Gaskiya online

Gaskiya online Wannan shafin mun budashi ne domin kawo muku muhimman labarai na gaskiya masu asali da kuma tushe.

Tinubu ya naɗa Olayemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan CBNShugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sunan Dr. Ola...
15/09/2023

Tinubu ya naɗa Olayemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan CBN

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sunan Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) na tsawon shekara biyar, da zarar Majalisar Dattijan ƙasar ta amince da shi.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, yau Juma'a.

Bayanin ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ne bisa dogaro da sashe na 8 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007, wadda ta bai wa shugaban ƙasar karfin ikon naɗa shugaba da mataimaka huɗu na Babban Bankin.

Sanarwar ta kuma bayyana sunayen wasu mutane huɗu da shugaban ya amince da su domin naɗawa a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin na Najeriya.

Mataimakan su ne:

(1) Mrs. Emem Nnana Usoro

(2) Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo

(3) Mr. Philip Ikeazor

(4) Dr. Bala M. Bello

Shugaban ya buƙaci waɗanda aka naɗan su mayar da hankali wajen aiwatar da muhimman sauye-sauyen da aka ɓullo da su a bankin a ƙoƙarin gwamnatinsa na sake fasalin tattalin arziƙin ƙasar.

A watan Yunin wannan shekara ne shugaban ƙasar ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ƙasar ta ce an dakatar da Emefiele ne ne domin gudanar da bincike da kuma kasancewa wani ɓangare na ƙoƙarin sauya fasalin harkokin kuɗi a ƙasar.

Kwanaki kaɗan bayan dakatar da shi ne rundunar tsaron ciki ta ƙasar, DSS ta tabbatar da k**awa tare da tsare tsohon gwamnan babban bankin.

DSS ɗin ta kuma gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa tuhumar sa da laifuka daban-daban.

Kai Tsaye: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasar 2023A yau Laraba, 6 ga Satumba, 2023, za a yanke h...
06/09/2023

Kai Tsaye: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasar 2023

A yau Laraba, 6 ga Satumba, 2023, za a yanke hukunci a kan karar shugaban kasa da 'yan takaran PDP, LP da APM su ka shigar.

Atiku Abubakar da Peter Obi ba su yarda da nasarar da Bola Tinubu ya samu ba, su na kalubalantar jam'iyyar APC da INEC a kotu.

Za a haska zaman kotun a gidajen talabijin kasar nan, kuma an ji cewa ba a bukatar ganin kowa sai wadanda aka tantance shi.

Za mu rika kawo rahoto kai-tsaye a kan yadda abubuwa su ke faruwa a kotun na Abuja.

Shugaban Bola Tinubu ya umarci bankin CBN da jami'an tsaro su kwato kudaden lamunin noma da 'yan Najeriya su ka handame....
05/09/2023

Shugaban Bola Tinubu ya umarci bankin CBN da jami'an tsaro su kwato kudaden lamunin noma da 'yan Najeriya su ka handame.

Wannan na zuwa ne bayan binciko biliyoyin Nairori da wadanda ke kiran kansu manoma su ka cinye.

Kungiyar Manoma a Najeriya (AFAN) ta ce tabbas samo kudaden zai yi wahala saboda mafi yawan wadanda su ka ci ba manoman gaskiya ba ne.

Najeriya na nazarin shiga ƙungiyar G-20Gwamnatin Najeriya ta ce tana nazarin aika buƙatarta ta shiga ƙungiyar ƙasashe 20...
03/09/2023

Najeriya na nazarin shiga ƙungiyar G-20

Gwamnatin Najeriya ta ce tana nazarin aika buƙatarta ta shiga ƙungiyar ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arzikin duniya, ake yi laƙabi da G-20.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale, ya ce gwamnati na auna alfanu ko kuma kasadar da ke tattare da zama mambar a ƙungiyar.

A ranar litinin ne shugaban ƙasar Bola Tinubu zai tafi birnin Delhi domin halartar taron ƙungiyar bisa gayyata ta musamman da firaministan Indiya Narendra Modi ya yi masa.

Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da matakai na farfado da tattalin arzikin ƙasar da ƙarfafa zuba jari amma kuma ƙasar na fama da hauhawar farashin kayayyaki da basuss**a da rashin ingancin kayayyakin more rayuwa.

A halin yanzu Afirka ta Kudu ce kaɗai daga Afirka ta samu zama mamba ƙungiyar ta G20.

Ecowas ta umarci dakarunta su ɗaura ɗamarar kai yaƙi NijarShugabannin ƙasashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ...
10/08/2023

Ecowas ta umarci dakarunta su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar

Shugabannin ƙasashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar, bayan juyin mulkin da sojoji s**a yi a ƙasar.

Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da s**a gudanar, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen a kan Nijar.

Sun cimma wannan matsaya ce yayin taron gaggawa da s**a gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Cikin sauƙi, ba za a iya fayyacewa ƙarara, a kan ko umarnin yana nufin dakarun sojin Ecowas za su auka wa Nijar da yaƙi, ko kuma za su ɗaura ɗamara su zauna cikin shirin yaƙi ba.

Tun da farko, Ecowas ta bai sojojin da s**a yi juyin mulki wa'adin kwana bakwai don su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da s**a hamɓarar daga mulki, ko su fuskanci matakin amfani da ƙarfin soji.

Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da s**a aika da kuma muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron Ecowas s**a bayar da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.

Sun kuma nanata Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.

Ƙungiyar ta ce za ta tabbatar da ganin ana aiki da duk ƙudurorinta kuma har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke. Shugabannin sun kuma ɗora wa jagororin Ecowas alhakin ci gaba da bibiyar takunkuman da aka ƙaƙaba wa shugabannin juyin mulki a Nijar

Haka zalika, sun gargaɗi waɗanda s**a ce suna kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Nijar su guji yin haka.

Hukumar Kula da Wasannin Match Official Limited (PGMOL) ta sake daukar Lee Mason aiki bayan an kore shi sak**akon babban...
10/08/2023

Hukumar Kula da Wasannin Match Official Limited (PGMOL) ta sake daukar Lee Mason aiki bayan an kore shi sak**akon babban kuskure a wasan Arsenal da ya gabata.

A cewar Daily Mail, hukumar alkalan wasa ta dauki Mason aiki domin ya taimaka wajen horar da sabbin jami’an Wasa.

Rahoton ya kara da cewa Lee Mason zai yi aiki tare da jami'ai a Premier League, EFL da Super League na mata, amma zai yi aiki ne musamman a gasa ta daya da ta biyu.

Lee Mason ya yi aiki a matsayin alkalin wasan Premier League tun daga 2007 zuwa 2022.

Asari Dokubo ya ce zai lallasa gwamnatin mulkin sojan Nijar idan aka ba shi dama.Tsohon shugaban kungiyar tsagerun Neja ...
10/08/2023

Asari Dokubo ya ce zai lallasa gwamnatin mulkin sojan Nijar idan aka ba shi dama.

Tsohon shugaban kungiyar tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, ya sha alwashin yin kasa-kasa da gwamnatin sojan Nijar.

Dokubo ya ce idan har gwamnatin tarayya da kungiyar ECOWAS s**a ba shi dama za su ga yadda zai yi da masu juyin mulki da dakarunsu a Nijar. A cewarsa yana da kaya da mutanen da ake bukata domin yin gaba da gaba da su.

Sai dai wasu na ganin duk soki-burutsu ne kawai domin a cewarsu fadan shara ba daya ne da na bakin ruwa ba.

MDD ta yi Allah-wadai da juyin mulki a NijarSakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres "ya yi kakkausar ...
27/07/2023

MDD ta yi Allah-wadai da juyin mulki a Nijar

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres "ya yi kakkausar s**a ga sauyin gwamnati da aka samu a Nijar ba bisa ka'ida ba," in ji kakakinsa a ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne bayan da sojojin Nijar din s**a sanar da juyin mulki a gidan talabijin na kasar, inda s**a ce sun jingine aiki da kundin tsarin mulkin kasar, tare da dakatar da dukkan hukumomi da kuma rufe iyakokin ƙasar.

