26/10/2023
Aunty Fauziyya D. Sulaiman; Gatar Marasa Gata. Burbushin Matan Sahabbai.
Haqiqa ita gata ce, garkuwa ce, kuma uwa ce ga wadanda s**a rasa gata, mace ce irin wacce tayi fintinkau a cikin tsararrakin ta mata da maza, samun tamkarta sai an tona kwarai, ta sanya walwala a fuskokin mutanen da bata san adadin su ba, tayi sanadiyar canzawar rayuwar mutane marasa adadi, ita abar yarda ce dari bisa dari ga masu buqatar sarrafa dukiyar su ta hanyar taimakawa mabuqata, ina mai basu tabaccin dukiyar su zata kai ga ire-iren mabuqatar da suke cikin yanayi na buqatar taimako kwarai.
Kuyi amfani da dukkan wani nau'in suna na Girmamawa da kuka sani, a yayin da kuka tashi ambatar sunan wannan baiwar Allah, dukkan sunan girmama da kuka ambace ta da shi, ba alfarma kuka yi mata ba, ina yi muku rantsuwa da Allah ta cancanci hakan daga garemu, alkairan ta ba zasu lissafu ba, babu abinda zamu ce da Aunty Fauziyya D. Sulaiman saidai muce Allah ya saka mata da alkhairy, zuciyar (FAUZIYYA) ba bu hassada ko ƙyashi a ciki, bata da ƙyamar mutane, ta na da tsarkin zuciya, kullum hannun ta mai bayarwa ne ga talakawa, ba ta da kwaɗayi, ta na girmama kai, amma sam - sam ba ta da girman kai, ta na da tausayi, mai son karatu da makaranta ce, mai son nishaɗi ce da raha, akwai ta da ƙoƙarin dogaro da kai, ta na son rayuwa ta girmama juna da mutunta juna.
HAJIYA FAUZIYYA D. SULAIMAN YAR ALJANNA CE IN SHA LLAHU DAMU BAKI DAYA.
Gwagwarmaya itace da gewa da jajircewa domin kawowa al'umma mafita a cikin cigaban rayuwarsu ko addininsu, Hajiya Fauziya D sulaiman duniya ta shaida da tarin alkhairin dake yi a cikin gwagwarmayarta, Macece mai fikirar rubutun labari, ko na film ko kuma na littatfi masu ma'ana da suke koyar da darasi ga rayuwar al'umma, kullum cikin fafutuka take da gwagwarmaya domin nemawa al'umma talakawa marasa qarfi taimako, tayi sanadin ceton rayuwar jama'ar annabi marasa adadi wanda s**a kamu da matsanantan rashin lafiya wajen nema musu tallafin kudin magani karkashin qungiyarta mutanen data ciyar bazasu lissafu sannan tayi sanadin da marayu da talakawa da yawa s**a samu matsuguni ko da yaushe dare da rana aikin tallafawa mabuqata shine a gabanta samun mutanen arziki irinsu hajiya fauziyya babbar rahama ce, duniya ta shaida da ayyukan alkhairinta bugu da kari macece mai kare mutuncin addininta a duk inda take bata wasa da addininta da al'adarta.
A shekarun baya lokacin ina yawan karance karance litattafin hausa ina yawan karanta litattafanta. To amma daga baya da na daina karatun litattafai sai na daina jin d'uriyarta. Kwatsam yanzu kuma sai nake yawan cin karo da postings dinta a media duk da dai bata cikin friends nawa.
Fauziyya D. Suleman marubuciya ce. Kuma macece jajirtacciya mai tsayawa akan lamarin talakawa wadanda basu da gata Ta zama tamkar uwa ko uba a garesu.Yawan kai kawo da take yi akan abin da ya shafi tallafi da nemawa bayin Allah taimako har ya mantar da ita aikinta. Kuma da alama Allah ya hadata da miji mai goya mata baya da bata had'in kai kan wannan aikin da ta d'orawa kanta.
Malama Fauziyya ba wai da aljihunta take taimakawa mabuqata ba a'a Tana dai amfani da baiwar da Allah ya bata ne ta rubutu tana taimakawa wajen rubuta halin da wani ko wata ke ciki game da rashin lafiya da kuma yawan kudin da ake buqata a wajen sayen magani Bayan rubutu kuma tana bin mutane masu hali wadanda suke da zuciyar tausayi tana kai musu koken talakawa Cikin ikon Allah sai ka ga duk yawan kudin da ake buqata an dace Babban kuma abin da ke birgeni da tsarin aikinta shine duk wani tallafi da ta samo ko adadin kudin da aka samu tana yin posting tare da sunayen wadanda s**a bayar din dan cire shakka ko zargi A takaice dai komai dai ana yinshi a bisa tsari da kuma dacewa.
Da irin wannan zamu fahimci cewa taimakon mabuqata ba sai mai kudi ba Ni da kai duka zamu iya yinsa ta hanyar yin amfani da irin baiwar da Allah ya bamu Kuma irin wannan aikin shine za kayi ko bayan ranka mutane ba zasu manta da alkhairyn da kayi musu ba Kuma uwa uba ka tarar da tarin ladan ka a cen lahira yana jiranka.
Muna rokon Allah (SWT) ya saka mata da mafificin alkhairinsa ya cigaba da daga kima da mutuncinta, Allah (SWT) ya kara mata Imani, lafiya, arziki da daukaka alfarmar Annabi Muhammad (SAW) Allah (SWT) ya yi mata tsari daga kowane irin sharri na duniya, Allah (SWT) ya yi ma gabanta da bayanta albarka saboda Alfarmar Annabi Muhammad (SAW).
YA ALLAH KA TALLAFAWA DUK MAI TALLAFAWA AL'UMMAH 🙏🙏🙏
Rubutawa ✍️ Abubakar S Malumfashi