25/08/2023
Neman ilmin abunda ya ke wajibi akan mu acikin Addini ko rayuwa,to Neman sanin sa dole ne gare mu,to amma sanin kowane ilmi bai zamo tilas akan mu ba.
Wanda ya sanar da kai Allah da maaiki a aikace,to yafi Wanda ya karantar da kai littafi dubu da ka kasa gane Allah da maaiki ta hanyar su.
idan Allah ya hada mu da masana Allah a aikace da karance, sai nesa tazo kusa ita kuma matuka ta samu.
idan mu ka rasa masana Allah a aikace, sai mu rayu cikin rikici ta hanyar takardun littafai.
idan muka rasa masana littafai sai mu rayu babu Qaida.
idan Allah ya hada mu da Wanda s**a hada abu biyu,sai mu tsira daga fitinar duniya da lahira.