za ta iya biyan ma'aikata albashi ba saboda gagarumin bashin da ya gada daga Malam Nasir El-Rufa'i

Yayin wani taro da ya gudana a ranar Asabar a Kaduna, Uba Sani ya ce ya gaji bashin dala miliyan 587 kwatankwacin naira biliyan 85 ga kuma kudin kamfanonin 'yan kwangila 115.

Mutane 8 da rundunar sojin Najeriya take nema ruwa-jallo bisa zarginsu da hannu a halaka jami'an ta 17 a Delta.Ana baku ...
28/03/2024

Mutane 8 da rundunar sojin Najeriya take nema ruwa-jallo bisa zarginsu da hannu a halaka jami'an ta 17 a Delta.

Ana baku cigiya Jama'a koda Allah yasa kungansu😡

Ɗan wasan Real Madrid da Brazil, Vinicius kenan a lokacin da ya fara zubar da hawaye bayan wani ɗan jarida ya yi masa ta...
25/03/2024

Ɗan wasan Real Madrid da Brazil, Vinicius kenan a lokacin da ya fara zubar da hawaye bayan wani ɗan jarida ya yi masa tambaya game da wariyar launin fata da yake fuskanta.

Vinicius ya ce wariyar na rage masa sha'awar taka leda.

SHIN ARTIFICIAL SWEETENERS NA DA ILLA?A wannan hali na tsaɗar rayuwa, mutane da dama sun koma amfani da artificial sweet...
25/03/2024

SHIN ARTIFICIAL SWEETENERS NA DA ILLA?

A wannan hali na tsaɗar rayuwa, mutane da dama sun koma amfani da artificial sweetener a maimakon s**ari wajen haɗa abinci da abun sha da ake bukatar zaƙi a ciki.

Hasali ma, tun kafin mu samu kanmu a wannan yanayin, mun daɗe muna amfani da sweeteners ba tare da mun sani ba, domin kamfanonin abinci da dama da shi suke amfani wajen haɗa lemukan kwalba, sabulun goge baki (toothpaste), magunguna masu zaƙi k**ar Vitamin C da dai sauransu

Dayawa daga cikin artificial sweeteners suna bayarda ɗanɗanon zaƙi ne kawai ba tare da sun ƙara yawan s**ari na jikin mutum ba. A dalilin haka ne masu ciwon suga, da musu teɓa s**an yi amfani da shi.

Shin yana da illa?

Amfani da sweetener yakan tsananta waɗansu matsaloli na lafiya k**ar phenylketonuria da waɗansu nau'ikan ciwon ciki. Duk da ana alaƙantawa da waɗansu matsaloli bacin wannan, ba a tabbatar da su ba tukunna. Har ila yau masu bincike suna kan zurfafa bincike game da amfaninsa da illolinsa, amma a halin yanzu likitoci sun bayar da shawara da ayi kaffa-kaffa wajen amfani da shi.

Likita24

Cikin wata sanarwa da NAHCON ta fitar mai dauke da sa hannun jami'ar hulda jama'a ta hukumar Fatima Sanda Usara NAHCON t...
24/03/2024

Cikin wata sanarwa da NAHCON ta fitar mai dauke da sa hannun jami'ar hulda jama'a ta hukumar Fatima Sanda Usara NAHCON ta yi Karin Naira milyan Daya da dubu dari tara kan milyan hudu da rabi da ta sanar a baya .

NAHCON ta ce karin ya samu ne sak**akon tashin Dala da aka samu daga dari takwas zuwa dubu da hudu.

TIRƘASH: Wata Kîristá ta tsinci kanta a asibiti bayan ta suma sau Biyu kafin karfe 4 na rana daga gwada yin azumin Ramad...
21/03/2024

TIRƘASH: Wata Kîristá ta tsinci kanta a asibiti bayan ta suma sau Biyu kafin karfe 4 na rana daga gwada yin azumin Ramadan

Wata kirista Eniola Fagbemi wacce ke auren wani músulmi a Kudu ta yi kurarin cewa azumin musulmi bashi da wuya tunda suna yin sahur kuma su sha ruwa lokacin magriba, don haka tace za ta jaraba don ta tabbatar masa,

Mahanga ta ruwaito Sai dai bayan Eniola ta yi sahur wajajen 4:30 na asuba tun wajen karfe 12 na rana ta fara fita hayyacinta, kan kace kwabo ta suma sau Biyu wajajen ƙarfe 4 na yamma ba arziki aka kwashe ta sai asibiti,

Allah ya taimaka an ceto rayuwar ta a asibitin Saanu Hospital dake garin Mokola.

17/03/2024

Munayi Muku Barka Da Shan Ruwa Daga Nan Shafin Arewa Daily Hausa News Da Meh kukayi Bude Baki Yau?

A gasar cin kofin zakarun nahiyar turai,Kungiyar kwallon kafa ta Man City, dake rike da kambun gasar zata fafata da Kung...
15/03/2024

A gasar cin kofin zakarun nahiyar turai,Kungiyar kwallon kafa ta Man City, dake rike da kambun gasar zata fafata da Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid,a wasan daf da kusa da na karshe,wato Semi final wace kungiya kuke gani zata samu nassara a wannan karon?

Man city dai itace ta doke Real Madrid a irin wannan mataki a shekarar 2023, kuma ta dauki gasar.

Wace kungiya kuke gani zatayi nassara akan abokiyar karawar tata? Kasancewar kowacce a cikinsu tana kokari a wannan Kakar?

10/03/2024

Sanarwa da yake fitowa daga commitee neman wata na Nigeria 🇳🇬 shine har zuwa yanzu babu labarin kallon sabon watan na Ramadan a fadin kasar.

Ku cigaba da bibiyan shafin mu domin samun sahihan labari akan kallon sabuwar watan ta Ramadan.

10/03/2024

YANZU-YANZU: Anga jinjirin watan Ramadan a kasar Saudiyya.

Kwamitin duba wata na kasar Saudiyya sun fara shirya wurinsu tsaf, domin fara duba jinjirin watan Ramadan Anjima da yamm...
10/03/2024

Kwamitin duba wata na kasar Saudiyya sun fara shirya wurinsu tsaf, domin fara duba jinjirin watan Ramadan Anjima da yamma.

05/03/2024

Wani irin yanayi kuka shiga yayin da ku kaji shafin sada zumunta ta Facebook ta dauke?

Address

Yola

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Daily Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Daily Hausa News:

Share



You may also like