Malumfashi Social Media Association - MASMA

Malumfashi Social Media Association - MASMA Manufar mu shine Malumfashi ta ci gaba ta kowane bangare.

10/11/2023

The sincere hearts and the pious supplications are soldiers which can never be defeated. - ibn Taymiyyah (may Allah have mercy on him)

10/11/2023

Ina matasa masu bukatar aikin Kamfani ?

( Chivita Nigeria Limited )
Suna massive recruitment. Aduba comments sections👇

10/11/2023

Happy follow-versary to my awesome followers. Thanks for all of your support! Yahaya Isah Dodi

10/11/2023

Muna Ya ba ma Gwamnatin Jihar KATSINA. A bisa kokarin da take wajan kawo karshen ta'addanci a fadin Jihar.

Allah ya karfafi guiwa yashige gaba.

10/11/2023

YADDA ALMAJIRI A KAN T**I ZAI KOYA MA KA HANYOYIN INGANTA SANA'AR KA!

Da ace almajiranci sana'a ce halastacciya kuma me kyau, da an yi mashahuran almajirai. Duk da ba sana'a ba ce, akwai wasu ɗabi'u masu kyau na kasuwanci da duk me sana'a zai koya daga wurin almajirai. Ga wasu daga cikinsu;

1. Kwarin gwiwa. Almajirai akan t**i su na da kwarin gwiwar neman taimako a wurin mutanen da ba su san su ba. Ba tare da jin kunya ba, almajiri, zai nemi taimakon ka ko kai waye. A matsayin ka na me sana'a, kar ka ji kunyar neman taimako, neman mentorship ko partnerships. Sanyin gwiwa ba na ka bane.

2. Samun gurin da ya dace. Almajirai sun laƙanci iya zaɓar location da mutane masu yawa ko masu ba da sadaka ke bi su zauna don yin bararsu. Kai da ka ke sana'a, ka koyi iya zaɓawa kasuwancin ka wurin da ya dace don cigaban harkokin ka. Wannan skill ɗin nau'i ne da ake kira positioning a business.

3. Haƙuri da juriya. Almajirai na fuskantar ƙalubale a kullum wajen ganin sun samu abinda za su yi hidimar rayuwa. Haka ba ya sawa su karaya ko su sare su daina bara. Su na da juriya sosai. Me sana'a kullum cikin fuskantar ƙalubale ya ke. In ya warware wannan, wancan ya ɓullo. Kar ka karaya domin nasara ba ta samuwa sai an sha wahala.

4. Sanin halin ɗan Adam da iya mu'amala da shi. Almajirai sun naƙalci halin mutane da ɗabi'unsu wanda hakan ya sa cikin fara'a da tausasa murya su ke neman taimako a wurin mutane. Me sana'a na buƙatar ya fahimci halayyar mutane, abinda da ke faranta mu su da wanda ba sa so don ya ciyar da kasuwancin da gaba.

5. Yawan godiya. Almajirai na yawan nuna godiya ga mutane a duk lokacin da aka basu sadaka. Mafi yawancin su na bin wanda ya ba su sadaka da addu'a. Wannan na nuna sun ji daɗin alkhairin da aka yi mu su komai ƙanƙantar sa. Me sana'a ya na da kyau ya zamanto me godiya ga Allah, me nuna godiya da jin daɗi ga kwastomominsa, ne godiya ga ma su taya shi aiki.

Allah ya ba da sa'a, ya ƙarawa nema albarka!

29/10/2023

Ina masu bukatar aikin NGOs ?

Ga babbar tsaraba an samo muku. Kar ayi wasa da wadannan portals din👇

27/10/2023

Alhamdullillah
1 dollar 11:0011:0011:00

27/10/2023

Mawakin Buhari yace Buhari ne ya kashe kasa yace kowa kunya yake ji ya fada😀. Allah ya sa mu dace 🤲🏿🤔🤔

27/10/2023

Ina masu bukatar Scholarships opportunity ?

( King Fahad University )
SaudiArabia, sun bude portal👇

26/10/2023

Ina masu bukatar aikin NGOs ?

( Action Against Hunger ) suna recruitment. A duba comments sections👇

26/10/2023

Ina masu bukatar opportunities daga NGOs ?

( International Alert ) wani babban NGO ne dake nan Najeriya. Sun fitar da wani opportunity👇

26/10/2023

Muna kewar Bello Mandiya Tsohon Sanata a Shiyyar FUNTUA.

