GNN Hausa

GNN Hausa Zamu Dinga Kawo Muku Labarai Akan Kari

Hajjin bana: An shawarci alhazai da su hakura da sallar Juma'a a Harami saboda tsananin zafiHukumar Kula da Yanayi ta Ka...
06/07/2023

Hajjin bana: An shawarci alhazai da su hakura da sallar Juma'a a Harami saboda tsananin zafi

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasar Saudiyya ta sanar da cewa yanayin zafi a gobe Jumma’a, 8/7/2023 zai kai daraja 50° na tsananin Zafi.

Saboda wannan zafin yanayin, Gwamnatin Saudiyya na bada shawarar cewa Alhazai da suyi Sallar Jumma’ah a Masallatan da s**a fi kusa da gidajensu, ba sai sun je Harami ba, don kaucewa shiga tsananin rana.

Don haka Ma’aikatar Aikin Hajji ta Kasar Najeriya ta yi kira ga alhazan ƙasar da su yi amfani da wannan shawara ta yin Salla a Masallatai Mafi kusa da Masaukan su.

Kamar yadda sanarwa daga Dr. Ibråhìm Muhammad Sodangi, Babban Jami’in Hukumar Alhazai ta Kasa a Birnin Makkah ta bayyana a yau Alhamis.

Wani Mutum Yayi Nasarar Lashe Gasar Gudu Da Wuta Na Ci A Jikinsa.Daga Zuhair Ali Ali Ibrahim (Z.A.I)“Wani ma’aikacin kas...
06/07/2023

Wani Mutum Yayi Nasarar Lashe Gasar Gudu Da Wuta Na Ci A Jikinsa.

Daga Zuhair Ali Ali Ibrahim (Z.A.I)

“Wani ma’aikacin kashe gobara dan kasar Faransa Jonathan Vero mai shekaru 39 ya kafa tarihi a duniya bayan ya yi gudu mai mafi tsayi ba tare da rigar kariya ba a jiki ko iskar oxygen.

“A cewar Guinness World Records a ranar Alhamis, Vero ya yi gudun mita 272.25 (893 ft) yayin da jikin sa ke ci da wuta ba tare da rigar kariya ba Vero ya kafa tarihin duniya na mita 204.23 (670 ft) wanda Antony Britton na Burtaniya ya kafa.

“Haka kuma Jonathan ya kafa tarihin tsere na duniya mai mita 100 cikin sauri ba tare da iskar oxygen ba, ya doke Britton da dakika 17, Britton shine wanda ya kafa tarihin da babu wanda ya doke sa sai a wannan lokacin 7.58.

Da Dumi-Dumi Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci Ganduje kan bidiyon DalaHukumar karbar korafe-korafe da ya...
06/07/2023

Da Dumi-Dumi
Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci Ganduje kan bidiyon Dala

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje bisa bidiyon Dala.

A shekarar 2017 dai ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu hotunan bidiyo, inda ake zargin tsohon Da karbar wani abu mai k**a da cin hanci daga hannun 'yan kwangila.

Sai dai tsohon Gwamnan ya musanta wannan zargi, inda yace bidiyon ba ya da sahihanci.

Barr Muhyi Magaji Rimin-Gado shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar a ranar Laraba ya ce binciken kwakwaf ya tabbatar da sahihancin bidiyon. Kazalika, da safiyar Alhamis, Barr Rimin-Gado ya ce hukumar ta gayyaci Ganduje domin ya amsa tambayoyi.

Daga DCL

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN Wata matar Aure ta chakawa mijinta wuka a kirgi ya mutu har lahira a jihar Bauchi. ...
06/07/2023

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN

Wata matar Aure ta chakawa mijinta wuka a kirgi ya mutu har lahira a jihar Bauchi. Gidan rediyon Albarka dake jihar Bauchi ne s**a kawo rahoton yanzu haka. Allah ya kyauta.

Koyi ta bada belin DCP Abba Kyari.Karin Bayani Yana Nan Tafe
06/07/2023

Koyi ta bada belin DCP Abba Kyari.

Karin Bayani Yana Nan Tafe

Address

Sokoto
840101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GNN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Media/News Companies in Sokoto

Show All

You may also like