Mista Guterres ya ce ya damu matuka da tsare Shugaba Mohamed Bazoum kuma ya damu da lafiyarsa, in ji kakakinsa Stephane Dujarric a cikin wata sanarwa.

Mista Dujarric ya ƙara da cewa "Sakatare-Janar ɗin ya yi kira da a gaggauta kawo karshen duk wasu ayyukan da ke kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya a Nijar."

DSS ta sake kwamushe Emefiele!Jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS sun sake cafke dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefie...
25/07/2023

DSS ta sake kwamushe Emefiele!

Jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS sun sake cafke dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele bayan karkare zaman Kotu.

Bayan arangama da jami'an hukumar gidan gyaran hali, DSS ta yi awon gaba da Mista Emefiele daga harabar Kotu.

Alkali ya bada belin Emefiele kan N20m da kuma wasu sharuɗɗa, ya umarci a tsare shi a gidan yari gabanin cika sharudda.

Sai dai duk da haka, DSS ta sake damƙe tsohon gwamnan babban bankin bayan gama zaman Kotu ranar Talata.

SUBHANALLAHI: Tsananin tsadar rayuwa tasa wani matashi a garin Ningi jihar Bauchi ya rat*aye kanshi. Sunan matashin Babb...
25/07/2023

SUBHANALLAHI: Tsananin tsadar rayuwa tasa wani matashi a garin Ningi jihar Bauchi ya rat*aye kanshi.

Sunan matashin Babba Mai Gyaran Sola, ya sanarwa da mutane cewa ya rataye kanshi ne saboda halin kunci na rayuwa da ya shiga ne sanadin yin hakan. Wasu mutane ne s**a je s**a taimaki matashin bayan ya rat*aye kanshi a daki, s**a kaishi asibiti har Allah yasa ya farfado.

Wallahi 'yan uwa mu cigaba da Addu'a, ana cikin halin matsin rayuwar da ya wuce duk yadda muke tunani, baka taba gane hakan sai kana fita wasu garuruwa da karkara, wallahi idan kaga halin da wasu suke ciki sai kayi kwalla saboda tausayi.

✍️ Comr Abba Sani Pantami

Abunda ke faruwa game da rabon mukammai a majalisar dokokin Najeriya.  Comrd Abba sani pantamiRikici na neman barkewa a ...
25/07/2023

Abunda ke faruwa game da rabon mukammai a majalisar dokokin Najeriya.

Comrd Abba sani pantami

Rikici na neman barkewa a majalisar dokokin Najeriya, bayan jihar Legas ta wawushe shugabancin manyan kwamitoci masu tsoka da ake ji da su a Majalisar.

Anki a bawa Betara mukamin da aka mishi Alkawari a lokacin da zai janye takararshi ta neman kakakin majalisa. Yanzu haka dan majalisar Ondo, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ake son ya jagoranci kwamitin ayyuka wanda aka yi wa Hon. Muktar Betara alkawari .

Muktar Betara ya nemi a dawo masa da kujerar shugaban kwamitin kasafin kudi, amma ana maganar Abubakar Kabir Bichi dake jihar Kano za'a bawa mukamin. Kusoshin a majalisa sun fusata, su na zargin an saba alkawarin da aka yi musu kafin su janye takararsu.

'Yan majalisar Tarayya na Arewa suna zargin masu rike da madafan iko a fadar shugaban kasa su na da hannu wajen yadda aka yi rabon kwamitocin majalisar kasar. Zuwa ranar Alhamis za'a kammala sanar da yadda aka yi rabon kwamitoci a majalisun wakilai da majalisar dattawa.

Rahoton da muka samu ya nuna mana cewa wani daga cikin ‘yan majalisar daga yankin Arewa ya ce an fifita ‘yan siyasan Legas da yaransu wajen raba muk**an, an ba su manyan kwamitocin da ake ji dasu.

Majiyar ta ce ‘yan majalisar Legas za su rike shugabancin kwamitocin tattalin arziki, tsaro, masana’antu da kwamitin ayyukan ‘yan majalisa da sauran wasu manyan kwamitocin.