FUNTUA ZONE INA MAFITA???Sulaiman AbdullahiZamu iya cewa a duk fadin Nigeria babu wani zone din da s**a samu Senator wan...
22/10/2023

FUNTUA ZONE INA MAFITA???

Sulaiman Abdullahi

Zamu iya cewa a duk fadin Nigeria babu wani zone din da s**a samu Senator wanda ba aikin cigaban al'umma da talakawa bane a gabanshi ba irin Funtua zone...

Sabida dalilai kamar haka:-

Dalili na farko shine, a cikin mawuyacin halin da muka shiga, babu wani Senator din da be taimaka ma yan makaranta na zone dinshi da tallafin kudin karatu ba sai namu na Funtua zone.

Dalili na biyu shine, a duk jihohin dake fama da rashin tsaro babu senator din da be tashi a majalisa ya gabatar da koke akan rashin tsaron dake damun al'ummar yankinshi ba sai na Funtua zone. Sabida shi be damu da halin da al'ummar yankin suke ciki ba!

Dalili na ukku shine, duk kokarin da me girma gwamnanmu Dr. dikkoh Umar Radda PhD. yayi akan tsaro tun daga fara daukar matasa da akaba horo har zuwa yayesu babu abinda senator dinmu yafito yayi akai, babu jinjinawa, babu yabawa koda a Media ya nuna murnarshi akan abun beyiba bare kuma ace yaje ya taimaka ma matasan da dan wani abu dazasu rike a hannunsu.

Hatta gwamnoni da sauran manyan mutane daga ko ina a fadin arewa sunzo wajen taron yaye wannan hazikan matasan amma nidai ko awajen taron yaye wannan matasan banga senator dinmu na Funtua zone ba.

Dalili na hudu shine, an kashe, an sace, an raunata, an sace dukiyoyin al'ummah amma banga yazo mana jaje ba koda sau daya ne.

Dalili na biyar shine, a cikin lokacin da s**ayi a senate akwai recruitments dinda akayi da yawa, kamar irinsu:-

-Nigerian Customs Service (NCS)
-National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA)
-Federal Road Safety Corps (FRSC)
-Nigerian Immigration Service (NIS) da sauransu.

Amma zamu iya cewa a gaba daya Funtua zone babu mutun goma da zaka iya nunawa daya samar ma aiki a cikin dukkan wannan bangarorin.

Amma saboda rashin sanin ciwon kai wai a haka wasu wanda basu kishin yankinsu da mutanen yankinsu suke cewa wai Funtua zone munsami wakili nagari.

Shin mutanen Karaduwa zone a haka zamu zuba ido muna gani a rinka yi mana irin wannan mulkin rashin adal

Malumfashi City.Wanne fata kuke ma wannan gari nan da shekaru 8 masu masu zuwa !
22/10/2023

Malumfashi City.

Wanne fata kuke ma wannan gari nan da shekaru 8 masu masu zuwa !

21/10/2023

Wadanda ke cikin tsananin kuncin ko damuwa YaaAllahu ka yaye musu.

YaaAllah ka kiyaye mu daga dukkan musibun duniya

17/10/2023

Muna yi ma al'ummar Malumfashi da jihar Katsina Baki Daya ta'aziyya bisa rasuwar Dr. Shamsu Abubakar. Allah ya kyautata makwanci.

17/10/2023

Sanarwa !

Janazar Malam Shamsu (Allah Yayi Masa rasuwa ) A kofar gidansu da ke Layin Tabarka (Layin Yan bori/Yar Matsiga) Kusa da gidan Kasimu mai Kasa, Makobta Da Gidan Marigayi Isan Nazoza, Da An yi Sallar Magriba In Sha Allah

08/06/2023
Sarki DikkoDaga Muktar Mudi SipikinAn ce wata rana Sarki Dikko ( Allah ya kyautata makwaci) yana zaune ana ta fadanci, k...
07/06/2023

Sarki Dikko

Daga Muktar Mudi Sipikin

An ce wata rana Sarki Dikko ( Allah ya kyautata makwaci) yana zaune ana ta fadanci, kawai sai aka ji Sarki ya ce " Mu mu ne, ba wanda yafi mu!"

Nan fa fada ta yi tsit, kowa ya yi shiru, sai Limamin Gari, ya nisa ya ce "mu mune ɗin dai" Sarki yana jin sa, amma sai yayi bakan kamar bai ji shi ba, haka aka gama fadanci aka aka tashi.