Babajimi Benson mai wakiltar Ikorodu zai rike kwamitin tsaro, Tasir Wale Raji mai wakiltar Epe zai shugabanci kwamitin ayyukan majalisar kasar.

Sannan an warewa ‘dan majalisar Oyo, Akeem Adeyemi shugabancin kwamitin noma, hakan ya kara fusata ‘yan majalisar da s**a fito daga Arewa.

Kanwar Mujaheed Asari-Dokubo, Hon. Boma Goodhead za ta rike kwamitin harkokin Neja Delta.

Abunda ya k**ata Mutane su sani, irin wa 'yan nan mukamman kwamitocin a majalisa sune suke bawa dan majalisa dama sosai wurin taimakawa al-ummarshi idan yana da zuciyar hakan, duk yadda yake son taimakon mutanan shi matukar baida wani babban kwami

Yanzu haka DSS ta gurfanar da Emefiele, a gaban kotu da ke Legas. Emefiele ya iso kotun ana rike da hannunshi da sunan b...
25/07/2023

Yanzu haka DSS ta gurfanar da Emefiele, a gaban kotu da ke Legas. Emefiele ya iso kotun ana rike da hannunshi da sunan baida lafiya. Wane hukunci kuke ganin ya dace a yanke mishi?

PDP ta zargi APC da kokarin rufe bakin Atiku Sai dai kuma, PDP a wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin, 24 g...
25/07/2023

PDP ta zargi APC da kokarin rufe bakin Atiku Sai dai kuma, PDP a wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, ta yi zargin cewa, da ikirarin da wasu mahara s**a yi, an dauki nauyin harin ne don raba Atiku da rayuwarsa kan dage da ya yi na kwato zabensa a kotun zaben shugaban kasa.

Kungiyar kare hakkin Musulunci ta MURIC ta bukaci hukumar DSS da ta gayyaci shahararren mawakin kudu Davido a kan bidiyo...
25/07/2023

Kungiyar kare hakkin Musulunci ta MURIC ta bukaci hukumar DSS da ta gayyaci shahararren mawakin kudu Davido a kan bidiyon wakar da ya wallafa a shafinsa wanda daga bisani bayan yaga musulman kasar sun fusata ya goge wakar.

Kungiyar MURIC ta ce akwai bukatar mawakin ya zo ya yi bayanin dalilinsa na sakin irin wannan bidiyo da ka iya tayar da zaune tsaye a kasar.

An dai gano Olori a cikin wakar tasa mai suna “Jaye Lo” wacce Davido ya wallafa, ya zauna a saman wani masallaci yana raye-raye.

Tinubu zai sanar da ministocinsa a ranar Talata, inji Bashir Ahmad.Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir...
25/07/2023

Tinubu zai sanar da ministocinsa a ranar Talata, inji Bashir Ahmad.

Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya tabbatar da cewar Shugaban kasa Bola Tinubu zai sanar da ministocinsa a ranar Talata.

Bashir ya ce za a sanar da jerin ministocin ne a zaman da majalisar dattawa za ta yi a yau, 25 ga watan Yuli.

Yan Najeriya na ta zuba idon ganin da wa da wa shugaban Tinubu zai zaba domin su zama abokan tafiyarsa a gwamnati.

Bayan Kai Masa Harin Bam A Gidansa Atiku Ya Magantu "An tura mutane hudu da ake zargin Boko Harám ne su kai mini hari, a...
24/07/2023

Bayan Kai Masa Harin Bam A Gidansa Atiku Ya Magantu

"An tura mutane hudu da ake zargin Boko Harám ne su kai mini hari, a wasu wurare a Yola, yanzu haka suna hannun sojoji, Inj Atiku Abubakar

Kylian Mbappe na shirin bin Cristiano kasar Saudiyya don ci gaba da buga tambola amma a kungiyar Al-Hilal.Kungiyar ta mi...
24/07/2023

Kylian Mbappe na shirin bin Cristiano kasar Saudiyya don ci gaba da buga tambola amma a kungiyar Al-Hilal.

Kungiyar ta mika tayin fiye da Yuro miliyan 300 don dauke Mbappe daga PSG, rahotanni sun ce kungiyar ta amince da tayin.