Can dare sai Liman ya ji ana ƙwanƙwasa mai ƙofa, ko da fitowar sa, sai ya ga sarki Dikko shi kaɗai, nan fa Liman ya zube ya kwashi gaisuwa. Sarki ya dubi Liman ya ce " ɗazu na ce mu mune mun fi kowa, amma sai na ga kamar kana inkarin maganar mu, don haka mu je kanuna mun wanda ya fi mu"

Nan liman ya koma cikin gida ya shirya, ya fito su ka nausa cikin gari. Liman na gaba Sarki na biye, har su ka zo ƙofar wani gida. Liman ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan "aka ce waye?" Liman ya maida batu da cewar shi ne da sarki ke sallama. Ai dandanan mai gidan ya buɗe ƙofa a guje, ya durƙasa ya gaida sarki. Bayan sun ɗan gaisa, mutumin nan ya koma cikin gida.

Liman ya kalli sarki ya ce, ran ka "ya daɗe ga wanda kuka fi nan" Sannan ya wuce gaba sarki na biye, a haka har su ka ƙara zuwa ƙofar wani gida, liman ya ƙwanƙwasa ƙofa "aka ce waye" Nan ma liman ya ce shi ne da sarki ke tafe, kawai sai su ka ji an ce "ina wani aiki ne, ina zuwa"

Bayan can an jima sai mai gidan ya fito, ya miƙawa sarki hannu a tsaye babu ko risinawa, ya ce " Ranka ya daɗe ya mulki?" Sarki ya amsa, shi ma ya tambayi wannan malamin ya karatu da almajirai, ya ce komai lafiya, ya shiga gida.

Liman ya kalli sarki ya ce "ranka shi daɗe wannan dai-dai ya ke da ku" wato dai tsaransa ne.
Nan dai s**a ƙara gaba har zuwa wani ƙofar gida, liman ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan, aka ce waye, nan ma liman ya ce, shi ke tafe da Sarki, sai mutumin ciki ya ce " ina zuwa, ku ɗan jira"

Su ka ɗan jima amma shiru. Liman ya ƙara ƙwanƙwasa ƙofa, aka ƙara cewa " na ce ku jira ina zuwa, ko?" haka dai su kai ta jira, can liman da Sarki su ka ƙosa, dan sun jima su na jira, s**a ƙara buga ƙofar, sai su ka ji an ce "abubuwa sun yi mun yawa, ka cewa Sarkin ya dawo gobe da safe"
Liman ya kalli sarki ya ce "ranka ya daɗe ga wanda su ka fiku nan"

Kashe gari, Sarki ya bada umarnin a je a zo da Malamin nan. Fadawa su ka je su ka riske shi ya na bawa almajirai karatu, su ka ce "sarki ya ce akai ka" Shi ko malamin nan ya cewa almajiransa " ku yi alola, za mu je yi wa sarki sallah"

Ai kuwa tun da malamin nan ya doshi hanyar gidan sarki, aka ce sarki ya fara jin ba daɗi a jikinsa, ai kuwa nan da nan aka je aka kirawo yayan wannan malamin aka faɗa masa yadda ake ciki. Ya je ya tare shi, ya hau shi da faɗa, sa'annan ya juya ya koma.

Bayan kwana biyu, sarki ya kalli liman yace "mun yarda an fi mu, daga yau ba a ƙara fin mu"
An ce daga ranar ba a ƙara ganin Sarki Dikko ya rintsa da daddare ba, ibada kawai yake!
Allah ya kyautata makwanci.

Ga mai tambaya akan wannan labarin a gaske ne ko kuwa, toh ni dai wani ɗan cikin gidan ne ya taɓa ba ni shi, ba karantawa na yi ba.
Yo! yawan tambaye-tambaye fa matsala ne dan su s**a sa "Amadu Kuren Daga" Sarkin Damagaram ya sa aka kashe Cazemajou (wani baturen Hwaranshi). Ko da shi ke, kashe shi (Cazemajou) gaba takaimu mu Kanawa, Dan Amadu ya isa jarimi, ban ƙara tabbatarwa ba sai da na hau dutsen Tirmini.