Mbappe ya samu matsala ne da kungiyar kan kin kara kwantiragi inda s**a cire sunansa a cikin 'yan wasansu.

Jami'an 'yan sanda sun cafke wasu da ake zargin sun shirya kai hari gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubaka...
24/07/2023

Jami'an 'yan sanda sun cafke wasu da ake zargin sun shirya kai hari gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne su hudu sun bayyana wurare na musamman da s**a shirya kai harin.

Daya daga cikinsu ya bayyana cewa shi dan Boko Haram ne daga karamar hukumar Damboa a jihar Borno.

Najeriya ta ba wa duniya kunya kan rashin dai-daita lamura- Olusegun Obasanjo tsohon shugaban Najeriya
24/07/2023

Najeriya ta ba wa duniya kunya kan rashin dai-daita lamura- Olusegun Obasanjo tsohon shugaban Najeriya

Abba ya naɗa Shehin Malami da ƙarin mace a matsayin kwamishinoni a Kano.Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙarin kwamis...
24/07/2023

Abba ya naɗa Shehin Malami da ƙarin mace a matsayin kwamishinoni a Kano.

Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙarin kwamishinoni biyu da Abba Gida Gida ya aike mata.

A zaman yau Litinin karkashin shugaban majalisa, Isma'il Falgore, majalisar Kano ta tantance mutanen biyu kuma ta amince da naɗinsu.

Kawo yanzu, majalisar Kano ta amince da naɗin kwamishinoni 22 a gwamnatin Abba Gida-Gida.

Waɗanda gwamnan ya naɗa su ne, Sheikh Tijani Auwal da kuma Hajiya Aisha Lawal-Saji.

Wane fata kuke musu

📷: Abba Kabir Yusuf (Facebook)

Dan wasan kwallon Najeriya Ahmad Musa ya karya farashin man fetur a Kano.Ya rage Naira 40 daga farashin da ake sayerwa a...
24/07/2023

Dan wasan kwallon Najeriya Ahmad Musa ya karya farashin man fetur a Kano.
Ya rage Naira 40 daga farashin da ake sayerwa a kasuwa.

Me za ku ce

Ko wa Allah ya bai wa mulkin Kano za mu bi shi - GawunaMataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙ...
15/01/2023

Ko wa Allah ya bai wa mulkin Kano za mu bi shi - Gawuna

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ko wa Allah ya bai wa mulkin jihar za su bi shi su kuma ba shi shawara, domin ciyar da jihar gaba.

Ɗan takarar ya yi wannan maganar ne a lokacin wata muhawara tsakanin 'yan takarar gwaman jihar Kano da BBC Hausa ta gabatar ranar Asabar.

Gawuna ya ce ''idan Allah ya so ya ba mu muna addu'ar ya yi riƙo da hannunmu za mu hidimta wa al'umma; idan kuma Allah bai ba mu ba, ko wa Allah ya bai wa za mu bi shi, kuma za mu ba shi shawara ta gaske, domin a samu ci gaban al'ummar jihar Kano''.

Ɗan takarar ya kuma sake nanata kiran al'ummar jihar da cewa a zaɓi cancanta a lokacin zaɓen gwamnan da ke tafe ''a duba mutumin da ya cancanta a zaɓa''.

Ya kuma ce a yi siyasa cikin lumana, domin kuwa ''Mu 'yan takarar duka da muka zo nan BBC Hausa ta sauke mu a ɗaki ɗaya kuma duka muka gaisa tare da mutunta junanmu'',.

''Dan haka ina kira ga magoya bayanmu da su zauna lafiya'' in ji Gawuna.

Ango Ya Rasu Ana Gab Da Ɗaurin Aurensa A Katsina.Daga Hizbullahi Bello boyiWani matashin Ango ya rasu ana gab da ɗaura m...
09/01/2023

Ango Ya Rasu Ana Gab Da Ɗaurin Aurensa A Katsina.

Daga Hizbullahi Bello boyi

Wani matashin Ango ya rasu ana gab da ɗaura masa Aure da Amaryarsa a jihar Katsina.