Mani Kasumawa Kalgeri ka taɓa hawa wannan dutsen kuwa? Ina tuni!😄

Shugaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan harkokin sufurin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya ce kaddamar da kamfanin...
06/06/2023

Shugaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan harkokin sufurin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya ce kaddamar da kamfanin Najeriya Air da aka yi yaudara ce.

Karin bayani - https://bbc.in/42qelc7

06/06/2023

Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un

Allah yayi ma Alhaji Ibrahim Dan ilu Safana rasuwa Magaji guzurawa

Ya rasu bisa gajeruwar rashin lafiya, za'ayi jana'izar shi a gobe da safiyar laraba a kofar gidan shi dake kamar Hukumar Safana

Allah ya jikan shi da Rahama yasa ya huta.

Daga Abbas Nasir

Kotu ta ce masu ƙalubalantar nasarar Tinubu su biya miliyan goma-gomaKarin bayani -
06/06/2023

Kotu ta ce masu ƙalubalantar nasarar Tinubu su biya miliyan goma-goma

Karin bayani -

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Good things take time and patience.
03/05/2023

Good things take time and patience.

02/05/2023

A yayin da ake cigaba da jiran sunayen mutanen da za su riƙe muƙamai na farko farko a gwamnatin tarayyar Najeriya da sabon zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu zai jagoranta, ana ta hasashen jiga-jigan da za su iya samun damar.

01/05/2023

Shin kun taɓa fuskantar dannau yayin bacci?

Dannau abu ne da mutane da dama ke fuskanta wanda ke danne mutum yayin bacci, kuma ya hana su tashi.

Ana yawan alakanta dannau da aljanu, amma masana sun sanar da cewa wannan ba haka ba ne.

Sun bayyana cewa dalilin da ya sa ake fuskantar dannau shi ne, idan mutum yana mafarki, akwai ɓangaren ƙwaƙwalwarsa da ke farkawa daga bacci amma kuma sauran ɓangarorin ƙwaƙwalwar ba su farka ba.

Hakan ke sa mutum ya ji kamar ya farka amma kuma gangar jikinsa ba ta farka ba.

01/05/2023

Ya Ubangiji ga Malumfashi ka fidda mata wadanda zasu fidda ta kunya.

01/05/2023

YA KAMATA A KALLI WASU AL'AMURRA KAFIN TURA WAƊAN DA ZA'A TURA DON YIN AIKI DA WANNAN SABUWAR GWAMNATIN.

1- ya kasance mazaunan Malumfashi ne, ma'ana cikin gari ko ƙauyukan ta shi da iyalinsa, saboda kada a tura ɗan Malumfashi mazaunin KATSINA ko Kaduna ko wani yanki na wata jaha ko ƙaramar hukuma wadda ba Malumfashi ba, wanda ko pure water MALUMFASHI bai saye, ballantana tattalin arzikin Malumfashi ya bunƙasa ta dalilin sa, don kaucewa masu ci da gumin Malumfashi da jama'arta.

2- wanda bai taba rike wani mukami na siyasa ba, saboda mafi yawan su, sunyi amma iyalan su kawai, s**a wakilta ba Malumfashi da mutanen Malumfashi ba, ko kuma idan za'a bada aba wanda ya taɓa riƙe muƙamin amma ya kamanta adalci lokacin sa.

3- mai kishin al'ummar Malumfashi da kewayen lungu da sakonta, ba wanda zai takaita kaikomon sa gani wasu yankuna ko unguwanni ba, ko wasu mutane ya manta da sauran, misali yafi damuwa da matasa banda dattawa ko akasin haka, ko yan siyasa banda sauran al'umma, a'a wanda zai taimaki Kowa da kowa.

4- mai kula addini kuma wanda ake hidimar addini tareda shi, don kada a tura ɗan boko aqida, saboda mafi yawan cin yan siyasa bakatur su da addini da masu addini sai idan zaɓe bukatar kansu ta taso, a lokacin suke tuna addini, suna manta bukatar addinin a garesu.

5- gogagge a sanin duniyar yau don kawo sababbin tsare-tsare da hanyoyin bunƙasa gari da al'ummar gari. Misali masanin hanyoyin kasuwancin zamani, noman rani ko na damina a zamanance.
Kaima zaka iya kara wasu qualities din.

Elsameen bin Musa.

11/04/2023

Address

Layin Lamarudu
Malumfashi

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00

Telephone

+2348038933311

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malumfashi Social Media Association - MASMA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category


Other Malumfashi media companies

Show All

You may also like