Abokin karatunsa Kamilu Abubakar shi ne ya bayyana mana haka a wayar salula, inda ya bayyana cewa, motar su angon ta taso daga jihar Nasarawa zuwa jihar Katsina a lokacin ne haɗarin mota ya rutsa da su a daide marabar ƙaramar hukumar Ɗanja dake jihar Katsin, k**ar yadda wakilin Katsina Post ya rawaito.

Lamarin ya faru ne saura kwana 6 a ɗaura Aurensa da Amaryarsa.

Wata majiya mai tushe daga Abokan karatunsa, Comrade Umar Musa Yar'addu'a da Mujahid Rabi'u sun bayyana cewa, sun yi waya da shi a ranar kuma sunyi chat da shi a kafar sadarwa ta Facebook, sun ce a lokacin da ya taho yayi rubutun addu'a a kafar Facebook kafin ya baro jihar Nasarawa inda yake cewa yana a hanya Allah ya kawo su gida lafiya.

Kafin rasuwar matashin, ya kammala karatunsa a Kwalejin Ilimi Ta Tarayya dake Katsina (FCE Katsina) a sashen HAUSA/ISLAMIC a 40SERIES.

Angon ɗan asalin garin Kuka-sheƙa ne dake yankin ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, ya rasu yana da shekaru 24 a duniya.

Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP reshen KanoDaga:- Najiyullahi Usman AltineWutar rikici ta ƙara ruruwa a PDPn j...
09/01/2023

Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP reshen Kano

Daga:- Najiyullahi Usman Altine

Wutar rikici ta ƙara ruruwa a PDPn jihar Kano duk da hukuncin kotu na baya-bayan nan da kuma matakin ɗaukaka ƙara daga ɗaya banagaren.

Lamarin ya faru ne bayan ɓangen Sadiq Wali wanda wata kotun tarayya ta ce ba shi ne ɗan takarar gwamnan ba, kuma ya ɗaukaka ƙara, daga baya ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa a jihar.

Sai dai ɓangaren da kotu ta ce shi halastacce na Muhammad Abacha ya fito ya yi Alla-wadai da wannan mataki yana cewa nuna raini ne ga kotu.

Bayanan da BBC ta samu na cewa a wannan Litinin ɗin ne ake sa ran kwamitin yaƙin neman zaben da ɓangaren Sadiq Wali s**a ƙaddamar zai fara zama domin tattauna yadda zai gudanar da aikinsa.

A makon jiya ne aka kafa kwamitin, al’amarin da ya ƙara tayar da kura.

Ɓangaren Muhammad Abacha sun ce ba su tare da wannan matakin k**ar, yadda Barrister Ibrahim Isa Wangida, lauyan jam’iyyar PDP a Kano ya shaida wa BBC.

To sai dai bangaren Sadiq Wali wanda ya ƙaddamar da kwamtin ya ce, waɗanda suke s**ar wannan matakin ba su fahimci yadda tsarin yake ba, a ta-bakin kakinsu Dakta Yusuf Bello Danbatta.

Masharhanta dai na ganin duk wannan rikici da taƙaddama, jam’iyyar ce ke yi wa kanta sakiyar da babu ruwa, dai-dai lokacin da hankulan sauran jam'iyyu s**a karkata ga yaƙin neman zaɓe.

Jam'iyyar ta PDP da ke sahun manyan masu hamayya a Kano har yanzu kanta a rarrabe yake lamarin da ake ganin hakan ba zai yi mata kyau, kasa da wata biyu a gudanar da zabe.

Muna buƙatar Buhari ya sa baki kan ƙarin kuɗin makaranta - Kungiyar DalibaiƘungiyar Ɗalibai ta Najeriya NANS ta buƙaci s...
07/01/2023

Muna buƙatar Buhari ya sa baki kan ƙarin kuɗin makaranta - Kungiyar Dalibai

Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya NANS ta buƙaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi ''gaggawar sa baki'' game da ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'in ƙasar ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin ƙasar''.

Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa ''duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari'',

A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu daga cikin jami'o'in ƙasar s**a bayyana ƙarin kuɗin makaranta.

To sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.

Dalilin ya da sa kenan s**a rubuta wasika ga shugaba ƙasa, inda s**a buƙace shi a matsayinsa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya.

Wasu jami'o'in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun nasu.

To sai dai ƙungiyar ta ce kundin tarin mulki ya wajabta wa gwamnati samar da ingantaccen ilimi ga 'yan ƙasa, don haka dole ta samar da kuɗin gudanar da ɓangaren ilimi.

Haka kuma Sakataren na NANS ya ce ''matuƙar ba a soke ƙarin kuɗin makarantar da aka yi ba, to kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na ɗaliban ƙasar ba za su koma makaranta ba, saboda ba za su iya biyan wannan kuɗi ba''.

Abin da kuma a cewarsa zai ƙara yawaitar masu aikata miyagun laifuka a fadin ƙasar saboda rashin makoma da ɗaliban ke da shi.

Mista Kankia ya kuma yi gargaɗin cewar ''matukar buƙatarmu ba ta biya ba, to za mu gudanar da gagarumar zanga-zangar da za ta shafi abubuwa da dama a faɗin kasar nan''.

Ƴan Sandan Nijeriya Sun Cika Hannu Da Yaron Da Yayi Garkuwa Da Mahaifinsa.Daga:- Najiyullahi Usman Altine‘Yan sanda a ji...
07/01/2023

Ƴan Sandan Nijeriya Sun Cika Hannu Da Yaron Da Yayi Garkuwa Da Mahaifinsa.

Daga:- Najiyullahi Usman Altine

‘Yan sanda a jihar Kwara sun k**a wani yaro Mai suna Issa Naigheti, wanda ake zargi da hada baki da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da mahaifinsa.

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar na yaki da masu garkuwa da mutane sun k**a Naigheti ne a ranar 4 ga watan Janairu, 2023 a Kambi kan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi ya amsa laifin hada baki da wasu mutane biyu wajen sace mahaifinsa.

“Mambobin rundunar ‘yan sanda da ke yaki da masu garkuwa da mutane sun k**a wani Issa Naigheti “m” a ranar 4/1/2023 a kusa da unguwar Kambi da ke Ilorin yayin da ake bin sahun masu garkuwa da mutane; A yayin da ake tattaunawa da shi ya bayyana cewa ya hada baki da wasu mutane biyu wajen sace mahaifinsa, daya Bature Naigboho “m,” a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo, kuma an karbo kudi #2.5 miliyan a matsayin kudin fansa.

Ana ci gaba da kokarin damke sauran wadanda ke da hannu a lamarin, kuma za a mika karar zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin.

“Kwamishanan ‘yan sandan ya nanata kudurin sa na samar da ingantaccen yanayi domin gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali,” in ji PPRO.

Shugaba Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2023Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ...
03/01/2023

Shugaba Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2023

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar wanda ya kai jimillar naira tiriliyan 21.83.

Shugaban ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan buki da aka yi a yau Talata a fadarsa da ke Abuja.

Hakan na zuwa ne kwana shida bayan majalisar dokokin ƙasar ta amince da kasafin.

Kasafin ya ƙunshi naira tiriliyan 6.6 na biyan bashin da ake bin ƙasar, da naira tiriliyan 8.3 na ayyukan yau da kullum, sai kuma naira tirilayn 5.9 na manyan ayyuka.

Wasu ɓangarorin da s**a samu kaso mafi tsoka su ne ma’aikatar tsaro wadda aka ware wa naira biliyan 285, da ma’aikatar lafiya mai naira biliyan 134.9, da ma’aikatar mak**ashi mai naira biliyan 195.5, sai ma’aikatar ilimi wadda ke da naira biliyan 153.7.

Na yi wa 'yan Najeriya duk abin da zan iya - Shugaba BuhariShugaban Najeriya Muhammadu ya shawarci 'yan kasar da su shig...
01/01/2023

Na yi wa 'yan Najeriya duk abin da zan iya - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu ya shawarci 'yan kasar da su shiga sabuwar shekarar 2023 da fatan ganin kasar ta ci gaba da fuskar hadin kai da fatan ci gaba.

Cikin sakonsa na sabuwar shekara da ya aika a jiya, Shugaba Buhari ya ce 2023 shekara ce da za a kara mayar da hankali kan harkokin tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yakin da cin hanci.

Buhari wanda ya yi maraba da s**a da yabon da 'yan Najeriya ke yi masa, ya ce ya yi iya abin da zai iya ga mutanen kasar, yayin da yake fatan duk shugaban da zai zo ya dora daga inda ya tsaya, domin ciyar da Najeriya caga.

Ya ce dole yan Najeriya su dauki ragamar tabbatar da zabukan da za a yi a 2023 an yi su babu cuta babu cutarwa.

Ya kuma shawarci 'yan kasar da su kiyaye da tayar da hankali a lokutan zabe, su kuma kiyaye daga duk wani dan siyasa da zai nemi su yi hakan.

’Yan Sanda Sun K**a Maharan Da S**a Addabi Abuja Da NasarawaDaga Najiyullahi Usman AltineRundunar ’Yan Sandan babban bir...
30/12/2022

’Yan Sanda Sun K**a Maharan Da S**a Addabi Abuja Da Nasarawa

Daga Najiyullahi Usman Altine

Rundunar ’Yan Sandan babban birnin tarayya, ta cafke gungun wasu mutum 10 da ake zargin su da kai hare-hare a Abuja da Jihar Nasarawa.

Da yake gabatar da su a gaban manema labarai, Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Sadiq Abubakar, ya ce an k**a wadanda ake zargin a wani otel da ke yankin Masaka, kilomita kadan zuwa Abuja.

An samu bindiga kirar AK-47 guda biyar, sai kwanson harsashi 22 da kuma kananan bindigogi guda uku.

Ragowar abubuwan da aka samu a wajensu sun hada mota kirar Toyota Camry 2000, katin aikin wani dan sanda da kuma janareto guda biyu.

Kazalika, rundunar ta cafke wasu bata-gari hudu da ake zargi da aikata fashi da makami a unguwar Maitama da ke Abuja.

Har wa yau, wadanda ake zargin sun yi wa wani mai sana’ar POS fashin kudi.

An samu karamar bindiga guda uku da harsashi 14, talabijin guda biyu, wayoyin hannu da kuma kayan yari da ake zargin fashin su s**a yi.

Rundunar ta kuma gano maboyar wasu masu kai wa ’yan bindiga mak**ai ne.

A yayin bincike mutanen biyun da s**a shiga hannun, sun bayar da ce ’yan fashi da ’yan bindiga suke yi wa safarar mak**ai.

An samu harsashi guda 900 da sauran muggan mak**ai a hannunsu wanda ake kyautata zaton na ’yan bindiga ne.

Masu garkuwa sun kashe wasu 'yan gida ɗaya bayan sun karɓi fansar naira miliyan 60Masu garkuwa da mutane sun kashe wasu ...
26/12/2022

Masu garkuwa sun kashe wasu 'yan gida ɗaya bayan sun karɓi fansar naira miliyan 60

Masu garkuwa da mutane sun kashe wasu 'yan uwan juna su uku tare da wani mai babur bayan da s**a karɓi fansar naira miliyan 60 daga mahaifin yaran a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Jaridar daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da dajin Garin Dogo a yankin ƙaramar hukumar Lau ranar Lahadi.

Rahotonni sun ruwaito cewa masu garkuwar sun k**a mutanen uku - waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya - inda kuma s**a buƙaci naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.

Mahaifin yaran uku wanda mai sana'ar safarar shanu ne ya daidaita da masu garkuwar - waɗanda s**a amince zai biya su naira miliyan 60 domin sakin 'ya'yan nasa uku.

Sai kuma ya ɗauki ɗan achaba tare da bashi kuɗin domin kai wa masu garkuwar a cikin dajin da ke kusa da ƙauyen nasu, dan sakin 'ya'yan nasa.

To sai dai bayan kai kuɗin fansar da mai babur ɗin ya yi sai s**a kashe shi tare da sauran yaran uku, bayan sun karɓi kudin fansar.

Address

Ahmad Rufa'i Road
Sokoto

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiya online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Media/News Companies in Sokoto

Show All